TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (6)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Kamar yadda muka bayyana a rahoto kashi na 5, a yau za mu karkata ne zuwa ga muhimman mutanen da aka karrama a yayin wannan taro. Za mu fara da Injiniya Muntari Sagir, wanda shi ma ya gabatar da jawabi, a yayin da aka karrama shi.
√ Wane Ne Injiniya Muntari Sagir?
Wannan bawan Allah, ɗaya ne daga cikin matasan attajiran da Allah ya albarkaci Ƙaramar Hukumar Malumfashi da kewaye da su. Mutum ne shi da Allah ya ba shi wasu keɓaɓɓun halaye guda biyar.
Waɗannan halaye su ne, “Kishin Al’umma.” Ga dukkan masu bibiyar al’amuransa a Malumfashi, zai tabbatar da wannan halayya tasa. Na biyu, mutum ne shi mai “Kawaici.” Wannan halayya ce ta sanya wasu ma da ba su yi mu’amala da shi ba suke zaton cewa Muntari Sagir mai girman kai ne. Kuma alhali ba haka al’amarin yake ba, domin kuwa halayyarsa ta kawaici ce ta sanya ba ya shiga harkar da ba ta shafe shi ba, ba ya da yawan magana ko surutu.

Halayyarsa ta uku, ita ce “Sanin Ya Kamata.” Hakan ke nufin cewa shi mutum ne mai natsuwa da tsara duk abin da yake son aiwatarwa. Na huɗu, Injiniya mutum ne “Mai Kyauta.” Halayyarsa ta biyar, ita ce “Zumunci.” ‘Yan uwa, abokansa da dukkan waɗanda suka jiɓance shi, su ne manyan shaidun da za su tabbatar da wannan babbar halayya tasa.
√ Jawabinsa A Taron Facebook:
Injiniya Muntari Sagir na ɗaya daga cikin zaratan mutanen da aka karrama a wannan muhimmin taro da aka gudanar a Malumfashi. A lokacin da aka gabatar da shi domin ya yi jawabi. Bai yi ƙasa a gwiwa ba.
Injiniya ya yi godiya, kamar kuma yadda ya yaba wa matasan da suka shirya wannan taro. Ya yi wa al’ummar Malumfashi albiahir da cewa, kamfaninsa zai gina katafaren zauren shirya taro na zamani (Event Centre) a Malumfashi. Kamar yadda ya ce, “in sha Allahu, a taron Malumfashi Facebook Connect na baɗi 2026, a cikin wannan sabon zauren da zan gina za a gudanar da shi.”
A jawabin nasa, a matsayinsa na matashi, wanda ya damu da ci gaban matasa da sauran al’ummar Malumfashi da kewaye, Injiniya ya ba matasa shawarwari game da rayuwa. Ya ce ya kamata matasa su daina zaman banza, su daina bari zuciyarsu tana mutuwa, su riƙa nemab aiki ko sana’a komai ƙankantarta. Ya ce “ba daidai ba ne yadda wasu matasa suka zama masu rashin kunya da wulaƙanta manya. Idan Allah ya azurta wani ko ya ba shi mulki, ba ƙarfinsa ko dubararsa ba ce. Maimakon ku riƙa nuna ƙyashi da hassada, ku tashi ku nema wurin Allah. Ku ma zai iya ba ku naku, domin shi ne ke bayarwa ga wanda ya so.”

Haka kuma ya yi gargaɗi na musamman ga wasu matasa da ke yin shaye-shaye kuma suke yi wa al’umma sace-sace da ɓarnata masu dukiya. Ya ce su shiga taitayinsu, domin akwai hukuma kuma akwai hukunci ga duk wanda ya fitsare ƙafarsa, ya shiga cikin irin wannan mummunar ɗabi’a.
√ Wasu Muhimman Bayanai:
A wata ganawa ta musamman da na yi da Injiniya Muntari Sagir, na tambaye shi game da wasu halaye nasa, musamman ayyukan tallafa wa al’umma da yake yi. Sai ya bayyana cewa: “A matsayina na Musulmi, na yi imani da Allah, cewa kyautatawa da tallafa wa al’umma abubuwa ne masu kyau, waɗanda Allah da manzonsa suke so. Don haka Allah ya hore mani, babu dalilin da zai sanya in riƙe hannu, in ƙi taimakon al’umma, alhali suna da buƙata.”
Ya ƙara da cewa, “idan na ga wani cikin matsala, kamar rashin lafiya ko wani rashi, nakan yi tunanin cewa idan ni ne nake cikin irin wannan jarabawar, yaya zan ji? Don haka ba na jin daɗin in ga na kasa taimako mai neman taimako. Kuma abin ikon Allah, ina ganin buɗi daga wurin Allah.”
Ko Injiniya yana da sha’awar tsayawa takarar wani muƙami a siyasa? Tambayar da na yi masa ke nan, inda shi kuma ya amsa da cewa: “A gaskiya a yau shugabanci ya koma wani irin abu, inda ake faɗin al’amura da baki, aikatawa ya gagara. Duk yadda shugaba a mulkin siyasa ya so ya kamanta gaskiya da adalci, idan bai samu mataimaka na gaske ba, ba zai iya aikata wani abin kirki ba. Don haka ba ya cikin tsarina, ba zan fito wata takarar kujerar siyasa ba. Amma za mu ci gaba da taimakawa ta hanyar da Allah ya ba mu, ta hanyar sana’armu.”
√ Ayyukan Jin Ƙai Da Raya Al’umma:
Kamar yadda muka tsakura a gabatarwa, cewa Injiniya Muntari Sagir mutum ne mai sanin ya kamata, mai kishin al’umma kuma mai kyauta, to hakan ta tabbata a rayuwarsa. Wannan dalili na daga cikin abin da ya sanya aka karrama shi da KAMBIN GIRMAMAWA a wannan taro.

Kaɗan daga ayyukan da yake wa al’umma sun haɗa da ginawa da yaran masallatai. Ginawa da gyaran asibiti da ɗakunan shan magani. Ginawa da gyaran makarantun Islamiyya da na boko. Yana ginawa da gyaran kwalbatoci. Yana tallafa wa ɗalibai da kuɗin makaranta ko na jarabawar WAEC, NECO, JAMB da sauransui. Yana tallafa wa marasa lafiya da kuɗin magani, yana gina rijiyoyin burtsatse.
Wannan shi ne Injiniya Muntari Sagir Malumfashi. Idan Allah ya kai mu rahoto na 7, za mu duba rayuwar Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson), wanda shi ma aka karrama a wannan taro.
______________












