Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
Daga Bukar Usman

__________
Sunan Littafi: Being True to Myself
Marubuci: Sule Lamido
Shekarar Wallafa: 2025
Yawan Shafuka: 487
Mai Sharhi: Bukar Usman
__________
Littafin tarihin rayuwar Sule Lamido mai suna Being True to Myself babban saƙo ne na musamman mai zaman kansa. Taken yana magana ne kan muhimmancin mutum ya kasance a zahirinsa na gaskiya kuma mai gaskiya a kansa. Kasancewar mutum mai gaskiya da yarda da kansa yana nufin bayyana kansa daidai da halayensa, darajojinsa da muradunsa na asali. Ana cewa mutum yana gaskata kansa ne, idan jin daɗinsa da walwalarsa sun samo asali daga cikakkiyar fahimta da manufa ta rayuwa. Wannan yana faruwa ne idan mutum ya saba gina rayuwarsa da girmama kansa, wanda hakan kan sanya shi ya yi aiki bisa abin da ya yi imani da shi; ba wai don kwaikwayo ko nuna isa kawai ba.
Kasancewar mutum mai gaskata kansa, ba yana nufin mutum mai bin Yarima domin ya sha kiɗa ba ne, ba tare da tantancewa ko tunani ba. Sai dai hakan yana nufin mutum mai bin abin da zuciyarsa ta gaskata masa. Haka kuma yana nufin mutum mai gano abin kirki, mai amfani da zai gamsar da shi a cikin rayuwar al’umma. Yana nufin sadaukar da kai ga abin da mutum ya tabbatar a ransa, cewa an kira shi ya yi domin kyautata rayuwar al’ummarsa. Wannan ne ya sa masanin falsafa, Aristotle ya ce, rayuwa mai ma’ana ita ce rayuwa ta gaskiya. Rayuwa ta gaskiya ita ce wadda ƙa’idojin ɗabi’a masu ƙima, kamar tausayi, karamci, riƙon amana, haƙuri da adalci suke jagorantar halayen mutum na yau da kullum.
Wannan ita ce fahimtata gaba ɗaya, game da furucin “being true to myself” wanda Sule Lamido, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma tsohon Ministan Harkokin Ƙasashen Waje na Najeriya, ya zaɓa a matsayin sunan littafin tarihin rayuwarsa. Duk da cewa ƙungiyar editoci guda biyar ƙarƙashin jagorancin marigayi Farfesa Haruna Wakili ce ta yi gyaran littafin mai shafuka 487 cikin ƙwarewa, ƙungiyar ta bayyana a sarari cewa dukkanin ra’ayoyi da bayanan da ke cikin littafin, na marubucin ne shi kaɗai.
Lamido ya bayyana cewa duk da an haife shi cikin wadata, ya taso da “tausayi da jin ƙai ga marasa galihu.” Yana mai cewa duk da ƙauyensu Bamaina ƙarami ne, “bambance-bambancen rayuwa da zamantakewa da tattalin arziki sun kasance a bayyane.” Haƙiƙa, ya tuna cewa tun yana yaro tausayin nasa har ya shafi dabbobi, ta yadda ba ya iya jure ganin ɗan akuya yana kuka; shi ma sai ya fara kuka (shafi na 14).
Wataƙila wannan tausayi da damuwa ga talakawa ne suka sanya ya zama “mutum mai yin suka mai ma’ana” a tsawon rayuwarsa, wanda ba wai kawai yana nuna kurakuran yadda ake tafiyar da mulkin Najeriya ba ne, har ma yana bayar da shawarwarin hanyoyin da za a gyara matsalolin da aka gano (shafi na 379).
Rahotannin yadda Lamido ya yi hulɗa da mutane daban-daban a ciki da wajen Nijeriya, ciki har da masu mulki da waɗanda ba sa cikin gwamnati a matakai daban-daban, sun bayyana a littafin sosai, tamkar Lamido yana yawo da na’urar naɗar murya ko kuma ya kasance ɗan jaridar da ke bayar da rohoto kai tsaye.
Wannan ya wadatar ya zama taƙaitacciyar gabatarwa game da halayen Lamido. Za a iya ƙara bayyana hakan, ta hanyar zaɓinsa na alaƙar siyasa da ayyukan siyasa.
