Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Taimakon al’umma, musamman raunana, mabuƙata, marasa galihu da faƙirai, yana daga cikin manyan ayyukan alheri da Musulunci ya ƙarfafa. Al’umma ba ta ƙarfi da dukiyar masu hannu da shuni kaɗai, sai dai idan waɗanda Allah ya hore wa dukiya suka kasance masu tausayi da tallafa wa waɗanda suke cikin buƙata.
Allah Maɗaukakin Sarki a cikin Alƙur’aninsa mai girma, Suratul Ma’idah (5:2) ya ce: “Ku yi wa juna taimako a kan alheri da taƙawa, kada ku yi wa juna taimako a kan zunubi da zalunci.” Wannan aya tana nuna cewa taimakon juna a kan abin da yake na alheri da amfani ga mutane wata hanya ce ta samun yardar Allah.
Bisa ga wannan gwadabe, ya zama wajibi a ambata sunan Jagoran Gidan Amana a Jihar Katsina, Alhaji Haruna Maiwada, Sadaukin Kaita kuma Ɗan Amanar Katsina da babbar murya; musamman yadda a kodayaushe yake saka farin ciki a zukatan mabuƙata da raunana, har ma da sauran al’umma.
A ranar Lahadin da ta gabata, 30 ga watan Agusta 2026, a irin wannan aiki da ya saba na jin ƙari, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan jin ƙan guda biyu. Ayyukan sun haɗa da raba kekunan guragu guda 100, a Ƙananan Hukumomin Katsina da Kaita, domin sauƙaƙa masu sufuri da samar masu walwala da jin daɗi. Haka kuma, ya bai wa kowannensu Naira dubu goma.
Haka kuma, duk dai a Lahadin da ta gabata, Ɗan Amana ya ƙaddamar da rarraba baburan hawa (Roba-Roba) guda 50 ga matasa, waɗanda suke tare da shi wajen hidimar siyasa da ta rayuwar yau kullum.
Wani al’amari na jin ƙai daga Dakta Maiwada ya sake faruwa a wanshekaren da ya yi wannan abin alheri, inda ya samu labarin wani matashi da aka sace wa abin hawa. Nan take ya ba shi kyautar sabon babur shi ma.
Irin wannan aiki sai mai ƙarfin imani, wanda yake bin umurnin Allah. A Alƙur’ani mai girma, Suratu Ali ‘Imrana (3:92), Allah ya yi magana kai tsaye game da kulawa da mabuƙata da raunana, inda ya ce: “Ba za ku sami kyautatawa ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so; kuma duk abin da kuka ciyar, to lalle Allah Masani ne gare shi.”
Wannan aya tana koyar da mu cewa ainihin kyautatawa ba wai mutum ya bayar da abin da ba ya buƙata kawai ba ne; a’a, ya bayar daga abin da yake so kuma yake daraja. Don haka, ya kamata masu hali su yi koyi da Dakta Maiwada, su sani cewa dukiyar da suke da ita, amana ce daga Allah, kuma akwai haƙƙoƙin wasu mutane a cikinta.
A wani Hadisi da aka ruwaito daga Jabir (ra), Manzon Allah (saw) yana cewa: “Mafi alherin mutane, shi ne wanda ya fi amfani ga mutane.”
Ma’ana dai ita ce, darajar mutum ba ta ta’allaƙa ne kawai da yawan dukiyarsa, muƙaminsa ko shahararsa ba, sai dai da irin amfanin da yake yi wa sauran mutane. Wanda yake amfani da dukiyarsa wajen ciyarwa, taimakon marar lafiya, ɗaukar nauyin karatu ga marasa hali, tallafa wa maraya ko taimakon wani da ke cikin tsananin rayuwa, yana barin kyakkyawan tasiri a cikin al’umma.
Haka kuma a Sahih Muslim, Hadisi mai lamba 2699, Manzon Allah (saw) ya kwaɗaitar da masu hali da su taimaki mabuƙata, yana bayyana girman ladan wannan aiki. Ya ce: “Duk wanda ya yaye wa mumini wata damuwa daga cikin damuwoyin duniya, Allah zai yaye masa wata damuwa daga cikin damuwoyin ranar alƙiyama kuma wanda ya sauƙaƙa wa wanda yake cikin tsanani, Allah zai sauƙaƙa masa a duniya da Lahira.”
Wannan babban kira ne ga masu arziki da su yi amfani da abin da Allah ya ba su wajen rage wahala da ƙuncin da mutane suke ciki. Dukiya ba ta zama abin alfahari kawai ba, tana iya zama hanyar samun rahamar Allah idan aka yi amfani da ita wajen taimakon bayinsa.
Bisa ga wannan hujja, muna roƙon Allah ya ƙarfafa himmar Dakta Maiwada, ya biya masa buƙatunsa na alheri, duniya da lahira. Allah ya sa sauran attajirai su yi koyi da ayyukan alherin da yake shuka wa al’umma a kullum.
__________













