• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (4)

RAHOTON MUSAMMAN

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 1, 2025
in Gizago
0
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (4)

Dokta Aminu Garba Waziri, yayin gabatar da ta'aliƙinsa a zauren taron

23
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (4)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Daga Dama: Dokta Aminu Waziri ne, tare da Malam Haruna Musa Rugoji, a zauren taron

 

A wannan muƙala mai samfurin rahoto, a yau za mu ɗora da abin da ya biyo bayan muƙalar da Shugaban Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina, Malam Haruna Musa Rugoji ya gabatar, wacce ta yi tambihi game da matsayin Musulunci dangane da Soshalmidiya.

Shin mene ne ya biyo bayan muƙalar tasa? Ta’aliƙi ne mai ɗaukar hankali da fadakarwa daga bakin Dokta Aminu Garba Waziri.

√ Wane Ne Dokta Aminu Waziri?
Dokta Aminu dai ɗaya ne daga cikin jajirtattun masu kishin al’umma da Allah ya albarkaci Malumfashi da su. Babu wai, bisa la’akari da tarihinsa, shi mutum ne da bai sa komai ba a gabansa face yadda zai rufa wa kansa da iyalansa da ma al’umma asiri.

Mutum ne shi mai himma da daraja harkar ilimi, dalili ke nan ma ya saita dugadugansa bisa neman ilimi da ilimantarwa, wanda a halin yanzu shi cikakken mamallakin Digirin-Digirgir (phD) ne kuma yana kan hanyar zama Farfesa. Fitaccen masanin harkokin safiyo da fuloti, malamin jami’a, ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa, wanda a yanzu haka yake shugabantar kamfanin harkokin fulotai da kasuwancinsu, na AG Waziri &Co.

A fannin siyasa kuwa, Dokta Aminu ya taɓa zama Sakatare a Ƙaramar Hukumar Malumfashi. Ya taɓa zama Shugaban Ƙaramar Hukumar Malumfashi. Ya taɓa zama Mataimaki Na Musamman ga Shugaban Majalisar Tarayya. Ya taɓa zama Sakataren Dindindin a Jihar Katsina, kamar kuma yadda ya taɓa zama Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaugawa ta Jihar Katsina (SEMA). Ta ɓangaren wasannin motsa jiki kuwa, mutum ne shi mai buga Kwallon Dawaki (Polo).

Ta fuskar halayya kuwa, Dokta Aminu Waziri ya samu kyakkyawar shaida, a matsayin mutum mai sauƙin kai, mai zumunci kuma mai taimakon mabuƙata. Ga duk wanda ya yi mu’amala da shi, da wuya ka ji ya ambata wani aibu daga gare shi, idan ka cire ajizancin da ake samu daga kowane ɗan Adam.

√ Ta’alikin Doka Aminu Waziri
Kamar yadda bayani ya gabata, Malam Haruna Musa Rugoji ne ya gabatar da muƙala mai taken, “Mahangar Musulunci Dangane Da Soshalmidiya.” A matsayinsa na mai ta’aliƙi, Dokta Aminu ya buɗe da addu’a, inda ya ci gaba da bayani tare da fashin baƙi dangane da al’amuran Soshalmidiya.

Wasu daga cikin mahalarta taron

Dokta ya bayyana cewa a halin da ake ciki, zamani ya kawo intanet kuma al’umma musamman matasa sun rungumi Soshalmidiya. Ya kawo ƙididdiga daban-daban, inda yake tabbatar da yadda a duk shekara, yawan al’ummar da ke amfani da kafar Intanet/Soshalmidiya ke ƙaruwa. A misali, ya ce a shekarar 2024, an samu ƙiyasi da ƙididdigar da ke shaida cewa akwai matasa, masu shekaru 16 zuwa 30 kimanin miliyan 16.2 da ke amfani da kafafen sadarwa na zamani. Ya ce kuma a kullum adadin ƙaruwa yake.

Dokta ya ce babu makawa, amfani da Soshalmidiya ya zama dole ga al’umma, domin rayuwa ta karkata gare ta. Sai dai kuma ya jawo hankalin al’umma da su bi al’amarin cikin tsari da abin da ya dace da umurni da hanin Allah da Manzonsa (saw). Ya ce iyaye da malamai da shugabannin al’umma suna da babbar rawar da za su taka, wajen yi wa matasa jagoranci, domin ganin an riƙa amfani da kafafen sada zumunta yadda ya dace.

