Nazari Da Sharhin Littafin Tarihin Garin Lassa
Daga: Bukar Usman
__________
Sunan Littafi: A History of Lassa (Tarihin Garin Lassa)
Marubuci: Abdulkadir G. Gadzama
Kamfanin Wallafa: Solstice Technologies Nig. Limited
Shekarar Wallafa: 2018
Yawan Shafuka: 283
Farashi: Ba a bayyana ba
Mai Sharhi: Bukar Usman
__________
Yau shekaru hamsin ke nan da Dakta Jordi Casals-Ariet, ƙwararren masanin cututtuka (epidemiologist), ya gano ƙwayar cutar Zazzaɓin Lassa kuma kusan ya rasa ransa yayin gudanar da wannan bincike; ya sanya garin Lassa ya shahara a duniya, sakamakon sanya wa cutar sunan garin, tare da sanar da wannan bincike nasa a shekarar 1969.
Yanzu kuma sai ga Abdulkadir G. Gadzama ya zo da wani tarihi na daban game da Lassa, lokacin da ya wallafa littafinsa mai taken A History of Lassa (Tarihin Garin Lassa), garinsu na haihuwa, a shekarar 2018.
Yayin da labarin da ya shafi asalin cutar daga dabbobi zuwa mutane (zoonotic) ke jawo wa garin Lassa wani irin kallon ƙyama da nuna wariya, bayanin da Gadzama ya gabatar ya yi ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a zuwa ga ɗaukakar tarihin garin na Lassa, tare da bayyana yadda garin ke cike da albarka da ci gaba a wannan zamani.
Lassa ya kasance “ƙaramin matsuguni” ne a shekarar 1904, lokacin da tarihinsa a matsayin wani yanki na ƙasa ya fara tabbatuwa a rubuce. Amma zuwa shekarar 2018, lokacin da aka wallafa tarihin da Gadzama ya rubuta, garin ya bunƙasa zuwa “babban gari mai gundumomi biyu,” inda kuma “yawan al’umma ya ƙaru matuƙa.”
Gadzama ya jima yana ɗauke da burin rubuta tarihin Lassa a zuciyarsa, garin da ya taso a cikinsa kuma wurin da ya tara ɗimbin abubuwan tunawa masu daraja na ƙuruciyarsa. Sai dai kuma littafin nasa mai babi 27, bai rubuta shi wai domin tayar da tsoffin abubuwan tunawa kawai ba ne. Babbar manufarsa, ita ce bayyana ingantattun ɗabi’u da al’adun gargajiya na Lassa, tare da fito da irin keɓantacciyar rayuwa da halayen al’ummar asalin yankin Marghi (Margi), waɗanda aka san su da karamci, kyakkyawar mu’amala da kuma juriya.
Labarin Lassa Mai Ɓangarori Biyu
Littafin Tarihin Garin Lassa na Gadzama ya ƙunshi ɓangarori biyu masu alaƙa da juna: ɓangaren Marghi da kuma ɓangaren Lassa, inda Lassa ke wakiltar wani ɓangare na tarihin ƙasar da al’ummar Marghi suka zauna.
Marghi wata ƙabila ce da aka fi samu a jihohin Adamawa da Borno a Najeriya, yayin da wasu daga cikinsu ke zaune a ƙasashen Kamaru da Chadi. An san su da tufafinsu na audugar da ake saƙawa da hannu mai suna Gumbara da kuma irin abincinsu na musamman, na Kifi Kubakuba (wani abinci da ake haɗawa da kifi da ganyayyaki). Duk da cewa Marghi ƙabila ce marar rinjaye, tana da tarihin da ya cancanci a yi alfahari da shi, wanda ya samo asali tun a ƙarni na 13.
Ƙabilar Marghi, wadda dangin marubuci Gadzama (Mingi) suka fito daga cikinta, ta dangana da ƙasar Borno a shekara ta 1250 Miladiyya, lokacin da Borno take cikin babbar Daular Kanem. Sun zauna a yankin tun kafin zuwan Kanuri (Barebare), waɗanda daga baya suka zama ƙabila mafi rinjaye. A zamanin Daular Kanem-Borno ƙarƙashin mulkin Mai Idris Alooma, an kai yaƙi kan Margi tsakanin shekarun 1564 zuwa 1576, saboda dalilan tattalin arziki da kuma ƙoƙarin musuluntar da su. Wannan kuwa ya faru ne tun kafin kafuwar Najeriya a shekarar 1914.
