KARUWANCI GUBAR KASHE MATA
(Tsakure Daga Littafin ‘YARTSANA)
Nan fa ƙazamin faɗa ya kacame, aka daɗe ba wanda ya raba, domin ba wanda ke son kallon ya ƙare. Matan biyu suka faɗi suka juya, ɗaya ta taushe ɗaya, sannan ɗayar ta juya da ɗayar. Sai dukan juna suke ta yi ba ji ba gani. Da yake Bebi ta fi yarinta, sai ta kama gashin kan Maijigida ta riƙa buga kanta da daɓen simintin da aka yi a tsakar gidan, har Maijigida ta fara gigicewa. A lokacin nan duk zannuwansu sun faɗi, daga su sai siket da kamfai. Maijigida ta samu sa’a ta kama nonon Bebi ɗaya (dama a tsaitsaye suke kamar ƙusa a jikin bango) ta kafa bakinta a bisa kan, ta garza mata cizo iya ƙarfinta. Da zafi ya shigi Bebi, sai ta fasa kururuwa. Nan take sai ga Lado ya shigo. Ya yi wuf ya raba su. Ya shiga tsine masu, yana cewa, “Wane irin rashin albarka ne wannan?” Su kuma suka tsaya suna haki suna zagin juna. A bakin Maijigida ga jini ya cika mata haƙora. Ita kuma Bebi nononta yana zubar da jini. Sauran matan gidan suka zuba ido kawai suna kallon ikon Allah, duk daɗi ya kama su.
(Tsakure Daga Shafi na 58, Sabon Bugu 2016).

✓DARASI:
Duk wani abu na zubar da mutunci yana tare da karuwa!
✓Jinjina ga Malam Ibrahim Sheme












