• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, September 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

RAYUWA

ƘASIDA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 21, 2025
in Adabi
0
RAYUWA

Bashir Yahuza Malumfashi

25
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

RAYUWA
__________
Ni Bashir Yahuza Malumfashi, na sadaukar da wannan waƙe ga ɗaukacin TALAKAWAN NAJERIYA, bisa halin matsi da jarabawa da ake ciki. Allah kawo sauƙi da sawaba – Amin!
__________

Bashir Yahuza Malumfashi

Komai wuya ko akasi,
Kar ka yi kukan matsatsi,
Kar ka zamo mai taratsi;
Ka yi godiya ko ba hatsi,
Rabbi Allah bai mance ka ba.

Related posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026

Idan ka samu dami ɗaya,
Waiga ƙasa wani ba ɗaya,
Wani bai da ko da ‘yar tiya,
Sai dai ya je yai magiya.
Ƙarfin jiki ba ka kai shi ba.

Kai ne kake da ƙafa biyu,
Har ka ƙara da ido biyu,
Ga hannuwanka guda biyu,
Ka ɗauki saiti biyu-biyu.
Rahama ta Allah ba mutum ba.

Wani ko ƙafarsa guda ɗaya,
Wani ko idonsa guda ɗaya,
Wani babu hannu ko ɗaya,
Bai da tsaba ƙwaya ɗaya,
Iko na Allah ba na su o’o ba.

Wani ga gida tangameme,
Filin noma wangameme,
Dokin hawa sangameme,
Ga tulun ciki sunƙumeme,
Komai ya biɗa bai rasa ba.

Ga wata can kanta gashi,
Ya yi kwance ya yi laushi,
Kowa ya taɓa ya ji taushi,
Kowa ya gani zai murmushi,
Hikima ta Allah ba wanin ba.

Wata kanta sai yai kamar bal.
Babu gashi ƙwal yake tal.
Doguwa ce ga ta shantal,
Wata kau gajera ce ‘yar gajal.
Halittar Allah ba ta gaza ba.

Wani yai gabas wani yamma,
Wani dariya wani hamma,
Wani kasala wani himma,
Suturar wani ta yi tsumma.
Kowa da inda ya sa gaba.

Wani kam ɗan kasuwa ne,
Wancan kuwa ma’aikaci ne,
Shi ɗan uwa kafinta ne,
Ga wani nan injiniya ne,
Rayuwa ce ba ta zam ɗaya ba.

‘Yan uwana sai mu gane,
Rayuwa dai kar mu gune,
Godiyar Allah mu manne,
Komai ka gani ƙalubale ne,
Allah Yake yi ba mutum ba.

Ni Bashiru na gode Allah,
Ni ɗan Yahuza ba ni gilla,
Na Malumfashi ba ni illa,
Fasihin Galadima aƙalla.
Kariyar Allah ba mutum ba!
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi
Talata 19-02-1445 (Hijiriyya),
05-09-2023 (Miladiyya).
__________

Previous Post

Sakatare Ibrahim Dasuƙi Abubakar: Al’ummar Malumfashi Ta Samu Ƙaruwa

Next Post

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Related Posts

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)
Adabi

ALLAH TSIN€ WA MAƘIYA MANZO (SAW)

September 12, 2026
Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
Adabi

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa
Adabi

Alhaji Sule Lamido: Jagoran Talakawa Na Haƙiƙa

August 29, 2026
Next Post
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

November 6, 2025
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (3)

December 30, 2025
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026
AUREN ‘YA’YAN YUSUF DINGYAƊI: Saƙon Godiya Da Ban Gajiya

AUREN ‘YA’YAN YUSUF DINGYAƊI: Saƙon Godiya Da Ban Gajiya

August 18, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78
  • ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya
  • SUNANTA UMMU-KHULSUM

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

MALAM SULE LAMIDO:  Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

September 15, 2026
ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

September 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.