A cewar marubucin, Marghi, kasancewarsu babbar ƙabila, sun samo asali ne daga ƙasar Habasha (Ethiopia) ko ma can gaba, wadda ake kallonta a matsayin tushen mahaifar ɗan Adam, kafin daga bisani suka nufi yankin Tafkin Chadi. Saboda tsananin barazanar rashin tsaro da ta samo asali daga maharan bayi da ‘yan fashi, tare da burin kare asalinsu da al’adunsu, ƙabilun Marghi, ciki har da dangin Gadzama, suka ci gaba da matsawa zuwa kudanci, domin neman wurin da za su zauna na dindindin.
Marubucin ya bayyana cewa mutanensa sun taɓa mamaye Unguwar Mafoni da wasu sassan Unguwar GRA (Government Residential Area) ta Maiduguri, babban birnin Jihar Borno na yanzu. Daga baya Kanuri suka kore su daga yankin, sannan kuma rundunonin mulkin mallaka na Faransa da Birtaniya suka sake tarwatsa su, yayin yaƙin da suka yi da Rabeh Fadelllah da ɗansa Fadarallah (Fadellah) wanda ya gaje shi.
A shekarar 1907, babban rukuni na Marghi da aka raba da muhallinsu ya ci gaba da tafiya zuwa kudanci, suna tsayawa a wurare daban-daban a hanya. Wasu daga cikinsu kuwa sun zauna a inda suka isa ko kuma suka haɗu da wasu al’ummomi, inda daga baya suka gaurayu da su; lamarin da ya sa suka rasa wani ɓangare na asalinsu.
Duk da haka, babban rukunin Marghi bai karaya ba. Sun ci gaba da wannan hijira domin neman ingantaccen wurin zama, da nufin cin ma babban burinsu na samun muhalli mai aminci, inda za su iya kare asalinsu da al’adunsu ba tare da gurɓacewa ba. Wannan tafiya ba ta kasance mai sauƙi ba, domin sun fuskanci ƙalubale da dama a hanyarsu. Wurin ƙarshe da suka tsaya kafin su zauna a Lassa shi ne Dilli (Dille).
Dangane da yadda aka samo sunan sabon matsugunin, marubucin ya bayyana cewa lokacin da wata tawaga ta tashi daga Dilli, domin nemo sabon wurin zama, wani dattijo ɗan Marghi mai suna Abana Tami Abau-kumi, wanda ya ƙi tafiya tare da su, ya gargaɗe su da harshensu na gida da kalmar “la sa,” wadda take nufin “za ku je ku ɓace” ko “kun shiga haɗarin ɓacewa.” Saboda haka, lokacin da suka yanke shawarar zama a sabon wurin, sai suka ba shi suna “La sa.” Daga baya jami’an mulkin mallaka na Birtaniya, kamar yadda suka yi wa wasu wurare da dama, suka sauya lafazin sunan zuwa “Lassa.”
Jagoran wannan balaguron bincike daga Dilli, shi ne ɗaya daga cikin dattawan Marghi mai suna Dzarma Abana Yelima Gadzama. Yana tare da bawansa da wasu mutane, lokacin da suka hango wani karan dawa tsaye a cikin wani daji. Karan dawar, yana ɗauke da ƙatuwar zangarniya cike da ƙwayoyi, wanda ba a saba gani ba. Bai san yadda dawar ta tsiro a wurin ba. Baya ga haka kuma, ƙasar dajin ta cika da takin kashin tana.
Don haka sai ya yanke kan dawar kuma ya ɗebi takin nan na kashin tana, ya tafi da shi, ya kai wa mutanensa a Dilli, ya nuna masu. Girman kan dawar da kuma alamomin ni’imar ƙasar da tana ta bari, sun zama hujjoji ƙarara cewa yankin yana da ƙasa mai albarka. Saboda haka aka zaɓi wurin a matsayin sabon matsuguni. A shekarar 1904, mutanen Marghi da ke Dilli suka yi hijira zuwa wannan wuri. Mutanen da suka kafa garin da farko da dangin Gadzama, su ne suka raɗa masa suna Lassa.