Littafin mai shafuka 487, an kasa shi zuwa gida takwas kuma yana ƙunshe da babi 16. Kamar yadda aka yi tsammani, littafin ya bayar da labarin rayuwar Lamido da zamaninsa. Domin nazari, za a iya karkasa ƙunshiyar littafin zuwa manyan sassa uku kamar haka:
A-Haihuwa da Rayuwa Kafin Shiga Siyasa
B-Shiga Siyasa da Harkokin Jam’iyya
C-Kammalawa
A-Haihuwa da Rayuwa Kafin Shiga Siyasa:
An bayar da bayanan da suka shafi batun haihuwar Lamido daga shafi na 1 zuwa na 47. Shi Bafullatani ne kamar yadda hotonsa da ke jikin littafin ya nuna, inda yake sanye da malafa (wacce aka sani da al’adar Fulani), wadda aka tufƙa da kaba kuma aka yi mata ado. Yana jin Fulfulde amma dai harshen Hausa ne yaren sadarwa a tsakanin iyalansa.
An haifi Lamido a ranar 30 ga Agusta, 1948 a Bamaina; wani matsugunin Fulani da kakanninsa suka kafa a kusan shekarar 1904, wato shekaru goma kafin Turawan Mulkin Mallaka su haɗa Arewa da Kudu, su kafa Najeriya. Garin Bamaina yana kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, (Route A237). A da yana cikin Jihar Kano amma yanzu yana cikin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Garin ya bunƙasa ya zama gunduma kuma iyayensa ne suka riƙa mulki tun farkon kafuwar garin daga tushe. Duk da cewa Lamido ɗan sarki ne amma a rayuwarsa, bai ɗauki matakan zama Hakimi ba saboda yadda ya tsunduma cikin harkokin siyasa. Ma’ana, ya zama cikakken ɗan siyasa. A yanzu, ɗaya daga cikin ’ya’yansa ne Hakimin Gundumar. A taƙaice dai garin Bamaina shi ne mahaifar Lamido.
Kodayake Lamido ya fara karatu a makarantar allo tun yana yaro, karatun boko ya kai shi zuwa wasu wuraren. Misali, daga makarantar firamare a Birnin Kudu ya tafi Kwalejin Gwamnati ta Zaria, wadda yanzu ake kira da Kwalejin Barewa. An ba shi gurbin shiga kwalejin a shekarar 1961 saboda ƙwazonsa kawai. Ya kasance fitacce kuma mai hazaƙa a makarantar.
Bayan kammala karatu a Kwalejin Barewa, Lamido ya fara samun aiki a Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya a matsayin mai koyon aiki a fannin Gine-Gine a shekarar 1967. Daga bisani ya ji ba ya sha’awar aikin, sai ya samu wani aiki a Kamfanin Taba Sigari na Najeriya (NTC), a matsayin Jami’i Mai Duba Inganci. An tura shi Gusau sannan daga baya Maiduguri. Aikinsa na uku kuwa shi ne Manajan Tallace-tallace a Kamfanin AC Christilieb. Yayin da yake wannan aiki ne aka mayar da shi Legas a shekarar 1974.
Zaman Lamido a Kwalejin Barewa, wadda falsafarta ta rashin nuna wariyar addini, ƙabila ko yankin da mutum ya fito, tare da tafiye-tafiyensa zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan a matsayin Jami’in Kasuwanci na kamfanoni masu zaman kansu, sun faɗaɗa tunaninsa game da bambance-bambancen Najeriya; tare da sanya shi ya zama mai hangen nesa kuma mai kishin ƙasa baki ɗaya.
B-Shiga Siyasa da Harkokin Jam’iyya
An tattauna wannan ɓangare na rayuwar Lamido sosai a mafi yawan littafin, daga shafi na 50 zuwa na 406. Bayanan sun haɗa da abokan hulɗarsa a Legas, lokacin da yake aiki a kamfani mai zaman kansa. Ta hanyar tattaunawa da waɗannan abokai, musamman a gidansa, ya samu fahimta game da falsafar Jam’iyyar Northern Elements Progressives Union (NEPU), wadda daga baya ta rikiɗe zuwa People’s Redemption Party (PRP), sannan ta zama wani ɓangare na tubalin da daga baya ya gina Jam’iyyar Nigeria People’s Party (NPP) da kuma People’s Democratic Party (PDP).
