• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 12, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Jaafar Jaafar Da ‘Yan Siyasar Kano: Ashe Wanzami Ba Ya Son Jarfa?

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 15, 2025
in Gizago
0
Jaafar Jaafar Da ‘Yan Siyasar Kano: Ashe Wanzami Ba Ya Son Jarfa?

Tsakanin Ja'afar Ja'afar Da 'Yan Siyasar Kano

46
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Jaafar Jaafar Da ‘Yan Siyasar Kano: Ashe Wanzami Ba Ya Son Jarfa?

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Tsakanin Ja’afar Ja’afar Da ‘Yan Siyasar Kano

 

                      _______________
Ga duk mai bibiyar al’amuran siyasa, musamman a Jihar Kano, zai cika da mamaki yadda wasu ‘yan siyasa ke nuna son rai da ƙeƙashewar zuciyar ɗaure wa ƙarya gindi. Babban abin da ke faruwa a yanzu, tsakanin ɗan jarida kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian, Malam Ja’afar Ja’afar da Gwamnatin Jihar Kano, ya isa misali.

A lokacin da shi Ja’afar ya kafa suna da tarihin bankaɗo almundahana da zurmuƙen da ‘yan siyasa da masu mulki, musamman a Jihar Kano suke aikatawa, su kuma sai suka zama ‘yan a bi Yarima a sha kiɗa.

Yadda abin yake shi ne, idan yau ya bankaɗo wani al’amari mara daɗi a kan ‘yan Gandujiyya, sai ‘yan Kwankwasiyya su yi ta kaɗa masa tambura, suna kwarzanta shi, tare da yaba masa cikin murna da jin daɗi. Haka kuma, idan reshe ya juye da mujiya, ya bankaɗo wani jami’in Gwamnatin Kwankwasiyya, sai kuma ‘yan Gandujiyya su kama murna, a yayin da su kuma za su yi ta kai gwauro da mari suna la’antarsa, tare da barazanar kai shi kotu. Akwai misalai masu yawa a kan haka.

A can baya, jaridar Ja’afar ta taɓa buga rahoton yadda aka zargi Sarki Kano, Muhammadu Sanusi II da lalata dukiyar Masarautar Kano, kimanin Naira biliyan 3.4, tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017. ‘Yan siyasa ɓangaren Gandujiyya sun yi murna da wannan. A yayin da su kuma ‘yan Kwankwasiyya suka gune.

A na nan kuma sai ga wata sabuwar wainar daga tandar Ja’afar, wadda ya toya a shekarar 2018. A wannan karon, wani faifan bidiyo ne ya wallafa, inda aka nuno Gwamnan Jihar Kano na lokacin, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje yana amsar daloli da aka ƙiyasta sun kai Dala miliyan biyar. An yi zargin cewa rashawa ce yake amsa daga hannun wani ɗan kwangila.

Ai kuwa abin nema ya samu, matar ɗan Kwankwasiyya ta haifi jar hula. A sakamakon wannan bankaɗa ta bidiyo, babu sunan da ba su raɗa wa Ganduje ba kuma babu yabon da ba su yi wa Ja’afar ba. Su kuwa ‘yan Gandujiyya, har matakin Shari’a sai da suka ɗauka. Daga bisani ma, wannan al’amari sai da ya tilasta masa yin gudun hijira zuwa Ingila.

Tafiya sannu-sannu kwana nesa. Haka ne har Allah ya kawo mu watan Agusta da ya gabata, inda ɗan jarida Ja’afar ya sake bamkaɗo wata ƙumbiya-ƙumbiyar, wacce ta shafi Gwamnatin Jihar Kano, a ƙarƙashin Gwamnan Kwankwasiyya, Abba Kabir Yusuf. A wannan karon, jaridar ta wallafa zargin Darakta Janar Protocol na Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Rogo da karkatar da Naira biliyan 6.5.

Kamar yadda tafiyar ta saba, yau ma ba ta canza zane ba, domin kuwa a halin da ake ciki Gwamnatin Jihar Kano da ‘yan Kwankwasiyya sun far wa Ja’afar ta hanyoyi da dama. Wasu suna zagi, wasu suna la’anta, a yayin da ita kuma gwamnati ta kai koke ga ‘yan sanda, cewa a bincike shi da laifin ɓata suna, kamar kuma yadda take shirin kai shi ƙara kotu!

A taƙaice dai, wanzami ba ya son jarfa. Ja’afar yana aikinsa na jarida, su kuma ‘yan siyasar Kano, kowane ɓangare bai so a ce an bankaɗo ɓarnar da yake aikatawa.
__________
Jama’ar Allah, yaya kuke ganin wannan al’amari? Ku bayyana ra’ayinku a Comment Section:

Previous Post

BATUN SASANCI DA ‘YAN BINDIGA A JIHAR KATSINA

Next Post

TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

TARON JIGAJIGAN KATSINA ALHERI NE

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SASSANYAN AMINCI (4)

SASSANYAN AMINCI (4)

September 11, 2025
Visit to Biu

Visit to Biu

May 11, 2024
YAU TAKE SALLAH! BARKA DA SALLAH!

YAU TAKE SALLAH! BARKA DA SALLAH!

June 28, 2023
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

January 31, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)
  • Malumfashi An Yi Babban Rashi
  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

May 12, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.