• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 28, 2025
in Babban Labari
0
BINCIKE:  Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

Gidan Rediyon BBC

788
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BINCIKE:

Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
Gidan Rediyon BBC

 

                      ••••••••••

A ‘yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta sun ɗauki ɗumi dangane da shahararriyar kafar watsa labarai ta duniya, Sashen Hausa na BBC. Wannan ya biyo bayan wata tattaunawa da gidan talabijin na Arewa24 ya yi da ɗaya daga cikin tsofaffin ma’aikatan tashar, Hajiya Halima Umar Saleh.

A tattaunawar ce aka jiyo ‘yar jaridar tana bayanin yadda rayuwar aikinta ya kasance a BBC Hausa. A cewarta, ba za ta taɓa mance zaman ƙunci da ta yi a gidan rediyon ba. Ta ce akwai wani shugaba da ya uzura mata, ya ɗora mata karan tsana, ya riƙa kyara da cin zarafinta, wanda haka ya sanya “na shiga addu’a da neman tsari daga gare shi,” in ji ta.

Hajiya Halima Umar Saleh, tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa

Halima ta ce Allah ya ji roƙonta, inda tana zaune aka neme ta da tayin aiki a Gidan Rediyon Turkiya. “Amma a rayuwata, ba zan taɓa mance wannan ƙunci da na shiga ba,” a cewar Halima a yayin tattaunawarta da Arewa24.

Jin kaɗan da fitar wannan tattaunawa sai kafafen sada zumunta suka kaure da maganganu da tsegunguma, tare da hasashe daban-daban. Duk da cewa Halima ba ta kama sunan “ogan” da ta yi zargin ya uzura mata ba amma an samu wasu da suka yi ta kwarmata batun, inda har wasu suka riƙa ambata sunan Shugaban Sashen Hausa na BBC na yanzu, Malam Aliyu Abdullahi Tanko, tare da jefa igiyar zargi a kansa.

Malam Aliyu Abdullahi Tanko, Shugaban Sashen Hausa na BBC

A binciken da Mujallar Taskar Gizago ta gudanar, wakilinmu ya gano sahihin abin da yake faruwa a babbar kafar sadarwa ta BBC Hausa. Wakilin namu ya tattauna da wani fitaccen ɗan jarida kuma jigo a fagen aikin a Arewa da ƙasa baki ɗaya. A bayaninsa, babban ɗan jaridar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi wa wakilinmu ƙarin haske dangane da al’amarin.

“Babu ƙanshin gaskiya ko kaɗan dangane da cewa akwai matsala ko akwai cin zarafin ma’aikata a BBC Hausa, domin kuwa kafar watsa labarai ce ta duniya, wacce ke da ingantaccen tsari na musamman, wanda ya sha bamban da ƙananan gidajen jaridu irin namu na gida;” a cewar babban ɗan jaridar.

Ya ce akwai tsari da ƙa’idojin aiki masu fa’ida waɗanda ke tabbatar da ɗa’a da kyakkyawan yanayin aiki tsakanin manya da ƙananan ma’aikata, inda babu wata ƙofa da wani babba zai ci zarafin ƙarami haka siddan.

Ya ce, “kuma kar ka manta, BBC Hausa ba su amincewa da ma’aikata masu kasala da ragonci. Duk ma’aikacin da ya ce zai riƙa makara ko aikata wani abu da ya saɓa ƙa’idar aiki, to ba zai samu amincewa ko ya ji daɗin aiki ba. Haka ma ma’aikacin da ya saba da gulmace-gulmace ko halaye marasa kyau irin haka, to ba zai ji daɗin aiki a nan ba. Irinsu ne za su ga kamar ana takura masu ko su ce ana uzura masu. Idan ba haka ba, muddin kana yin aikinka daidai, babu wani babba da ya isa ya uzura maka.”

Game da masu zargin cewa wai ma’aikata suna barin BBC Hausa saboda wannan batu na Halima, Taskar Gizago ta gano cewa ba haka al’amarin yake ba. A binciken da wakilinmu ya gudanar, ya gano cewa babu wani ma’aikaci da aka ce ya bar aiki saboda uzurawa.

Taskar Gizago ta ji daga bakin ɗan jarida kuma mawallafin Jaridar Alheri, Malam Mu’azu Harɗawa kan lamarin. Ya shaida wa wakilinmu cewa babu wani ma’aikacin BBC Hausa da ya bar aiki a ‘yan kwanakin nan. “Kawai dai abin da na sani shi ne, kimanin shekaru biyu da suka gabata, wasu ma’aikatan sun koma Gidan Rediyon Turkiya, amma ba don uzurawa ba. Kuma wannan ba laifi ba ne, domin ‘yan jarida na canja wurin aiki idan sun buƙaci haka,” inji Malam Harɗawa.

Malam Mu’azu Harɗawa, ɗan jarida kuma mawallafin Jaridar Alheri

Wakilinmu ya tuntuɓi Shugaban Sashen Hausa na BBC, Malam Aliyu Abdullahi Tanko ta wayar tarho dangane da wannan al’amari.

“Ni babu wani abu da zan iya cewa kan wannan al’amari. Duk wanda yake son ɓata mani suna ko yake nema na da sharri, na bar shi da Allah.” Inji Abdullahi Tanko, inda ya ƙara da cewa suna zaune lafiya da ma’aikata a BBC Hausa, babu wata hatsaniya ko raini tsakanin manya da ƙanana.

Previous Post

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (2)

Next Post

CREATION OF NEW STATES IN NIGERIA: Between Political Deception and National Development

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
CREATION OF NEW STATES IN NIGERIA: Between Political Deception and National Development

CREATION OF NEW STATES IN NIGERIA: Between Political Deception and National Development

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]

Lost Heritage Series #1 – Mazari [Spindle]

September 19, 2023
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
TY BURATAI LITERARY INITIATIVE: Unveiling the Young Literary Giants

TY BURATAI LITERARY INITIATIVE: Unveiling the Young Literary Giants

November 4, 2024
Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Tumbu-Madalla

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Tumbu-Madalla

July 21, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.