• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, July 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

ZINATU MATAR GWAMNA (2)

ƘIRƘIRARREN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 20, 2024
in Adabi
0
ZINATU MATAR GWAMNA (2)

Zinatu Matar Gwamna

176
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ZINATU
MATAR GWAMNA
(2)

~~~~~~~
A makon jiya mun tsaya inda aka ce:
“Ƙawarta ce Balaraba ta ƙara tabbatar mata da cewa, lallai ita da samun sauƙin irin waɗannan tsegunguma sai ta yi aure ko kuma wani sanadi ya zo, yadda za ta rabu da iyayenta.”
Ga ci gaba:
~~~~~~~

Related posts

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026

“Ina son ki gane yanayin al’adunmu da na addininmu,” in ji Balaraba. “A ƙasar Hausa, saboda tasirin addini, yarinya da ta fara girma, ta zama abin tashin hankali ke nan ga iyayenta. Ba za su sake samun kwanciyar hankali ba sai sun ga ta yi aure. Idan ba haka ba kuwa, to, ba za su guje wa maganganu da tsegunguman maƙwabta ba. Idan an yi rashin sa’a kuma sai ki ji ana yi mata yarfe da cewa, ta yi kwantai.”

“To, amma ai ya kamata mu gane cewa duniya ta canza; da da yanzu ba ɗaya ba ne. A zamanin da, kamar yadda muka karanta a tarihi, babu yawan al’umma kamar yanzu, babu talauci da kwaɗayin neman duniya kamar yanzu. Haka kuma, babu ilimin zamani, inda mata da maza za su samu wayewa. To, tun da yanzu duk waɗannan al’amura sun samu canji, me zai hana mu canza mu ma?”

Zinatu na ƙarin bayani ga ƙawarta. Suna tafiya ne bisa titi da maraice. Ga alama, sun dawo daga kasuwar ’Yar Kutungu ne; suna dawowa zuwa gida. Balaraba ta tauna cingam da ƙarfi, ta hura shi bisa leɓɓanta, ta yi balo da shi, sannan ta maida shi cikin baki.

“Kash! Zinatu, kin mance da wani abu ɗaya. Da kike cewa duniya ta canza, wane ne ya canza? Ina son ki gane cewa, mu matasa da ƙananan yara, ’yan zamani; mu ne muka canza, amma su baba da inna da kakanninmu fa, sun canja ne? Don haka, dole ne za mu ci gaba da tafiya haka, suna tafiya, ana canjawa a hankali; har nan gaba yanayinmu da al’adunmu sai su canja.”

“Na yarda da wannan bayanin naki, amma me iyayenmu ke gudu, da suke matsa mana haka game da aure?”

Zinatu ta ci gaba da magana, amma ba ta jira amsar ƙawarta ba, sai ta ci gaba da bayaninta.

“Ina ganin namiji ne ya kamata ya nemi yarinya da aure ko? To, idan bai nema ba fa? Ya kamata yarinya ta je wajen saurayi ne tana roƙon sa, cewa ya zo ya aure ta? Ai wannan zubar da mutunci ne kuma ya saɓa wa al’adar Malam Bahaushe. Ni kam gani nake kamar gajiya aka yi da ni a gidanmu, shi ya sa ake tsangwama ta, wai in yi aure. Duka yaushe na gama wannan makarantar? Ki tuna fa ko jarabawarmu ma ba ta ida fitowa ba.”

Balaraba ta tuntsure da dariya, har tana tuntuɓe. Takalminta ne ya ci karo da wani bulo da ke gefen hanya. Ta yi tangal-tangal haka, kamar za ta faɗi.

“Shegiya! Wallahi kin sanya ni dariya a kan titi haka, kamar zautatta. Wai an gaji da ke, babu wanda ya gaji da ke. Su a ganin su, abin kunya ne ɗiyarsu ta kai kamar ki ba ta samu miji ba. Kuma suna tsoron abin kunya, musamman kada wani shege ya ɗirka maki ciki, ki haifar masu ɗan rariya.”

“Haba, haba, don Allah ki bar wannan maganar. Ai ni ban ga ɗa namijin da ya isa ya yi mani wannan sakarcin ba. Ki tuna fa ina da ilimi hagu da dama. Kin san dai na sauke Alƙur’ani bara, ga shi ma har na fara hadda. Arba’una Hadis kuwa tuni na sauke shi, har ma na fara shiga manyan littattafan Fiƙihu. Ta ɓangaren karatun zamani kuwa, ba sai na gaya maki ba, tun da aji ɗaya muke; kwalin difiloma kawai muke jira. Don haka, duk illar zinace-zinace ba wacce ba mu sani ba. To, yaushe zan zubar da mutuncina har in yarda da wani mayaudari ya yaudare ni?”

Zinatu na gama wannan batu sai Balaraba ta amshe, ta ce: “Ni dai ina ganin mu bi a hankali da iyayenmu, mu lallaɓa da su, mu rabu lafiya. Tun da dai mun yi karatun nan na zamani, sai mu ƙoƙarta mu yi ta roƙon Allah Ya koro mana da mazajen aure. Mu yi aurenmu mu huta, alabashi idan muna ɗakunan mazajenmu sai mu san hikimar da za mu shawo kansu, su bar mu mu ci gaba da neman ilimi ko kuma ma mu yi aiki ko sana’ar neman kuɗi, don rufin asirin kanmu.”

Da wannan zancen ne suka kawo inda za su rabu, kowace ta kama hanyar gidansu.
***

~~~~~~~
Za mu ci gaba a ranar Lahadi in sha Allahu. Ku ci gaba da bibiyar mu.
~~~~~~~

Previous Post

KARUWANCI GUBAR KASHE MATA

Next Post

Lt. Col. Danjuma’s Book: Captivating Insight Into Civil-Military Relations In Nigeria

Related Posts

Maryam ‘Yar Aljanna (2)
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa
Adabi

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

June 21, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna

June 20, 2026
Next Post
Lt. Col. Danjuma’s Book: Captivating Insight Into Civil-Military Relations In Nigeria

Lt. Col. Danjuma's Book: Captivating Insight Into Civil-Military Relations In Nigeria

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

An Kafa Gidauniyar Danbarno

An Kafa Gidauniyar Danbarno

June 30, 2023
Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

July 17, 2023
ZUMUNCI: Ƙungiyar Ɗalibai Ta Karrama ACC Tasi’u Saulawa

ZUMUNCI: Ƙungiyar Ɗalibai Ta Karrama ACC Tasi’u Saulawa

January 5, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana
  • Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage
  • Zaɓen 2027: Akwai Yiwuwar Farfesa Pantami Ya Yi Nasara – Farfesa Lawanti

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

July 10, 2026
Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

Book Launch Seeks to Rewrite Lassa’s Story, Preserve Cultural Heritage

July 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.