• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, September 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

TA'AZIYYA

Bukar Usman, OON by Bukar Usman, OON
August 22, 2026
in Adabi
0
Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

Marigayi Farfesa Bello Sa'idu

74
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Daga Dakta Bukar Usman

Related posts

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

August 29, 2026
Marigayi Farfesa Bello Sa’idu

__________
Innah lillahi wa innah ilaihi rajiun!

Allah ya yi wa tsohon malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Bello Sa’idu rasuwa a Kano, ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 2026. Rai ya yi halinsa.

Da fari na so in rubuta wannan ta’aziyya da Turanci saboda bayan harshena na Babur/Bura, ina rubutu a cikin harsunan guda biyu, watau Hausa da Turanci amma na fi sakin jiki da yin rubutu da Turanci.

Bayan haka, ya kamata in rubuta ta’aziyyarsa da harshen Hausa, domin harshen Hausa ne sanadiyyar hulɗar da na yi da shi ta fiye da shekaru ashirin.

Dangantaka da mu’amala cikin mutunci tsakanina da Farfesa Sa’idu, ta faro asali ne a lokacin da na fara rubuce-rubucen tatsuniyoyi a cikin harshen Hausa. Na nemi taimakon wasu mutane ƙwararru a harshen. Salisu Saleh Na’inna Dambatta, wani tsohon jami’in sadarwa a Gwamnatin Tarayya ya haɗa ni da Farfesa Gangaran Dandatti Abdulƙadir, kuma tsohon Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, domin duba waɗannan littattafai da yin gyare-gyaren da suka dace a cikinsu.

Jerin littattafan Taskar Tatsuniyoyi daga na 1-14 da na Ajami da kuma babban kundi ɗaya

Bayan ni da Farfesa Ɗandatti mun haɗu a Abuja, sai ya haɗa ni da wasu jami’an Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya a Jami’ar. Ɗaya daga cikin su shi ne Farfesa Bello Sa’idu. Daga nan fa muka haɗa gwiwa, har ta kai ya yi aikin editan littattafaina har goma sha huɗu, a matakin ƙarshen kammala su. Shi ne ya fitar da darusan da kowace tatsuniya ta ke nusarwa, tare da gina jimlolin cikin littafan, bisa tsari da ƙa’idar rubutun Hausa.

Da na tashi haɗe littattafan a kundi ɗaya, Farfesa Sa’idu ne ya ƙirƙiro sunan kundin, watau ‘Taskar Tatsuniyoyi’ wanda muka fitar a shekarar 2010.

Hagu zuwa Dama: Bangon ‘Taskar Tatsuniyoyi’ Bugu na farko da na biyu

Sunan da ya raɗa wa littafin, watau ‘Taskar Tatsuniyoyi,’ ya zauna daram saboda ya dace kuma ya jawo min ƙauna da yabo masu yawa a ciki da wajen Najeriya. A sanadin ayyukan da ya yi na gyara da taskance tatsuniyoyi a harshen Hausa, ni da Farfesa Sa’idu mun ƙulla zumunta da ƙaunar juna har ƙarshen rayuwarsa.

A duk lokacin da na halarci taron Kungiyar Manazarta Fasaha da Al’adun Gargajiya ta Najeriya (Nigerian Folklore Society) a Kano, mukan gana da juna. Tun da ina Abuja da zama, shi kuma yana Kano, mukan gaisa ta waya jefi-jefi, domin jaddada danƙon zumuncin da Allah ya ƙulla tsakanin mu.

Ana kamar saura kwana biyar Allah ya yi masa rasuwa, sai ya buga min waya muka gaisa cikin lumana da kwanciyar hankali. Daga nan sai ya ce yana neman ahuwata saboda duk da ƙarfin zumunci da mutuncin da ke tsakanina da shi na shekara da shekaru, bai gaya min rashin lafiya da jinyar da ya daɗe yana yi ba. Ya bayyana sanadin rashin lafiyar, da ƙoƙarin da yake yi na neman waraka.

Sai fa a safiyar 17 ga watan Agusta 2026, na ga wayarsa. Ban sami damar amsawa ba sai daga baya na kira amma ba a amsa ba. Sai can da yamma aka sake kira na da wayarsa. Da na ɗaga sai na ji ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, Malam Salim ne yake magana.

Kaico! A nan ne fa Malam Salim ya sanar da ni rasuwar mahaifinsa kuma a lokacin suna shirin yin jana’izar shi ne. A nan take na isar da ta’aziyya ta ga Malam Salim da iyalan marigayin.

