Bayan Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina: Ya Kamata A Tallafa Wa Iyalan Mutanen Da Aka Tarwatsa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
A halin yanzu, bayan tattaunawa da sulhu da ake yi da ‘yan bindiga a wasu yankunan Jihar Katsina, akwai buƙatar gwamnatin jiha, a ƙarƙashin adalin Gwamna, Dokta Dikko Umar Raɗɗa, ta karkata hankali wajen kula da mutanen da suka fi fuskantar illar wannan rikici.
Duk da cewa manufar sulhu ita ce kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali, akwai daruruwan iyalai da suka rasa komai, daga rayuka, gidaje har zuwa dukiyoyi, waɗanda har yanzu ba su dawo hayyacinsu ba. Wannan rukuni na jama’a, bai kamata a manta da su ba a lokacin da ake ƙoƙarin gina sabon tsarin zaman lafiya.
Gwamnatin Jihar Katsina tare da shugabannin ƙananan hukumomi, ya kamata su taka wata rawar gani wajen shirya wani shiri na musamman domin tallafa wa waɗannan iyalai. Misali a Ƙaramar Hukumar Malumfashi, akwai marigayi ASP Ɗahiru, wanda a kwanakin baya ‘yan bindiga suka kama, ya kwashe tsawon lokaci a hannunsu, sannan suka raba shi da rayuwarsa kuma suka hana iyalansa gawarsa. Bayan shi, akwai wasu da dama a sassa daban-daban na jihar.
Ga mutanen da aka tarwatsa ƙauyukansu, tallafi gare su bai kamata ya tsaya ga kayan abinci kaɗai ba. Ya dace a haɗa da sake gina gidajen da suka ƙone, ba da jari ga mata da matasa da suka rasa hanyar samun abin dogaro da kuma shirye-shiryen ilimi da kiwon lafiya ga yara da tallafi na musamman ga tsofaffi. Hakan zai tabbatar da cewa waɗanda suka tsinci kansu cikin wahala sakamakon ta’addancin ‘yan bindiga, ba za su zama masu tabbata cikin rayuwar zaman gudun hijira a ƙasarsu ba.
Haka kuma, akwai buƙatar a kafa wani kwamitin kulawa da farfaɗowar al’umma, wanda zai duba yankunan da aka fi lalatawa, tare da nazarin hanyoyin da za a dawo da su cikin tsarin rayuwa mai ma’ana. Wannan kwamitin zai ƙunshi jami’an gwamnati, shugabannin al’umma, malamai da ƙungiyoyin agaji, domin tabbatar da cewa tallafin da ake bayarwa ya isa ga waɗanda suka fi buƙata, ba tare da nuna son kai ko fifiko ba.
Bugu da ƙari, gwamnati ta kamata ta samar da hanyoyin tsaro da sa ido a yankunan da aka ƙulla sulhu, domin kauce wa sake dawowar ‘yan bindiga. Mutanen da aka tilasta barin gidajensu su samu tabbaci cewa idan suka koma, za su rayu cikin aminci. Wannan mataki ne da zai ƙarfafa imani da gwamnati kuma ya rage yuwuwar komawar wasu cikin ‘yan gudun hijira ga hanyoyin laifi saboda matsin tattalin arziki.
Har kullum dai ya kamata mu san cewa, sulhu ba zai cika ba idan ba a kula da waɗanda suka shiga matsala a sakamakon harin ‘yan bindiga ba. Zaman lafiya na gaskiya yana nufin dawo da martaba da mutuncin rayuwar al’umma. Don haka, kira ga gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi shi ne, a gaggauta samar da shirin tallafi na musamman ga iyalan da aka tarwatsa, domin su samu ƙarfin gwiwa, su bar bara da gudun hijira, su koma zama ‘yan ƙasa masu alfahari da ƙasarsu.
_______________












