JONATHAN – KWANKWASO: Sabon Lissafin 2027
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Wata majiya ta tabbatar mani da cewa, akwai yiwuwar Madugun Kwankwasoyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso zai koma Jam’iyyar PDP, inda ake sa ran shi kuma Goodluck Ebele Jonathan zai fito takarar Shugaban Ƙasa a 2027.
Idan haka ta tabbata, ana tsammanin shi Kwankwaso zai yi masa matakaimaki. Ke nan Kudu Shugaban Ƙasa, Arewa Mataimaki. Kudu, Kirista; Arewa, Musulmi.
Inda lissafin yake shi ne: Jonathan zango ɗaya kawai zai yi a mulki, domin ya taɓa yin zango ɗaya a baya. Daga nan kuma sai Kwankwaso ya ci gaba, idan Allah ya amince da haka.
Masu nazarin siyasa suna ganin cewa wannan lissafin mai ɓullewa ne, domin kuwa Jonathan zai iya samun ƙuri’un Kudu da tsoka. Shi kuma Kwankwaso zai taɓuka abin gani sosai a jihohin Arewa.
Haka kuma, Jonathan Kirista ne, shi kuma Kwankwaso Musulmi. Ke nan babu tsegumin cewa wani addini ya danne wani, kamar yadda APC ta yi a 2023.
__________
Jama’ar Allah, yaya kuke ganin wannan shiri?














Gaskiyane wannan mu kokarta muyi abunda ya da ce