Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC
Daga Aminu Lawan Hassan

__________
A yayin da ake tunkarar kakar zaɓe a baɗi, tuni jam’iyyu da ‘yan siyasa suka fara shirye-shirye, domin ganin sun cin ma nasara a muƙaman da ke akwai, tun daga na Shugaban Ƙasa, Majalisun Tarayya, Gwamnoni da sauransu. Kan haka ake ganin cewa jam’iyyu biyu ne za su fi gwada ƙwanji – jam’iyya mai mulki ta APC da kuma mafi ƙarfin adawa ta ADC.
Ɗan kasuwa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Aminu Lawan Hassan ya zayyano wasu shawarwari da dubaru, waɗanda yake tunanin cewa idan Jam’iyyar Adawa ta ADC ta bi su, to za ta iya wujijjiga Jam’iyya mai mulki ta APC, ta kafa gwamnati a Najeriya.
Malam Aminu, ya bayyana shawarwarin nasa ne a shafinsa na Facebook, inda ya buɗe da cewa: “ADC, ita ce jam’iyyar da ake wa kallon za ta iya ƙalubalantar Jam’iyyar APC mai mulki amma sai ta yi da gaske saboda APC ba ta shirya barin mulki ba. Za ta yi duk mai yiwuwa, domin ta ga ta ci gaba da mulki ko ta halin ƙaƙa.”
Ya ci gaba da cewa, “daga cikin shirye-shiryen da take yi, akwai ƙoƙarin ta ga ta mayar da Nigeria tsarin jam’iyya ɗaya, wanda tana dab da cin ma burinta; domin ta bi duk wata hanya ta mayar da gwamnonin jam’iyyun adawa nata, wanda ‘yan adawa suke zargin amfani da kuɗi da tsoratarwa.”
A cewarsu, “abu na biyu shi ne, ƙoƙarin rufe bakin ‘yan adawa ta hanyar cinna masu hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa kuma ana zargin ta da haɗa rikicin cikin gida wajen amfani da Wike a PDP da Nafi’u a ADC. Sannan za ta yi amfani da ƙabilanci da addini wajen hilatar masu zaɓe.
“Hakazalika, za ta yi amfani da halin talauci da ƙuncin rayuwa da ta tsunduma ‘yan Nijeriya a ciki, wajen raba shinkafa da taliya da sauran kayan masarufi, har ma da kuɗi.”
A nazarin nasa, Malam Aminu ya ce, “ita kanta Hukumar Zabe wato INEC, abar zargi ce, domin tun yanzu ‘yan adawa da ƙungiyoyi sun fara kiraye-kiyayen a sauke shugabanta.”
Ya ce, “idan Jam’iyyar ADC tana so ta kuɓuta daga waɗannan makirce-makircen na Jam’iyyar APC, to ga shawara: A sani fa, ADC babu wani abin da za ta faɗa wa ‘yan Najeriya da za su yarda da ita, domin mutanen cikinta ba wasu sababbi ba ne kuma ba sahihai ba ne. Mutane ne waɗanda akasarinsu, da su aka rusa Najeriya, aka tatse ta kuma ‘yan Nijeriya kar suke kallonsu. Sun san taron fusatattu ne da waɗanda ba a yi da su, da waɗanda suka faɗi zaɓe. Saboda haka babu wata guguwa da za su yi amfani da ita wajen kayar da APC, kamar yadda Buhari ya yi a 2015.