Daga baya aka gano cewa a Kudu Maso Gabashin wannan matsuguni, akwai faffadar ƙasa mai matuƙar albarka da kogin Yedzaram ya tara, wanda tushensa yake daga Dutsen Mandara, sannan ruwansa ke kwarara zuwa Tafkin Chadi.
A cewar marubucin, Lassa ta taɓa kasancewa cikin yankin mulkin Jamus, kafin daga baya ta faɗa ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya. Bayan sun zauna a Lassa, sauran tarihin ya mayar da hankali ne kan irin ƙoƙarin da shugabannin Marghi daban-daban suka yi, wajen ƙarfafa ‘yancin kansu, tabbatar da zaman lafiya da maƙwabtansu da kuma inganta rayuwar al’ummarsu.
Marubucin ya bayyana cewa, duk da sauye-sauyen da aka samu a sarautar Marghi ta Lassa, mafi yawan waɗanda suka hau karagar mulkin, sun fito ne daga zuriyar Gadzama. Ya fara ne da ba da labarin yadda aka amince da sarautar gargajiya ta Marghi mai suna Ptil (Sarki) a hukumance, a shekarar 1911.
A lokacin mulkin mallaka, naɗin wanda zai zama Ptil yana buƙatar amincewar Lamiɗo na Adamawa da ke mazaunin Yola, wanda shi ne babban mai iko na gargajiya a yankin, tare da kuma amincewar jami’an mulkin mallaka na Birtaniya, ƙarƙashin tsarin Indirect Rule (Mulkin Kaikaice Ta Hannun Sarakunan Gargajiya).
Kodayake an samu lokutan da wasu sarakuna suka sauka daga mulki da kansu, aka tuɓe wasu daga sarauta, aka mayar da wasu, har ma wasu suka yi mulki sau biyu, sarautar Ptil ta ci gaba da wanzuwa har zuwa yau. Marubucin ya yi bayanin manyan nasarori da kuma ƙalubalen da aka fuskanta a zamanin kowane daga cikin sarakunan Lassa.
Har ila yau, littafin ya yaba da irin gudunmowar da ‘yan asalin Lassa suka bayar wajen bunƙasa garin, musamman rawar da fitattun mutane na farko suka taka.
Daga cikin Rataye biyu (Appendices) da littafin ya ƙunsa, Rataye Na I ya lissafo sunayen mutane 51 daga cikin al’ummar Marghi na farko, waɗanda suka ba da gagarumar gudunmowa a matsayin malamai da ma’aikatan asibitoci a ƙasar Marghi, tare da nuna musu godiya.
Rataye Na II kuwa, ya ƙunshi hotunan wasu fitattun gine-gine da kadarori da aka lalata a garin Lassa a watan Disamba na shekarar 2014, inda hakan ya zama tarihi mai nuna mummunar ɓarnar da ƙungiyar Boko Haram ta haddasa.
Gudunmowar Jami’an Mishan
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan tarihi da suka bar gagarumin tasiri mai ɗorewa a rayuwar zamantakewa, tattalin arziki, har ma da wani ɓangare na rayuwar siyasar Lassa da ƙasar Marghi baki ɗaya, shi ne isowar jami’an Mishan na Church of the Brethren Mission (CBM) daga Amurka.
Jami’an Mishan na farko daga Amurka, sun haɗa da Mista (daga baya Fasto) H. Stover Kulp, wanda likita ne da kuma Mista (daga baya Fasto) Albert D. Helser. Bayan isowarsu Arewa maso Gabashin Najeriya a shekarar 1923, sun fara kafa cibiyarsu a Garkida, bayan sun samu amincewar gwamnati. Daga nan ne suka kafa wata cibiyar mishan a Dille (Dilli) a shekarar 1927, sannan daga bisani suka mayar da hedikwatarsu zuwa Lassa a shekarar 1928.
