• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TSAKANIN MALAM PANTAMI DA HASSADAR MALAMAI

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 13, 2025
in Gizago
0
TSAKANIN MALAM PANTAMI DA HASSADAR MALAMAI

Farfesa Isa Ali Pantami

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TSAKANIN MALAM PANTAMI DA HASSADAR MALAMAI

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Sheikh Isa Ali Pantami

 

                          __________
Ashe haka malamai suke da tsananin hassada ga junansu? Babu shakka na yadda da cewa tabbas hassada da ƙyashin juna sun yi katutu a zukatan wasu malaman addini.

A kwanan nan ne na ƙara tabbatar da haka, musamman bisa la’akari da na yi, yadda a Jihar Gombe wasu rukunnan malaman addinin Musulunci suka yi ta kumfar baki tare da tada jijiyar wuya ga ɗan uwansu, tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.

Abin mamaki ne yadda ɗaya daga cikinsu, ba kunya ba tsoron Allah, ya fito a bainannasi yana adawa da Sheikh Pantami. Yana faɗin cewa wai idan Allah ya kai mu 2027 wai “su malamai” a Jihar Gombe, ba za su goyi bayan Malam ya tsaya takarar Gwamna ba.

Abin mamaki, wai kare da tallar tsire. Ko kuma mu ce abin dariya, wai yara sun tsinci haƙori.

Kun san inda abin mamakin yake? Wai fa malami ne yake faɗin haka ga malami ɗan uwansa. Shin idan malamin addini bai goyi bayan ɗan uwansa mai nagarta kamar Sheikh Pantami ba, to wa zai goya wa baya? Jahili, ɗan duniya ke nan zai zaɓa? Kun ga ke nan, hassada da ƙyashi ne suka yi tasiri a nan!

Abin dariyar kuma shi ne, gurgun dalilin da malamin ya kawo, a matsayin hujjarsa ta rashin amincewa da Pantami. Abin da ya sanya na ce dililinsa gurgu ne, shi ne, wai a lokacin da Sheikh yake Minista, wai ba ya ɗaga kiran wayarsu. Wai kuma bai taimaki malaman Jihar Gombe ba da dukiya.

Ni kuwa na ce assha! Wai malami ne yake faɗin wannan mummunar magana, kamar wanda bai taɓa sanin Allah ba, balle amanarsa. Shin shi malamin nan bai san cewa dukiyar gwamnati ta al’umma ba ce? Yana son Malam ya ɗebi dukiyar al’umma ya raba masu? Shin bai san akwai ranar hisabi ba? Ke nan yana nufin wanda za su zaɓa ya zama Gwamna a Jihar Gombe, shi ne wanda zai buɗe masu bakin baitulmali su ɗebi dukiyar da suke so, ba wanda zai yi wa al’umma mulki da adalci ba?

Gaskiya an yi walƙiya mun ga idon kowa. Idan ba hassada ba, ai malamai, musamman ma a Jihar Gombe, kamata ya yi su yi murna da alfaharin yadda ɗan uwansu Malami ya riƙe babban muƙami a Gwamnatin Tarayya, kuma ya samu yabo na riƙe amana. Ko kuwa suna nufin ba su ga yadda Pantami ya samu shaida daga sassan duniya ba, yadda ya tafiyar da aikinsa na Ministan Sadarwa?

A batun gaskiya, muddin Farfesa Pantami ya fito takarar Gwamna a Jihar Gombe kuma al’umma suka juya masa baya, to su sani, ba su cuci kowa ba sai kansu.

Allah ya kare mu da halayen ƙyashi da hassada, Amin.
_______________

Jama’a, yaya kuke ganin wannan al’amari? Shin ko Sheikh Pantami ya cancanci ya tsaya takarar Gwamna a Jihar Gombe? Ku bayyana ra’ayinku a Comment Section:

 

Previous Post

SASSANYAN AMINCI (5)

Next Post

SASSANYAN AMINCI (6)

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
SASSANYAN AMINCI (6)

SASSANYAN AMINCI (6)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

October 18, 2023
Kaduna State Pilgrims are to Deposit ₦2.5 Million

Kaduna State Pilgrims are to Deposit ₦2.5 Million

October 6, 2023
WHEN THE SPIRIT WHISPERS: Littafin Tsarkake Tunani Da Samar Da Saita Rayuwa

WHEN THE SPIRIT WHISPERS: A New Beacon of Inner Awakening

October 11, 2025
TSOKACINMU NA YAU (20)

TSOKACINMU NA YAU (20)

March 20, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.