Jaafar Jaafar Ya Buɗe Idanun ‘Yan Kwankwasiyya
__________
Fitaccen ɗan jarida kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian (online), Jaafar Jaafar, ya gabatar da wani tsokaci mai ban mamaki, a shafinsa na Facebook, dangane da matakin da Jam’iyyar NDC a Jihar Kano ta ɗauka; inda ta ayyana Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin wanda zai zama Mataimaki ga ɗan takarar Gwamna a Jihar ta Kano.
Tun da farko, Malam Jaafar ya buɗe bayanin nasa da kaushin harshe, inda ya ce: “Ɗaukar Mustapha Kwankwaso a “Deputy Governor” ba daidai ba ne. Haƙƙi ne a gare mu, mu faɗi gaskiya duk inda muka gan ta. Kujerar “Deputy Governor” ba abar wasa ba ce.
“Yau in Allah ya ɗauki ran Gwamna, Deputy za a rantsar ya maye gurbinsa. Kujera ce wacce gogaggun mutane irin su B.B. Faruk, Audu Dawakintofa, Wada Abubakar, Professor Hafiz Abubakar da sauransu suka riƙe.

Ɗan jaridar, wanda ya yi fice wajen bankaɗo bahallatsar ‘yan siyasa, ya ci gaba da cewa: “Amma a haƙiƙanın gaskıya ɗaukar Mustapha a matsayin “Deputy Governor” ya saɓa da duk shika-shikan Ɗarikar Kwankwasiyya. Ni a karan kaina, Mustapha yana mutunta ni kuma ko a yanzun nan da nake wannan rubutu, na ga ya kira ni a waya. Idan maslahata zan duba, ba ni da matsala da shi. Amma a kan abin da ya shafi al’umma, ina da matsala da shi.”
Da yake magana game da halayen Mustapha Kwankwaso, Jaafar ya bayyana cewa: “Ba wai ina so na aibata Mustapha ba ne amma duk wanda ya san Mustapha ya san bai cancanci wannan kujera mai girma ba. Walau a fannin Boko ko Muhammadiyya ko mu’amula, babu inda za a ce Mustapha ya kere duk zaƙakuran mutanen da suka yi shekara da shekaru suna hidimta wa tafiyar Kwankwasiyya.”
Ya ci gaba da cewa: “Ko shi kansa Oga, a duk harkokin da yake yi na sana’a, ban ga ɗaya da Mustapha ne ke kula da ita ba. Ko manajan gona bai ba shi ba amma kuma yau a ɗora shi a gwadaben da zai yi “managing” dukiya da rayukan miliyoyin al’umma?”
Daga ƙarshe dai, babban ɗan jarida Jaafar ya ƙarƙare bayaninsa da gargaɗi da kuma neman Jam’iyyar NDC da shugabanninta da su gyara lamarin, inda ya ce: “A gyara lamarin nan, kada garin neman gira a rasa ido.”
Abin tambaya a nan shi ne, ko iyayen Jam’iyyar NDC a Jihar Kano za su ɗauki shawarar Jaafar da sauran ‘yan Kwankwasiyya da suke ganin ba a yi masu daidai ba? Lokaci ne kawai zai nuna haka.
Jama’a masu karatu, shin yaya kuke ganin wannan lamari, mene ne ra’ayinku? Ku bayyana a Comment Section.
__________