Baya ga aikin yaɗa addinin Kirista, jami’an na Mishan sun kafa makarantu tare da koyarwa a cikinsu. Haka kuma sun gina asibitoci, inda suke ba da magani ga marasa lafiya daga kusa da nesa. Sun kuma koyar da al’ummar yankin sana’o’i daban-daban na hannu da kuma dabarun noma na zamani, ciki har da gabatar da sababbin nau’ukan amfanin gona da ingantattun hanyoyin noma.
Bugu da ƙari, sun inganta koyarwa da koyo cikin harshen Marghi. Domin rage wahalar aikin niƙan hatsi da ake yi da hannu, sun gabatar da injinan niƙa, waɗanda suka sauƙaƙa wa al’umma nauyin aiki ƙwarai.
Domin nuna godiya ga irin gudunmowar da jami’an Mishan suka bayar, ba tare da son rai ko neman wani sakamako ba, wajen bunƙasa ƙasar Marghi da yankunan da ke kewaye da ita, marubucin ya yi musu gagarumin yabo. Ya ƙara nuna godiyarsa ta hanyar wallafa hotuna 46 na wasu mutane da ma’aurata baƙi daga Cocin Amurka, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen gudanar da aikin Mishan a Najeriya baki ɗaya, musamman a Lassa da tsakanin al’ummar Marghi.
Marubucin ya bayyana cewa irin waɗannan mutane sun fi cancanta a saka musu da alheri saboda sadaukarwar da suka yi (Babi na 18, shafuffuka na 171–194).
Batu Game Da Zazzabin Lassa:
Abin takaici, a shekarar 1969, ɗaya daga cikin jami’an Mishan da suka zo daga ƙasashen waje, wadda ma’aikaciyar jinya ce, ta rasa ranta sakamakon wata cuta mai ban tsoro kuma mai ruɗani, wadda daga baya aka sanya wa suna “Zazzaɓin Lassa” (Lassa Fever). Ta kamu da ƙwayar cutar ce, yayin da take kula da marasa lafiya, sannan aka kai ta birnin Jos, domin samun ƙarin kulawa amma daga bisani ta rasu a can.
Wannan lamari ya tayar da hankalin Dakta Jordi Casals-Ariet, wani ƙwararren masanin ilimin yaɗuwar cututtuka (epidemiologist) ɗan ƙasar Amurka, wanda ya fara gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan cuta da ba a san asalinta ba, kuma wadda a wancan lokacin ba ta da magani. A cikin shekarar 1969, Dakta Casals-Ariet ya gano ƙwayar cutar da ke haddasa wannan zazzaɓi, sannan ya sanya mata suna “Lassa,” bisa sunan garin da aka fara gano majiyyaciya ta farko, daidai da al’adar sanya wa ƙwayoyin cututtukan zazzabin zubar jini (hemorrhagic fever viruses) suna, bisa la’akari da wurin da aka fara gano su.
Kodayake sanya wa wannan ƙwayar cuta suna Lassa ya ci gaba da jawo wa garin wani nau’in ƙyama da tozarci, abin da mutane da dama ba su gamsu da shi ba, amma abin takaici, sanya wa ƙwayoyin cututtukan zazzaɓin zubar jini suna, bisa la’akari da wuraren da aka fara gano su, ya kasance wata al’ada da aka saba bi.
Daga cikin ƙwayoyin cututtukan zazzaɓin zubar jini da aka sanya musu suna bisa la’akari da wuraren da aka fara gano su, akwai Guanarito Virus (mai haddasa zazzaɓin zubar jini na Venezuela), wadda aka sanya mata suna daga yankin Guanarito da ke ƙasar Venezuela; Junin Virus (mai haddasa zazzaɓin zubar jini na Argentina), wadda aka sanya mata suna daga lardin Junin na ƙasar Argentina; Machupo Virus (mai haddasa zazzaɓin zubar jini na Bolivia), wadda aka sanya mata suna daga Kogin Machupo da ke ƙasar Bolivia; da kuma Lujo Virus, wadda aka samo sunanta daga haruffan farkon biranen Lusaka na ƙasar Zambia da Johannesburg na ƙasar Afirka ta Kudu, birane biyu da suka kasance cikin annobar cutar da ta ɓarke a shekarar 2008.