Lamido ya shiga siyasar jam’iyya ne ta hanyar PRP a shekarar 1979. Aƙidar NEPU, tare da ƙima da manufofinta na kula da mutunci da jin daɗin ɗan Adam, waɗanda suka dace da irin imaninsa, su ne suka kasance ginshiƙin shigarsa al’amuran siyasa da mulki (shafi na 409). Ya ce duk da cewa dandamalin siyasa na iya sauyawa, shi yana nan daram a kan aƙidar NEPU, wadda yake da cikakken imani da ita kuma yake aiwatarwa har zuwa yau.
√ Ɗan Majalisa:
An zaɓi Lamido a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar PRP zuwa Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya, inda ya wakilci Birnin Kudu, wadda a lokacin tana cikin Jihar Kano, daga 1979 zuwa 1983. A matsayinsa na ɗan majalisa, Lamido ya kasance memba a Ƙungiyar Neman Ƙirƙiro Jihar Jigawa. Daga baya an cin ma wannan buri, sannan aka zaɓe shi a matsayin Gwamnan jihar.
√ Jami’in Jam’iyya:
Siyasa ta ba Lamido dama ta samun muƙamai daban-daban. A Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), ya riƙe muƙamin Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kano. Daga baya kuma ya zama Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa. Kafin da bayan zaɓensa a matsayin Shugaban Jam’iyya, ya fuskanci rikice-rikicen cikin gida da saɓanin ɓangarori. Haka ma a muƙamin Sakataren Ƙasa bai rasa irin waɗannan ƙalubale ba.
Lamido ba ya goyon bayan tsarin zaɓen fidda gwani wajen zaɓar ’yan takarar muƙaman siyasa. Ya ce hakan ya samo asali ne daga yadda ake amfani da kuɗi wajen rinjayar zaɓe, sakamakon yunwa da talauci da kuma ƙarancin wayar da kai a tsakanin wakilan zaɓe. Ya bayyana cewa duk da cewa zaɓen fidda gwani yana kan dimokuraɗiyya wajen zaɓen ’yan takara, sakamakonsa yana lalata manufofi da ainihin dalilin tsarin. Lamido ya fi son tsohon tsarin da shugabannin jam’iyya ke da ikon tsayar da ’yan takara.
Lamido ya bayyana irin wahalhalun da shi da iyalinsa suka fuskanta, musamman saboda matsayinsa kan wasu batutuwa da kuma yunƙurinsa na neman shugabancin ƙasa. An ɗaure shi sau biyu kuma an tsare shi har sau takwas saboda dalilan tsaro a rayuwarsa ta siyasa. Daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta a matsayin jami’in jam’iyya, akwai rikicin soke Zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993, inda duk da tsananin adawa ya tsaya tsayin daka wajen ɗaukar matakan da suka tabbatar da haɗin kan ƙasa, zaman lafiya da kwanciyar hankali sama da komai.
√ Shugaban Hukuma:
An naɗa Lamido a matsayin Shugaban Bankin Noma da Haɗin Gwiwa na Nijeriya (NACB) a ƙarƙashin Gwamnatin Abacha. Bankin yana ƙarƙashin Ma’aikatar Noma ta Tarayya. Ya riƙe muƙamin na tsawon watanni uku kacal kafin ya tafi a matsayin wakili zuwa Babban Taron Tsarin Mulki na Ƙasa. Ya ce shugabancin bankin shi ne muƙamin farko da ya taɓa riƙewa a gwamnati kuma hakan ya ba shi damar fahimtar yadda gwamnati take aiki a ciki.
Yayin da yake ba da labarin abin da ya fuskanta a can da kuma daga baya a Ma’aikatar Harkokin Waje, inda aka naɗa shi Ministan Harkokin Waje a Gwamnatin Obasanjo, ya ce ya yi ƙoƙarin nisantar rashawa da “jarabar tara abin duniya” domin kada ya tauye mutuncinsa da ikon ɗabi’arsa a kan waɗanda yake jagoranta. Saboda wannan dalili ne ma lokacin da yake Ma’aikatar Harkokin Waje, duk zarar kuɗin alawus ɗin tafiya aiki zuwa ƙasashen waje da bai kashe ba, yana mayar da su ga gwamnati (shafuka 160-166).
