• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, July 28, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

ADABI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 28, 2026
in Adabi
0
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman, OON da jerin sabbin littattafansa shida

20
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman, OON da jerin sabbin littattafansa shida


__________
Fitaccen marubucin nan da ya shahara wajen wallafa manyan littattafan tatsuniyoyi, al’adu, al’amuran mulki da zamantakewar al’umma, Dokta Bukar Usman, OON, ya wallafa sababbin littatafai har guda shida ringis, a bana.

Related posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026

Marubucin, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Nazari da Kiyaye Al’adu ta Najeriya (Nigerian Folklore Society – NFS), ya fitar da sababbin littattafan nasa guda shida ne a makon farko na watan Afrilu da muke ciki.

Sabbin littattafan sun haɗa da: Looking Back, Looking Forward: 80th Birthday Reflections and Commentaries, wanda yake ɗauke da shafuka 973. Littafin, ya yi tariya ne da nazarin muhimman al’amuran da suka shafi rayuwarsa a shekaru 80 da suka gabata, waɗanda suka haɗa da ayyukansa, rubuce-rubucensa da sauransu, sannan kuma ya hasaso al’amura na gaba. Kamfanin wallafa na Klamidas Communications Ltd. Abuja ne ya yi aikin wallafa dukkan sabbin littattafan shida.

Uku daga cikin sabbin littattafan Bukar Usman

Littafi na biyu mai taken: My Folklore Journey, mai shafuka 402, yana ɗauke da bayanan da suka shafi al’amuran rubuce-rubucen Dokta Usman, waɗanda suka danganci al’adu, tatsuniyoyi da kuma shugabancinsa na Ƙungiyar Nigerian Folklore Society da makamantansu. Littafin ya samu aiki mai inganci tare da kyawawan hotuna.

A jerin sabbin littattafan shida, akwai My Involvement in the World of Folktales, mai shafuka 364. Akwai littafan Peace, Unity and Nation Building in Nigeria and Africa, wanda ke ƙunshe da shafuka 355.

Littafi na biyar shi ne A Review of Philip Chikwuedo Asiodu CFR, CON, HLF: A Legacy of Dedication and Service, mai shafuka 189. Littafin yana ɗauke da bunƙasasshen sharhin littafin tarihin rayuwa da ayyukan tsohon babban ma’aikacin gwamnati, Dattijo Philip Asiodu.

Littafi na shida kuwa, mai taken: Bukar Usman’s Short Stories: A Literary Analysis, Duve Nakolisa ne ya rubuta shi. Ya ƙunshi nazari da sharhi ne dangane da wasu zaɓaɓɓun tatsuniyoyin da Dokta Usman ya wallafa a wasu littattafan nasa.

Wasu uku daga sabbin littattafan Dokta Bukar

Dokta Usman, a Disambar bara ya cika shekaru 83 a duniya, amma har yanzu yana cikin karsashi da ƙwazo wajen aikin da ya sanya gaba, na rubuce-rubuce da wallafa, domin wayar da kan al’umma da adana tarihi.

A lokacin da yake bayanin yadda ya tsunduma cikin ayyukan rubuce-rubuce, Dokta Usman ya ce: “Bayan na yi ritaya a shekarar 1999, na yanke shawarar in ilimantar da jama’a game da wasu daga cikin abubuwan da na koya kuma na fahimta dangane da rayuwar sama da shekaru talatin da na yi ina hidimar gwamnati a muƙamai masu daraja. A yayin yin hakan, sai na karkata zuwa tatsuniyoyi, waɗanda ni da mutane da dama masu daraja muka amfana sosai da su, tun muna yara har zuwa girma. Wannan ne ya sa na gudanar da bincike kuma na kalato tare da tattara tatsuniyoyi masu yawa daga al’ummomi da ƙabilu daban-daban na sassa daban-daban na faɗin Najeriya.

“Yayin da nake raba ayyukana na littattafai da rubuce-rubuce da suka shafi nazari da bincike a fannonin da na mayar da hankali a kai ga al’umma; sakamakon da nake samu daga masu karatu, tare da kafofin yaɗa labarai a matsayin masu ƙarfafa mini gwiwa, da kuma karramawa iri-iri da na samu daga cikin gida da waje, sun sa na ji cewa ana daraja abin da nake yi kuma hakan yana ƙara ƙarfafa mini gwiwa,” in ji shi.

Kodayake ba a san shi sosai a matsayin marubuci ba lokacin da yake aikin gwamnati, Dokta Usman ya ce, “Sai dai hakan ba yana nufin ban taɓa rubuce-rubuce ba a cikin aikina na hukuma. Na yi amma a mataki kaɗan.”

Ya ci gaba da cewa, “ritayata ce kawai ta ba ni ƙarin lokaci na sadaukarwa ga rubuce-rubuce. Kuma na yi amfani da wannan damar sosai da taimakon Allah, wanda ya albarkace ni da lafiya da kuma ikon yin hakan. Kamar yadda na taɓa bayyanawa a can baya, na yi imanin cewa kowanne ɗan Adam yana da baiwar rubutu a jikinsa. Sai dai yana buƙatar ɗan turzawa kaɗan, domin ya bunƙasa. Kuma goyon bayan jama’a da na samu ya taka rawar gani wajen hakan,” in ji shi.

A shekaru 83, marubucin ya bayyana cewa har yanzu yana cikin ayyukan rubuce-rubuce da kiyaye adabi. Ya ce yana aiki ne tare da wasu ma’aikata kaɗan, galibi a lokutan yamma na ranakun aiki, yayin da yake ware ƙarshen mako da ranakun hutun gwamnati domin “karatu da yin tunani domin ƙara cika aikin da nake yi ni kaɗai, a sauran lokuta.”
__________

Previous Post

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Next Post

Farewell Ashaka

Related Posts

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
Adabi

Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa

July 18, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna (2)
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa
Adabi

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026
Next Post
Farewell Ashaka

Farewell Ashaka

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (2)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (2)

May 7, 2025
Hajia Amina Donates Mosque Building to Muslim Community

Hajia Amina Donates Mosque Building to Muslim Community

March 11, 2024
Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (2)

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 22, 2023
Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

November 16, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja
  • A Voice for Eternity
  • A New Dawn for NIgerian Defence: The Strategic Expansion of the Nigerian Army to 12 Divisions

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

Yan Bindiga Sun Halaka Babban Jami’in Soja A Abuja

July 28, 2026
A Voice for Eternity

A Voice for Eternity

July 28, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.