Saɓani guda ɗaya kaɗai da aka taɓa samu, wajen saka wa cututtuka sunayen yankin da aka gano su, ta faru ne a shekarar 1976, lokacin da Ƙungiyar Masu Bincike Kan Cutar Ebola, saboda ƙudirinsu na kauce wa danganta cutar da wani taƙamaiman gari (al’ada da a tarihi ta kasance tana jefa al’ummomi cikin ƙyama da tozarci), kamar yadda ya faru da garin Lassa, inda aka fara samun majiyyaciya ta farko, suka yanke shawarar sanya wa ƙwayar cutar suna bisa wani muhimmin fasalin ƙasa (geographical feature), maimakon wani taƙamaiman wuri.
Saboda haka, duk da cewa babbar annobar farko ta cutar Ebola, ta ɓarke ne a shekarar 1976, a ƙauyen Yambuku da ke Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), ƙungiyar masu binciken ta yanke shawarar sanya mata suna Ebola Virus, bisa la’akari da sunan Kogin Ebola da ke kusa da yankin.
Abin da labarin Ebola yake nunawa, shi ne cewa al’adar sanya wa ƙwayoyin cututtukan zazzaɓin zubar jini suna, bisa la’akari da wurin da aka fara gano su, ba wajibi ba ne. Kuma ana iya watsi da shi saboda dalilan jin ƙai da zamantakewa. Laƙaba wa wani gari bala’in kamuwa da wata ƙwayar cuta, ya isa abin takaici amma nacewa a sanya wa cutar sunan wannan gari, wanda hakan ke haifar masa da ƙyama da tozarci, ra’ayi ne mara kyau da ya kamata masana ilimin yaɗuwar cututtuka su sake dubawa, su canja. Maimakon haka, za su iya ƙirƙirar sunan da ya dogara da wata siffa ta musamman ta cutar, ko wani abin la’akari dabam, wanda ba zai jefa garin da aka fara gano majiyyacin farko cikin ƙyama ko tozarci ba.
Batutuwan Al’adu Da Zamantakewa
Kodayake iyakar yankin Lassa ta shekarar 1911, a cewar marubucin, ta ci gaba da kasancewa yadda take, yanayin al’adun garin ya sauya. Duk da cewa an yi wasu ƙoƙari na kare da kuma adana wasu sassa na al’adun Marghi, shigowar mutane daga ƙabilu daban-daban zuwa Lassa, ya sa garin ya zama wuri mai yalwar bambancin al’adu.
Buɗe ƙasar Marghi ga tasirin al’ummomin waje bai rasa nasa sakamakon ba. Duk da cewa hakan ya haifar da ci gaba gaba ɗaya a rayuwar al’umma, an samu sauye-sauye masu bayyana a wasu al’adu da ɗabi’un Marghi, musamman wajen gudanar da wasu bukukuwan gargajiya, salon sutura, al’adun matakan rayuwa da kuma al’adun sanya suna, aure da jana’iza.
Waɗannan sauye-sauyen sun samo asali ne musamman daga tasirin addinai da kuma sakamakon zamanantarwa (Duba Babi na 19 zuwa na 21). Kamar yadda ake sa ran faruwa, hulɗa da mutanen da ba ‘yan wannan al’umma ba, ba za ta yiwu ba tare da ta bar wasu tasiri ba, masu kyau da kuma marasa kyau.
Haƙiƙa, a wannan zamani, kiyaye asalin al’ada da martabar kowace al’umma ya ƙara zama aiki mai wahala, musamman saboda ƙara ƙarfi da faɗaɗar tasirin dunkulewar duniya (globalization). A yau, mafi yawan mutanen Marghi, ko waɗanda ke zaune a Lassa ko waɗanda ke zaune a wasu wurare, suna iya magana da harsuna biyu ko ma uku.
Marubucin ya jaddada muhimmancin farfaɗo da al’adun Marghi, musamman ma ya yi kira ga mutanensa da su dawo da Bikin Yawal (wani biki na addini da al’ada), wanda a da ake gudanarwa kowace shekara, domin neman kariya daga mace-mace a cikin al’umma. Daga baya, Ptil Girama Madu ya yi masa kwaskwarima, inda aka mayar da shi biki na al’adu kawai, ta hanyar cire duk wani abu da ya shafi tsafe-tsafe da bautar gumaka. Duk da haka, daga bisani bikin Kirsimeti ya maye matsayinsa a matsayin babban bikin addini na shekara. Marubucin yana goyon bayan a sake farfaɗo da wannan biki, tare da mayar da shi bikin al’adu na shekara-shekara, wanda za a riƙa kira “Ranar Waɗanda Suka Assasa Al’umma” (Founders’ Day).