Ba zan manta da gagarumar gudunmawar da Farfesa Sa’idu ya bayar, ba tare da gajiya wa ba. Ya yi amfani da lokacinsa wajen tsifa da tace littattafaina guda goma sha huɗu a cikin harshen Hausa da kuma tsara ‘Taskar Tatsuniyoyi.’

Wani babban abin ƙayatarwa da tunawa da ya yi, shi ne sa albarka a ‘Taskar Tatsuniyoyi.’ A ranar 25/10/2010 ya rubuta cewa: “Babbar manufar yin tatsuniya a al’adar Bahaushe ita ce koya wa yaro kyawawan ɗabi’u, domin ya aiwatar da su da kuma nusantar da shi munanan ɗabi’u, domin ya nisance su. Wannan zai ba shi damar samun jagora da samun nasara a rayuwarsa.”

Ya ƙara da cewa: “Da ma dai tun lokaci mai tsawo ake yi wa ɗa tatsuniya, domin ita ce makaranta ta farko da zarar fara iya magana. Galibi kakanni mata ne malaman wannan makaranta; su ne suke tara yara da daddare bayan sun ci abinci su dinga yi musu tatsuniya.”

Farfesa Sa’idu, wanda ya rasu yana da shekara 86 a duniya, ya bar ‘ya’ya bakwai da uwargidansa. Ya yi suna wajen riƙe addini da yawan ibada, har ma ya yi limancin masallaci a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Farfesa Bello Sa’idu, wurin jama’a, ya kasance fitaccen masani a fannin harshen Hausa da adabinsa, marubuci, malami, kuma limamin da ake girmamawa.

Marigayin ya sadaukar da tsawon rayuwarsa wajen neman ilimi da yaɗa shi ga al’umma. Ya kasance cikin malaman ƙasar nan na farko da suka taimaka wajen bunƙasa Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya (Centre for the Study of Nigerian Languages) a Jami’ar Bayero da ke Kano. Tsawon shekaru da dama na koyarwa da bincike, ya bayar da gagarumar gudunmawa mai ɗorewa wajen haɓaka harshen Hausa, adabinsa, waƙoƙinsa, fassara, da kuma suka da sharhin adabi.

Ayyukan da ya wallafa sun nuna faɗin iliminsa da ƙwarewarsa. Daga cikinsu akwai:
• Ka’idojin Rubutun Hausa
• Daidaita Hanyar Rubutun Ajamin Hausa da Inganta Shi
•Tarbiyya a Musulunci
• Dausayin Soyayya
• الموجز في أصول الفقه

Ayyukansa na ‘Dausayin Soyayya’ sun kasance muhimmiyar gudunmawa wajen nazari da kuma adana waƙoƙin Hausa. A dunkule, littattafansa sun ƙara wadata ilimin Hausa da na Musulunci, kuma har yanzu suna ci gaba da amfanar ɗalibai, malamai, masu bincike da marubuta.

A lokacin rasuwarsa, ana kan shirya wani muhimmin kundin bincike nasa mai suna Gudunmawar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa domin wallafa shi. Asali dai, wannan kundin bincike shi ne kundin karatunsa na digiri na biyu (Master’s thesis), wanda ya yi nazari kan gudunmawar shugabanni da malaman Jihadin Sakkwato ga adabin Hausa. Abin baƙin ciki, ya rasu kafin ya ga an buga wannan aiki nasa.

Haka kuma, gudunmawar iliminsa ta kai har ga hidimar Alƙur’ani Mai Girma. Ya taka rawa wajen samar da tafsiran Alƙur’ani guda biyu a harshen Hausa.

Tsawon fiye da shekaru ashirin, ya kasance Limamin Masallacin Jami’ar Bayero. Allah ya jikansa, ya sa aljanna ce makomarsa.

__________
Dakta Bukar Usman, OON
Tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Kasa kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Manazarta Fasaha da Al’adun Gargajiya ta Najeriya (21/8/2026)

Previous Post

Musulunci Ba Addinin Tsauri Ko Sakaci Ba Ne…

Next Post

Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

Related Posts

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
Adabi

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa
Adabi

Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

August 29, 2026
ALBARKAR HAUSA
Adabi

ALBARKAR HAUSA

August 26, 2026
Next Post
Professor Bello Sa’idu: The Demise of a Literary Icon

Professor Bello Sa'idu: The Demise of a Literary Icon

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

August 19, 2023
KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU JUMA’A

KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU JUMA’A

February 6, 2026
Janar Buratai: Sarki Mai Littafi

Janar Buratai: Sarki Mai Littafi

July 6, 2023
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

December 30, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
  • Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
  • SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.