√ Wakilin A Taron Tsarin Mulki:
Lamido ya kasance wakili a Babban Taron Tsarin Mulki na Ƙasa na shekarun 1994/1995. Ya lura cewa tattaunawar farko a taron ta cika da zazzafar muhawara mai sosa rai, tsakanin ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki daban-daban. Bayan hankula sun kwanta ne aka gabatar da shawarwari. Ya kuma ga taron a matsayin wata hanya ta ƙulla alaƙar siyasa da haɗin gwiwa.
√ Muƙamin Minista:
An naɗa Lamido Ministan Harkokin Ƙasashen Waje na Najeriya daga 1999 zuwa 2003. Ya ƙi sanya hannu kan takardar cewa ya yi murabus. Takardar, wacce ba ta ɗauke da kwanan wata, Fadar Shugaban Ƙasa ce ta bai wa kowane minista a waccan gwamnati.
Lamido ya fahimci cewa babban aikin ma’aikatarsa shi ne bayyana ayyuka da abubuwan da suka shafi Najeriya ga duniya. Saboda haka, bayan ya kama aiki ya bayyana wa ma’aikatan da ke ƙarƙashinsa cewa kada su yi riya, yana mai ƙarfafa su da cewa su nuna Nijeriya yadda take, ba yadda wasu ƙasashen waje suke son ta kasance ba.
Daga cikin abubuwan da ya ba fifiko, akwai inganta yanayin aiki da ɗaukaka martabar ma’aikatar. Ya ƙuduri aniyar kammala ginin hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja, wanda aka bari ba a kammala shi ba kusan shekara goma. Cikin sa’a, tare da goyon bayan Fadar Shugaban Ƙasa, ya yi nasarar kammala aikin, duk da ƙoƙarin da aka yi na ƙalubalantar ƙima da sahihancinsa. Ginin wanda yake kusa da Eagle Square, bayan an kammala shi an sanya masa sunan Firaministan Najeriya na farko kuma guda ɗaya tilo da aka taɓa samu, Sir Abubakar Tafawa Balewa.
Yayin da Lamido yake aikin hulɗar jakadanci da ƙasashen waje, kamar kuma yadda halartar tarukan ƙasa da ƙasa, ya tsaya tsayin daka wajen kare muradun Najeriya daga wasu manufofin munafunci da wasu ƙasashe ke ƙoƙarin ɗora wa ƙasarsa. Daga ciki akwai ƙin amincewa da wasu ƙudurori da ke la’antar shugabannin wasu ƙasashe da aka ƙaƙaba wa takunkumi, duk da irin mummunar illar da takunkumin ke yi ga talakawa. Haka kuma ya yi magana ƙwarai kan yadda manyan ƙasashe masu ci gaban tattalin arziki suka kasa cika alƙawuran kuɗaɗen tallafi ga ƙasashe masu tasowa, kamar alƙawuran da aka yi a shahararren taron Lome Convention.
Dangane da talauci da yunwa, ya fi son ya gayyaci masu ruwa da tsaki su zo Najeriya su gani da idanunsu, irin mawuyacin halin da ƙasar ke ciki maimakon tattaunawa marar amfani a ƙasashen waje. Haka kuma ya kasance babban mai rajin neman a yafe wa Najeriya bashin ƙasashen waje da kuma dawo da kuɗaɗen da aka wawure.
Najeriya ta amfana daga batun sake tattauna bashin ƙetare saboda waɗannan ƙoƙari na Lamido. A ƙarƙashin jagorancinsa, ma’aikatar ba ta amince da salon munafunci na wasu ƙasashe da suke sukar aiwatar da Shari’a a wasu ƙasashe amma suna yin shiru idan ana aiwatar da ita a wasu wurare ba.
√ Muƙamin Gwamna:
Lamido ya yi nasarar zama Gwamnan Jihar Jigawa karo biyu a jere daga 29 ga Mayu, 2007 zuwa Mayu, 2015. Haka kuma, ya taɓa yunƙurin neman zama Gwamnan Jihar Kano kafin a ƙirƙiro Jihar Jigawa amma bai samu nasara ba. Zaɓensa a matsayin Gwamnan Jihar Jigawa ma ya zo ne bayan an daƙile wasu yunƙure-yunƙure da dama a baya.