Dangane da ƙara tsanantar barazanar ɓacewar harshen Marghi kuwa, marubucin ya yi kira mai ƙarfi da a aiwatar tare da tabbatar da bin manufofin koyar da ɗaliban makarantun firamare cikin harshen al’ummar da suke rayuwa a cikinta. Ya kuma ƙalubalanci ‘yan uwansa na ƙabilar Marghi, da su tashi tsaye wajen tabbatar da isar da harshensu ga al’umma masu zuwa, domin kare al’adunsu daga ɓacewa.
Ni ma ina goyon bayan damuwar marubucin, domin harshen Marghi da harshen Babur/Bura nawa, duk suna cikin rukunin harsunan Yankin Chadi. Na lura da wasu kalmomi masu kama da juna da suka bayyana a cikin littafin, kamar “mdurtaku” (mahayi), “kadaka” (shingen da aka yi da busassun kara ko ciyawa), “kindai/pili” (kwano da faifai na ciyawa, “kwatam” (akushi) da kuma “mdurki” (maigida).
Ya kamata a lura cewa, daga cikin harsuna sama da 500 da ake da su a Najeriya, kusan kashi biyu cikin uku suna yankunan gabashin ƙasar kuma dukkansu suna fuskantar babbar barazanar ɓacewa. Don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaugawa, domin ceto su daga wannan mummunan yanayi.
A bayyane yake cewa jerin tsaunukan Mandara/Cameroon, waɗanda suka miƙe daga arewa zuwa kudu a gabashin Najeriya, sun kasance tamkar katanga da ta hana ƙananan ƙabilun Najeriya ci gaba da ja da baya yayin da suke neman mafaka daga matsalolin da suka addabe su. Saboda haka ne suka taru a wannan yanki.
Dangane da sauran batutuwan zamantakewa, marubucin ya yi kira ga Gwamnatin Jiha da ta Ƙananan Hukumomi, tare da kuma ‘yan uwansa masu hali da matsayi, da su haɗa hannu wajen magance ƙarancin abubuwan more rayuwa. Waɗannan sun haɗa da ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi, samar da ingantaccen ruwan sha, kasuwanni, wutar lantarki da kuma farfaɗo da ƙananan masana’antu, waɗanda ƙasar Marghi ta shahara da su a da.
Ya bayyana cewa, abin farin ciki ne yadda aka haɗa garin Lassa da babbar hanyar wutar lantarki ta ƙasa amma a lokacin da yake rubuta littafin babu wutar lantarki a zahiri.
Har ila yau, ya ambaci cewa Gwamnatin Jihar Borno ta yi ƙoƙari a shekarun 1980, wajen samar da ruwan sha daga Kogin Yedzaram da ke kusa amma abin takaici, ba a ci gaba da kula da aikin ba, har dam ɗin ya bushe. Saboda haka, marubucin ya ba da shawarar a gina madatsar ruwa a kan Kogin Yedzaram, domin ta samar da isasshen ruwa da zai biya buƙatun al’ummar yankin.
Kammalawa
Wataƙila masu karatu suna iya yin mamakin abin da hoton bangon gaban littafin, wanda ke nuna wani mahayi a kan doki tare da ruwa a matsayin bango, yake nufi. Ni ma hakan ya ba ni mamaki. Don haka na tambayi marubucin game da ma’anar wannan zane da aka yi a bangon littafinsa. Ya bayyana cewa dokin alama ce ta ƙwarewa da bajintar mayaƙan al’ummar Marghi. Hoton ƙananan ƙoramu kuwa, suna wakiltar Kogin Yedzaram da ke kusa, a lokacin rani.
