Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
A makon da ya gabata, wanda ya faro daga ranar Litinin 17 zuwa 23 ga Agusta, 2026, an gudanar da al’amura masu yawan gaske a Jihar Katsina, musamman ma ayyukan da suka danganci bunƙasa rayuwar al’ummar jiha, a ƙarƙashin jagorancin mai girma Gwamna Hadimin Talakawa, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, CON.
A makon da ya gabata ne, a ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, CON, ya ƙaddamar da shugabannin Ƙungiyar APC Zalla, na ƙananan hukumomi 34 da mazabu 361 da suke a faɗin jihar.
Ƙungiyar, wadda Sadaukin Kankia, Dakta Bala Nuhu Kankia ya kafa kuma yake jagoranta, an ƙaddamar da ita ne a filin taro na People’s Square da ke Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa a yanzu al’umma ba sa kallon alƙawuran da ake yi musu kawai, illa ayyukan da gwamnati ta gudanar a zahiri. Ya ce ayyukan da gwamnati ta aiwatar a faɗin jihar a bayyane suke kuma al’umma za su iya tantance su tare da yin hukunci a lokacin zaɓe.

Wasu daga cikin manyan da suka halarci taron, sun haɗa da tsohon Ministan Gidaje a Gwamnatin Tarayya, Arch. Ahmed Musa Dangiwa da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Hon. Bishir Gambo Saulawa da manyan ‘yan siyasa, kwamishinoni, masu ba Gwamna shawara, shugabannin jam’iyya, matasa, maza da mata da sauran al’umma daga sassa daban-daban na Jihar Katsina.
Haka kuma, duk dai a ranar ta Juma’a, 21 ga Agusta, 2026, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya gana da masu ruwa da tsaki na Ƙaramar Hukumar Ingawa, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Abubakar Idris 02.
Waɗanda suka yi jawabi a yayin taron, sun haɗa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Ingawa, Hon. Abubakar Idris 02 da Ubandoman Katsina, Hakimin ‘Yandoma, Alhaji Muntari Dambo da Ɗan Majalisar Jiha mai wakiltar Ingawa, Hon. Abubakar Sulaiman Tunas da Shugaban Masu Ruwa da Tsaki na Karamar Hukumar, Engr. Mustapha Mahmud Kanti. Dukkansu sun gabatar da godiya ga Gwamnan bisa ayyukan raya ƙasa da gwamnatin jihar ta gudanar a Karamar Hukumar Ingawa, tare da nuna cikakken goyon baya ga Gwamna da Jam’iyyar APC a zaɓukan da ke tafe.
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya gode wa al’ummar Karamar Hukumar Ingawa, bisa goyon baya, haɗin kai da amincewar da suke ba gwamnatinsa. Ya kuma bayyana farin cikinsa bisa yadda ya ga masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar suka haɗa kai tare da fahimtar juna a harkokin siyasa.

Taron ya samu halartar PPS na Gwamnan, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji; Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Engr. Sani Magaji Ingawa; Kwamishinan Wasanni da Matasa, Hon. Surajo Yazeed Abukur; Hon. Bala Sani Yaya; Hon. Labaran Magaji; Hon. Danlami Ingawa; Mai Martaba Sarkin Fulani Dambo, Alhaji Tukur Sulaiman Dambo; Hon. Akilu Mamman Yandoma; Dr. Bilyaminu Sulaiman; Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar, Hon. Yahya Champion, Kansiloli, ‘yan siyasa, mata, matasa da sauran masu ruwa da tsaki na Karamar Hukumar Ingawa.
A ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da rabon muhimman kayayyakin aiki da magunguna ga cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a faɗin jihar.
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ce ta jagoranci shirin ta hannun Hukumar Kula da Magunguna da Kayayyakin Lafiya ta Jihar (DMSA), tare da tallafin Ƙungiyar Baitulmaal da shirin State-Wide Approach Programme (SWAP).
Gwamnan ya kuma umarci hukumomin lafiya da su tabbatar da adalci da gaskiya wajen rabawa, tare da tabbatar da an yi yadda ya kamata wajen amfani da kayayyakin da kuma kula da kayan aikin, domin su daɗe suna aiki yadda ya kamata.
Mahalarta taron sun haɗa da Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe da Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, Kwamishinoni da sauran Jami’an Gwamnati.
Sai kuma a jiya Lahadi, 23 ga Agusta, 2026, inda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da rabon tallafin abinci, kuɗaɗe da sauran kayan agaji ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Musawa, waɗanda hare-haren ‘yan ta’adda ya shafa.
Tallafin ya samu ne sakamakon haɗin gwiwar shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar, musamman Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Abdullahi Aliyu (Dujiman Katsina). Sun tanadar da kayayyakin ne, domin tallafa wa al’ummar yankin tare da rage musu raɗaɗin halin da suke ciki.
A yayin ƙaddamar da tallafin, an raba buhunan shinkafa 1,500 da buhunan taki 200, yayin da Hon. Abdullahi Aliyu Ahmad (Dujiman Katsina), ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 30 domin tallafa wa al’ummomin da lamarin tsaro ya shafa, ya kuma ba da Babura 109, ga masu gari, da sauran mutanen da suka hidimta masa a siyasa.
Sauran waɗanda suka ba da gudunmuwar akwai Muhammad Abu Ibrahim, Ministar Al’adu, Fasaha da Tattalin Arziki, Hon. Hannatu Musa Musawa (Naira miliyan 10), Alhaji Muttaqah Badaru (Naira miliyan 5), Hajiya Zainab Musa Musawa (Naira miliyan 5), Nura Tela (Naira miliyan 5) da sauran shugabannin siyasa da ‘yan asalin yankin.
Da yake jawabi, Gwamna Radda ya yaba da wannan kyakkyawan yunƙuri na ‘ya’an Musawa da Matazu, yana mai bayyana tallafin a matsayin wata muhimmiyar gudunmawa wajen rage wa al’ummar da suka fuskanci hare-haren ta’addanci raɗaɗin halin da suke ciki.
Waɗannan su ne kaɗan daga cikin muhimman al’amuran da suka wakana a Jihar Katsina a makon da ya gabata. Sai kuma ƙarshen wannan makon, idan Allah ya kai mu, za mu sake kawo maku sabon shiri. A huta lafiya.
__________