A lokacin, yana kama aiki a matsayin gwamna, ya fara ƙoƙarin inganta gine-ginen gwamnati da kuma bunƙasa rayuwar al’umma a jihar. A yayin haka, ya mayar da ma’aikatun gwamnati gaba ɗaya zuwa Dutse, babban birnin jihar, domin a baya suna warwatse a yankunan masarautu daban-daban. Haka kuma ya dawo da Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jiha.
Domin shimfiɗa tubalin zaman lafiya a matsayin ginshiƙin ci gaba da sauƙaƙa cin ma manufofinsa, Lamido ya nemi goyon bayan ’yan majalisar jihar da manyan masu ruwa da tsaki. Haka kuma ya fara shirye-shiryen wayar da kan jama’a, domin rage matsalolin da ke haddasa rashin fahimta da tashin hankali tsakanin al’umma. Duk da ƙarancin kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR), Lamido ya samu goyon bayan hukumomin bayar da tallafi na ƙasa da ƙasa wajen aiwatar da ayyukansa na jin ƙai, wanda ya ƙara wa kuɗaɗen da jihar ke samu daga asusun tarayya ƙarfi.
Lamido ya tarar da harkar ilimi a jihar cikin wani mummunan hali. Ya ce tsawon shekara uku, babu wani ɗalibi daga Jigawa da ya samu gurbin shiga manyan makarantu saboda gwamnatin da ta gabata ta kasa biyan kuɗin jarabawar NECO na Naira miliyan 10. Amma zuwa shekararsa ta biyar a mulki, kuɗaɗen da jihar ke ware wa ilimi sun zarce ƙa’idar mafi ƙarancin kaso 25% da Hukumar UNESCO ta tanada daga kasafin kuɗin jiha. Jihar ta ware kusan kaso 30% domin gyara halin da ake ciki ta ɓangaren ilimi (shafuka 310 da 316).
A ƙarshe, Lamido ya yi nasarar aiwatar da manyan ayyuka masu ɗorewa a fannoni kamar ilimi, lafiya da sauran muhimman sassa. Littafin ya ƙunshi hotuna masu ƙayatarwa na wasu daga cikin ayyukan da ya bari. Daga ciki akwai Jami’ar Jihar Jigawa wadda aka sake mata suna zuwa Sule Lamido University; Makarantar Jinya da Unguwarzoma; Cibiyar Koyon Sana’o’i; ofisoshin gwamnati da gidajen ma’aikata domin rage matsalar muhalli ga jami’an gwamnati da kuma filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa.
Domin samun ra’ayin jama’a kan yadda yake gudanar da waɗannan ayyuka da sauran manufofi, Lamido ya buɗe layin wayarsa ga kowa a kowane lokaci. Ya ce wannan shi ne tsarin da yake bi duk lokacin da yake riƙe da muƙamin gwamnati.
C-Kammalawa
Babin ƙarshe na littafin, ya nuna yadda Lamido ya gode wa Allah bisa shiryar da shi a tafiyarsa ta siyasa, wadda mafi yawanta ta kasance mai nasara. Idan aka cire rashin nasarar zama Shugaban Ƙasar Najeriya, Lamido ya yi nasarar samun sauran muƙaman siyasa da ya nema. Ya ce bayan ya zama Gwamna, bai taɓa son idan ya sauka ya nemi kujerar Sanata ba, kamar yadda wasu tsofaffin abokan aikinsa suka yi. Ya ɗauki muƙamin Gwamna da matuƙar daraja kuma bai taɓa son yin wani abu da zai rage darajar wannan matsayi a idanun jama’a ba.
Yanzu da yake da shekaru 77 a duniya, Lamido har yanzu yana nan a cikin hidimar siyasa kuma yana cikin Jam’iyyar PDP, duk da ƙalubalen da jam’iyyar take fuskanta a yanzu. An amince da shi a matsayin mutum mai ƙa’ida da kuma kyawun ɗabi’a. An aminta da shi a ƙasa ta hanyoyi daban-daban, ciki har da ba shi digirin girmamawa na Doctor of Philosophy a Federal University of Agriculture Abeokuta. Ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Jam’iyyar PDP, musamman a cikin fitattun ’yan siyasa tara da aka sani da ‘G9’ waɗanda suka haɗa kai a zamanin Gwamnatin Abacha, domin ganin an kawar da soja daga mulki.
__________
Dr. Bukar Usman, OON tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Ƙungiyar Nigerian Folklore Society na yanzu.