Kamar sauran ƙananan ƙabilu da dama, ƙabilar Marghi ta yi gwagwarmaya mai tsanani, domin ta ci gaba da wanzuwa a matsayin al’umma tare da kare martaba da asalin al’adunta. Abdulkadir G. Gadzama, wanda ya yi abin a yaba na rubuta tarihinsu, ya bayyana a ɗaya daga cikin babin ƙarshe na littafinsa cewa:
“Lassa ita ce tashar ƙarshe ta wannan ƙaramin rukuni na zuriyar Gadzama (Mingi) daga ƙabilar Marghi, waɗanda aka tilasta musu barin mahaifarsu a Daular Kanem-Borno, kimanin ƙarnoni biyu da suka gabata. Sun ƙi yin sulhu ko yin watsi da kyawawan al’adunsu da al’adun gargajiyarsu kuma suka riƙe mutuncinsu a matsayin mutanen Marghi da ƙwazo da jajircewa. Sun yi mafarkin samun sabuwar ƙasa ta zama mahaifarsu kuma suka yi ta nema da himma; har sai da suka same ta. Da suka gano wannan wuri a ƙarshe, sai ya zama tamkar sun yi babbar nasara! Kakanninsu, waɗanda suka assasa wannan gari, sun yi gwagwarmaya tuƙuru wajen kare da kuma riƙe wannan sabuwar mahaifa, tare da tabbatar da cewa babu wani mai neman mamaya, a lokacin ko nan gaba, da zai kuskura ya mamaye ko ya yi iƙirarin mallakar ko da inci ɗaya na wannan ƙasar, da Allah ya ba su.” (shafi na 248).
Da wannan ruhin jarumtaka da jajircewa ne ya ginu kuma ya ƙarfafa al’ummar Marghi. Tun a zamanin farko sun samu nasarar kare ƙasarsu daga hare-haren masu farautar bayi da kuma ‘yan fashi. Har wa yau, suna ci gaba da tsayawa da ƙarfin hali wajen fuskantar hare-hare da ta’addancin sabbin manyan maƙiyansu, wato ‘yan ƙungiyar Boko Haram.
Marubucin ya nuna matuƙar damuwa kan yadda Dajin Sambisa, wanda ke maƙwabtaka da yankinsu, har yanzu yake zama mafakar ‘yan ta’adda. Ya kuma yi tambaya cikin mamaki, me ya sa jirjirtattun sojojin Najeriya, waɗanda suka yi yaƙi har suka yi nasara a Yaƙin Basasa na tsawon watanni talatin, amma cikin shekaru 15 suka gaza murƙushe wata ƙaramar rundunar ‘yan ta’adda, da ta kafa sansani a cikin ɗan ƙaramin yanki kamar Dajin Sambisa? (shafi na 247).
A History of Lassa na Gadzama, littafi ne da ke tarairayar ruhin jarumtaka da gwagwarmayar al’ummar Marghi. Yayin da yake girmama jaruman Marghi na baya, littafin yana ƙarfafa azama da ƙudurin al’ummar Marghi na wannan zamani, musamman na Lassa, domin su shawo kan ƙalubalen yau tare da kare da kuma ƙarfafa makomar al’ummarsu.
A cikin kalamansa na ƙarshe, marubucin ya yi kira ga sauran ƙabilu, da su rubuta tarihinsu domin su sami ƙarfi da darussa daga abubuwan da suka gabata. Kamar yadda ya bayyana:
“Akwai hikima ƙwarai wajen rubuta tarihin kowace al’umma, domin kowace tana da tarihin da ke bayyana asalinta, al’ummarta da kuma irin baiwar da take da ita, wadda za ta amfani ɗan Adam. Kowace al’umma ta samo asali ne daga mutum ɗaya ko wasu mutane masu ƙarfin hali. Waɗannan mutane sun yi sadaukarwa, sun fuskanci ƙalubale kuma sun yi nasarar shawo kansu. Haƙiƙa, wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu, domin wasu su rayu. Irin waɗannan mutane sun cancanci a riƙa tunawa da su da girmamawa, domin su ne masu ƙirƙirar tarihi.” (shafi na 258).
__________
Dakta Bukar Usman, OON, tsohon Babban Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Ƙungiyar Manazarta Fasaha da Al’adun Gargajiya ta Najeriya (Nigerian Folklore Society) a halin yanzu.
27 ga Yuni, 2026













