• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

BAKIN JAƁA (7)

Labarin Cin Amana

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 15, 2025
in Adabi
0
BAKIN JAƁA (7)

Bakin Jaɓa (7)

25
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BAKIN JAƁA (7)
(Labarin Cin Amana)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

ALHAMDU LILLAH

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Bakin Jaɓa (7)


                   _______________
Bayan mutuwar jaririn Jummalo, an sha marƙabu da jeka-ka-dawo tsakanin hukumomi, har zuwa dai daga ƙarshe aka bar maganar ta bi shanun sarki. Ma’ana dai babu wani hukunci da ya biyo bayan wannan aika-aika da ta aikata, domin a cewar su, babu wata ƙwakkwarar shaida da ta tabbatar da cewa ita ta halaka jaririn.

Ta faru ta ƙare, wai an yi wa mai dami ɗaya sata. Mahaifin Jummalo yana ji kuma yana gani, amma ba a son ransa ba, ɗiyarsa ta tsunduma kacokan cikin kasuwar jawarci. Ga ta dai yarinya ɗanya shar (sakin wawa), ba ciki kuma babu goyo. A kullum idan gari ya waye ba ta da aiki sai kwanciya, sai kallace-kallacen finafinai. Idan ta gaji da kallo, sai ta kunna sauti a akwatin MP3 ta ƙure iya ƙararsa, ta bi lafiyar katita. Babu ruwanta da salla balle salati. Kuma babu abin da ya shalli kakarta da innarta!

Hikima Drama Joint gida ne da ya shahara a garin su Jummalo. Matattara ce ta matasa maza da mata, da ma duk wanda ke son shaƙatawa. Sukan fara wasan kaɗe-kaɗe da raye-raye da misalin ƙarfe biyar na yammacin kowace rana, sannan kuma su ƙarƙare da wasan kwaikwayo na daɓe. Haka kuma da dare sukan ɗora daga inda suka tsaya, daga nan har tsakiyar zuwa dare. Jummalo ta maida gidan nan tamkar gidanta na biyu. Ko runhu mutum ya riƙo, madamar yana nemanta, to da ya zo gidan diramar nan zai same ta.

A kullum ta kasa samun nutsuwa, ta kuma daina sauraron shawarar iyayenta, musamman ma mahaifinta, wanda a kullum yake roƙonta ta gyara halinta amma kamar yana saran ruwa.

A cikin ‘yan wasan gidan Drama Hikima Joint, akwai wata yarinya da jininta ya haɗu da na Jummalo, inda suka zama ƙawaye. Kusan a kullum suna tare. Yarinya ce kyakkyawa, wacce kuma daga Kano take. Tana daga cikin jami’an da ke gudanar da shirye-shiryen wasan kwaikwayo da raye-raye a wannan gidan dirama. Sunanta Hajara amma an fi saninta da laƙanin Takano. Tana da hazaƙa sosai, domin ita ce ma jagaba a fannin rubuta wasannin kwaikwayo da ba da umurmi ga ‘yan wasa a gidan.

Wata rana da Jummalo ta je gidan dirama, sai ta samu wuri ta zauna ta yi jugum. Abin duniya duk ya taru ya caɓe mata. A daidai wannan lokaci ne ta yi ta tunani, tana tariyar yadda rayuwarta ta kasance. A yayin da take cikin nazari da tunani, sai ta ankara da wasu ‘yan mata su biyu, suna zaune a can gefe guda suna zuƙar sigari, suna ta annashuwa suna ƙyalkyata dariya, tamkar babu wata matsala da ke damun su a rayuwa.

A cikin wannan yanayi ne ƙawarta Takano ta zo ta same ta. Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana tsaye amma Jummalo ba ta san ta zo ba, domin kuwa idanunta suna kafe ga ‘yan matan nan da suke shan sigari, a yayin da ta lula cikin tunani.

“Juma, me ya faru ne?” Takano ce ta jefa mata tambaya da murya mai ƙarfi, a lokaci guda kuma ta muskuta, ta zauna kusa da ita.