Ya ce, a matsayin mutum na Musulmi, ya tabbatar da ya nemi ilimin addini da na mu’amala, yadda zai riƙa tu’ammali da kafafen yadda ya dace da kuma ɗaukar abin da zai amfane shi duniya da lahira, tare da kauce wa faɗawa cikin abin da zai cutar da shi da imaninsa. Wata babbar shawara da ya bayar ga al’umma ita ce: “A duk lokacin da muka shiga intanet, to mu yawaita yi wa Annabi Muhammadu (saw) salati.” Ya ce akwai fa’ida mai yawa ga haka, inda mutum zai samu lada kuma ya samu jagorar aikata abubuwa masu muhimmanci a waɗannan kafafe na sada zumunta.
Haka kuma, ya ja hankalin cewa, wani babban ƙalubale da ake fuskanta a kafafen sada zumunta, shi ne yaɗa hotuna da bidiyo masu lalata ko bayyana tsiraici. Wannan abu ne da ya saɓa wa koyarwar Musulunci. Allah (SWT) ya ce: “Ka ce wa muminai su rage kallonsu kuma su kiyaye farjinsu, hakan shi ne mafi tsabta a gare su.” (Suratun Nur: 30). Wannan umarni yana nuna muhimmancin kiyaye kallo da bayyana sassan jiki a bainar jama’a.

Daga Hagu: Injiniya Muntari Sagir, Alhaji Jirgin Sama’ila (Jibson), da Sarkin Fulanin Galadiman Katsina, da sauran mahalarta taron

Game da mu’amalar rayuwa kuwa, haƙiƙa Musulmi ya kamata ya kasance wakili na alheri a ko’ina, har da kafar intanet. Dandalin sada zumunta na iya zama wata hanya mai kyau ta yaɗa addini da kyawawan halaye idan aka yi amfani da ita bisa adalci da tsoron Allah. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya ga wani mummunan aiki a cikin al’umma, to ya gyara da hannunsa, idan ba zai iya ba, da bakinsa, idan har hakan ma ba zai iya ba, to ya ƙi abin a zuciyarsa…” (Muslim).

Wajibi ne ga Musulmi ya lura cewa, duk abin da yake yi, mala’iku na rubutawa. Wallafawa ko yin comment a kan wani abu na laifi, ko kallon abubuwa haram, duk suna cikin abin da ake rubutawa. Allah ya ce: “Babu wata kalma da zai faɗi sai akwai mai lura da rubutawa a gabansa.” (Surah Qaf: 18). Wannan yana nuna cewa duk abin da ake aikatawa a kafar sada zumunta zai bayyana a ranar hisabi.

Daga ƙarshe, Dokta Aminu Waziri ya shawarci mutane da cewa, yana da kyau Musulmi ya mayar da Soshalmidiya matsayin wata hanya ta neman lada, ta hanyar yaɗa ilimin addini, ingantattun hadisan Manzon Allah, da karfafa zumunta cikin gaskiya da amana. “Duniya wata rana za ta ƙare, amma duk abin da aka aikata za a sake ganinsa a gaban Allah. Don haka, kada mu bari kafar da za ta iya zama hanya ta alheri ta koma hanyar da za ta kai mu ga halaka. Allah ya shiryar da mu baki ɗaya.” In ji Dokta Waziri, a yayin da yake ƙarkare ta’aliƙinsa.

In sha Allahu, a rahoto na gaba, za mu kawo maku jawabi na musamman daga bakin Sardaunan Matasan Galadiman Katsina, Malam Abdul’aziz Ibn Abdul’aziz.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

Jajirtataccen Jigo A Fagen Samar Da Nagartaccen Shugabanci: Gabatarwar Littafin Tarihin Dokta Adegoroye

Next Post

2027 and the Rise of a Third Force: Can ADC’s Political Heavyweights Unseat Tinubu?

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
2027 and the Rise of a Third Force: Can ADC’s Political Heavyweights Unseat Tinubu?

2027 and the Rise of a Third Force: Can ADC’s Political Heavyweights Unseat Tinubu?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

December 14, 2025
Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

Matsalar Tsaro A Najeriya: Madalla Da Majalisar Dokokin Amurka

November 26, 2025
TSOKACINMU NA YAU (24)

TSOKACINMU NA YAU (24)

March 24, 2025
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (6)

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (6)

August 14, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.