Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
• Yarona Ne
• Har Yanzu Ina Son Sa
Daga Wakilinmu

__________
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya kuma ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa a shirye yake ya sasanta da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, domin yaronsa ne. “Har yanzu ina son sa,” in ji shi.
Gwamna Yusuf, wanda a baya ya kasance babban ɗan Kwankwasiyya, ya lashe zaɓen shekarar 2023 ƙarƙashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), daga bisani kuma ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Wannan sauyin ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin Kwankwaso da Yusuf, wanda ya yi wa Kwankwaso aiki a matsayin mataimaki na tsawon shekaru 40 da suka gabata.
Sai dai, a wata hira da Sashen Hausa na BBC, wadda aka wallafa a shafinsa na sada zumunta da aka tabbatar, Kwankwaso ya ce zai iya yafe wa Abba Yusuf tare da sulhu da shi, idan shi Gwamnan yana son hakan.
Kwankwaso ya ce bai taɓa yin watsi da Yusuf ba kuma bai taɓa umartar sa da ya sauya jam’iyya ba.
“Ban yi watsi da shi ba, ban ce masa ya tafi ba kuma ban kore shi ba. Har yanzu ina son sa,” in ji shi.
Kwankwaso ya ce shi ba mutum ne mai ɗaukar fansa ba kuma a kullum yana yafe wa waɗanda suka yi masa laifi.
Ya ce ya yafe wa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, duk da kurakuran da ya ce Gandujen ya aikata masa a lokuta daban-daban.
“Sau nawa ne na samu matsala da Ganduje? Ya yi adawa da ni a lokuta da dama. A shekarar 2007, lokacin da muke Ma’aikatar Tsaro, shi ne Mataimakina na Musamman (SA) amma suka riƙa gudanar da tarurruka domin ganin an kawo ƙarshen tasirina saboda na yi takara da su.”
“Duk da waɗannan saɓanin, na fito da Ganduje tare da mara masa baya,” in ji shi.
Kwankwaso, wanda ya ce bai taɓa ɗaukar kansa a matsayin jagoran da yake tilasta wa mutane abin da za su yi ko kuma yake ba su umarni kai tsaye ba, ya ƙara da cewa har yanzu yana cikin harkokin siyasa kuma ba ɗan siyasar da yake zaune gefe yana kallon al’amura ba ne.
“Ni ba Allah ba ne. Don haka, idan Yusuf ko wani mutum yana son zuwa, dole ne ka kasance mai haƙuri, mai zuciya mai faɗi da tausayi, domin ba kowa ne zai bi tafarkinka ba.”
“Ba za ka yi tsammanin kowa zai yi aiki, ya kasance ko ya yi tunani kamar yadda kake yi ba, domin kowane mutum yana da irin nasa tunani, shekarunsa, tarihin rayuwarsa da kuma matakin iliminsa.”
“Saboda haka, da ban kasance mai yafiya ba, da ba mu fito da Ganduje ba. Haka lamarin yake da Yusuf.”
“Ba ma neman ko sisi daga hannun kowannensu, domin mu ba su goyon bayanmu ko tikitin takara; ba ma sayar da ɗan takararmu.”
__________
Ku yi “LIKE” “COMMENT” da “SHARE” domin saƙon nan ya faɗaɗa da yawa.
__________