“Kash, har kin ba ni tsoro,” in ji ta. Babu abin da ya faru. Kawai ina ta nazarin rayuwa ce, sai hankalina ya kai ga ‘yan matan can biyu. Na ga suna ta jin daɗinsu.

“Ke dai ki bi a hankali da rayuwar nan, kada ki je ki zautu. Ba ki san cewa yawan tunani yana kawo damuwa ba? Ita kuma damuwa idan ta yi yawa, takan sa mutum ya susuce. Ki tashi mu je mu ɗan sha Soɓo.”

Bayan sun isa wajen mai shago da ke cikin harabar gidan wasan, sun sayi abin sha, sai suka samu wani benci suka zauna. A nan ne Takano ta tsegunta wa Jummalo labarin ‘yan matan nan biyu da ta gani suna hira. Ta shaida mata cewa ai ƙawaye ne kuma masoyan juna. Ta shaida mata cewa ana zarginsu ma da cewa sun ɗaura auren jinsi a junansu, a asirce.

“Kuma gaskiya, mu ma ya kamata mu natsu, mu duba rayuwarmu domin gaba,” in ji Takano.

“Kamar yaya cewa mu duba rayuwarmu? Ban gane ba.” Jummalo ta faɗi haka, a yayin da ta juyo da fuskarta ta kalli ƙawarta kai tsaye, cikin mamaki.

“Abin da nake nufi shi ne,” a cewar Takano. “Kin ga a labarin da kika gaya mani, kin taɓa aure har kin haihu. Ni kuwa ban ko taɓa aure ba amma dukkanmu mun fitsare ƙafafunmu. Ni na baro iyayena a Kano, na zo nan na tare ina bariki. Ke kuwa a gaban naki iyayen kike shuka bariki. Ba ki ganin idan muka ci gaba a haka, rayuwarmu za ta lalace gaba ɗaya?”

“Ina jin ki. To me kike so mu yi yanzu?” Jummalo ta ƙara natsuwa, ta tsotsi Soɓo, a yayin da ta zura wa Takano idanunta dara-dara kamar na autan ƙururu.

“Abin da nake nufi shi ne, mu duba rayuwarmu, mu yi tunanin abin da zai fisshe mu. Misali, ni kin ga na gama digiri, don haka ya kamata in samu aiki mai kyau, kuma in samu mijin aure maimakon wannan zaman da nake yi a gidan dirama. Duk da cewa ina samun kuɗi sosai amma babu mutunci, domin kowa kallon ‘yar iska yake mani.

“Ke kuma Juma, me zai hana ki koma makaranta ki gyara jarabawarki ta WAEC, sannan ki shiga babbar makaranta? Kin ga ke yarinya ce, kina da sauran chance a gaba. Kin san fa wannan zamani ne na ilimi, duk wanda ya zauna da jahilci tam…”

Jummalo ta yi tunani sosai, ta kuma ji kamar wannan shawara ce ta gaskiya. Bayan wasu watanni, sai ta sake rubuta jarabawarta ta WAEC kuma ta yi nasara sosai. Kodayake ba ita ta rubuta jarabawar da kanta ba. Takano ce ta shirya da malamai, suka ba da cin hanci. Shi ne aka amince ta yi ɓadda-bami, ta shiga zauren jarabawar a madadin Jummalo.

(Za Mu Ci Gaba)
_______________

Previous Post

Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina: Ya Kamata A Tallafa Wa Iyalan Mutanen Da Aka Tarwatsa

Next Post

Taya Murna Ga Manaja Isma’il A. Sanda

Related Posts

ALHAMDU LILLAH
Adabi

ALHAMDU LILLAH

May 15, 2026
Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
Adabi

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
Next Post
Taya Murna Ga Manaja Isma’il A. Sanda

Taya Murna Ga Manaja Isma'il A. Sanda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
RAMADAN KARIM: 29-1447

RAMADAN KARIM: 29-1447

March 18, 2026
RAMADAN KARIM: 07-1447

RAMADAN KARIM: 07-1447

February 24, 2026
KANNYWOOD JIYA DA YAU: DARASIN RAYUWA DAGA WASU TAURARI (1)

KANNYWOOD JIYA DA YAU: DARASIN RAYUWA DAGA WASU TAURARI (1)

August 3, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.