• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 15, 2026
in Siyasa
0
MALAM SULE LAMIDO:  Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Alhaji, Dr. Sule Lamido, CON

16
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

MALAM SULE LAMIDO:

Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Related posts

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

August 24, 2026
Alhaji, Dr. Sule Lamido, CON

__________

A ranar Lahadi mai zuwa, ɗimbin masoya ‘yan uwa da abokan arziki da ma abokan siyasar gwarzon ɗan kishin ƙasa, jigon siyasar Najeriya, Dakta Sule Lamido CON, za su yi kwamba a garin Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, domin taya shi murnar cika shekaru 78 da haihuwa.

Mutum mai muhibba da martaba amma mai sauƙin kai, wannan fitaccen ɗan siyasar masu ra’ayin ci gaba, ya tabbata jajirtacce, mai sadaukar da kansa ga aikin gina Najeriya.

Ɗan siyasa mai himma da tsayayyen ra’ayin gina al’umma, daraja zaman lafiya mai ɗorewa, haɗin kai da kwanciyar hankalin ƙasa, Alhaji Sule ya amsa sunansa a zukatan miliyoyin ‘yan Najeriya.

A halaye da ɗabi’a, ya ci gaba da kasancewa mai aminci, amana da biyayya ga jam’iyyar da shi da wasu kamar Cif Solomon Daushep Lar da Mista Sunday Awoniyi da Alhaji Muhammad Abubakar Rimi, tare da sauran ’yan uwansu ’yan kishin ƙasa suka yi amfani da ita wajen korar sojoji daga mulki a shekarar 1999.

Ƙungiyarsu ta G34, wacce daga baya ta rikiɗe zuwa PDP, ita ce ta karɓi mulki daga hannun sojoji. Lamido ya ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyarsa ta PDP duk da matsaloli da dama, barazana da tsoratarwa, da kuma wasu ƙawancen siyasa marasa kyau da wasu ’yan jam’iyyar suka ƙulla da jam’iyyar da ke mulki, musamman ta hannun wasu wakilai da Abuja ke mara wa baya; abubuwan da suka haifar da watsewar ’ya’yan jam’iyyar na gaskiya zuwa wasu sansanonin siyasa.

Ana sa ran bikin ranar Lahadin nan, wanda aka shirya domin girmama tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya a Jamhuriya ta Biyu – Lamido, zai kasance babban biki.

Alhaji Lamido, a matsayinsa na ɗalibin siyasar Malam Sa’adu Zungur da Malam Abba Maikwaru da Malam Illa Ringim, tun sama da shekaru 50 da suka gabata, ya kasance mai ingantaccen tarihin zaman lafiya da kowa – ba shi da abokin gaba a siyasance da kuma mu’amala.

Jagoran Talakawa Lamido, Allah ya azurta shi da halayen son jama’a, yafiya, tausayi da kyakkyawar mu’amala da mutane. Ko yana kan kujerar gwamnati ko ba ya kanta, yana halartar bukukuwan aure na manya da ƙanana, yana zuwa bukukuwan ƙaddamar da ayyuka, sannan yana zuwa gaisuwar ta’aziyya ga kowane irin mutum, ba tare da la’akari da ƙabila, addini ko ra’ayin siyasa ba.

A yayin wannan gagarumin biki, Farfesa Nu’uman Muhammad Habib ne zai gabatar da jawabin buɗe taro, yayin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, CON, zai jagoranci taron. Babban mai gabatar da jawabi, Dakta Awwal Anwar, zai yi tsokaci ne mai taken: “Gina Sabuwar Najeriya: Jagorantar Matasa Bisa Hanyar Ingantacciyar Siyasa Mai Bin Ƙa’ida da Tsari.” Farfesa Kamilu Sani Fagge da Dakta Akilu Indabawa, su ne masu tattaunawa kan wannan batu.

Muna amfani da wannan dama wajen yi wa Kwamared Sule Lamido fatan ƙarin shekaru masu yawa cikin ƙoshin lafiya da wadata, domin ya ci gaba da yi wa bil’adama hidima.

Allah ya ƙara maka lafiya, ya kuma tsawaita maka rayuwa mai albarka, Baba.

_________

Previous Post

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

Next Post

JAGORA: Leader of the Masses

Related Posts

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
Siyasa

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)
Siyasa

Katsina A Makon Jiya (17-23-08-2026)

August 24, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
Siyasa

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
Next Post
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Sufeto-Janar Ya Ƙuduri Sauya Halayen ‘Yan Sanda

Sufeto-Janar Ya Ƙuduri Sauya Halayen ‘Yan Sanda

July 1, 2023
Kyautata Wa Marayu Da Mabuƙata Alheri Ne

Kyautata Wa Marayu Da Mabuƙata Alheri Ne

July 17, 2023
Go Back to the Roots, Write in African Tongues – PAWA

Go Back to the Roots, Write in African Tongues – PAWA

March 18, 2024
KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (3)

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (3)

August 13, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.