“Abin da ya rage wa ADC,” in ji Aminu, “shi ne amfani da kaifin hankali wajen zaɓen ‘yan takararta. Da farko shi ne, Atiku Abubakar da Peter Obi su haƙura da takara. Dalilina kuwa shi ne, duk wanda aka ɗauka a cikinsu, APC za ta yi amfani da ƙabilanci wajen ɓata shi. Idan ka ɗauki Atiku, ‘yan Kudu za su ga Arewa suna so su ƙwaci mulki daga hannunsu ne, alhalin ba su gama zangonsu (tenure) na shekara 8 ba. Sannan Kiristocin Arewa tun da suka fahimci tsarin Muslim Muslim yaudara ce, za su gwammace su sake zaɓen Tinubu, tun da sun ga ya fi karkata a kansu fiye da Musulmai,
“Idan suka tsayar da Peter Obi kuwa, akasarin ‘yan Arewa Musulmai za su gwammace su sake zaɓen Tinubu, domin sun san sharrin Inyamiri ya fi na Beyarabe, sannan ana zarginsa da mugun ƙabilanci, lokacin da yake Gwamna a Jihar Anambra.”
A ci gaba da nazarin nasa, Malam Aminu ya ce, “abin da ADC za su yi shi ne, su nemo Goodluck Ebele Jonathan, su haɗa shi Dlda Rabi’u Musa Kwankwaso, su ba su takara.
“Tunanin masu tunani zai koma kan cewa, ai a lokacin Goodluck an yi fama da matsalar Boko Haram, sai dai kuma na san duk zargin da aka yi wa Jonathan bai wuce wannan ba; sai dai a ce an yi rashawa lokacinsa da ƙabilanci. Amma duk abin da za a yi zargi a wannan Glgwamnatin da ta Buhari, an yi ko ana yin sa ninki goma. Da Boko Haram, da ‘yan bindigar daji da ƙabilanci da rashawa da kama karya da sata, waɗannan sun ninka waɗancan.
“Hikimar kawo Goodluck ita ce, shi Kirista ne, ɗan Kudu, mai sauƙin ƙabilanci, mai jin maganar ‘yan Najeriya, akwai tausayin talakawa a lamarinsa kuma faɗuwarsa zaɓe ta sa ya fahimci kurakuran da ya tafka. Ga shi kuma zango (tenure) ɗaya zai yi, daga nan ɗan Arewa ya zo ya nema ba hamayya a gaba. Inyamurai za su haƙura su zaɓe shi. ‘Yan Nejdelta za su zaɓe shi. Kiristocin Kudu da Arewa za su zaɓe shi kuma zai samu goyon bayan ƙasashen Yamma saboda Obama ya bayar da gudunmawa wajen kayar da shi a 2015, Trump zai goya masa baya; domin ya baƙanta wa ‘yan Jam’iyyar Democrat rai kuma ga shi Shugaba Tinubu ba ya shiri da Trump.”
Malam Aminu ya ƙarƙare nazarinsa da cewa: “Haɗa Kwankwaso da Goodluck za ta sanya takararsu ta samu gagarumar nasara da miliyoyin ƙuri’u. Wani zai ce Kwankwaso a 2023 ƙuri’a miliyan ɗaya ya samu. Haƙiƙanin gaskiya Kwankwaso ya fi Peter Obi ƙuri’u. Shi iya mutanen Kano ne suka zaɓe shi, sauran jihohin Arewa ba su zaɓe shi ba, saboda sun san mulkin Kudu zai koma. Saboda Arewa sun yi takwas kuma ga yaudarar tsarin Muslim-Muslim ya yi tasiri. Abin da zai daɗa karya APC, shi ne ta maye gurbin Kashim Shettima da Kirista. A nan ne mutanen Arewa maso Yamma da na Arewa maso Gabas za su ce ba da su ake mulkin ba. Za su tuttuɗa wa ADC (Goodluck/Kwankwaso) ƙuri’u.
Aminu ya ce, “tabbas, idan ADC suka yi wannan haɗin, sai Peter Obi ya koma ya a nemi takarar Sanata, a banƙara ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ko kuma a ba shi Sakataren Gwamnatin Tarayya. Yadda ‘yan Najeriya suke a ƙufulen nan, Goodluck ne kawai zai ci zaɓe, ba ba a yi hayaniya ba. Shugaba Tinubu ba zai yadda ya faɗi a hannun Atiku ba ko Peter ba.”
Abin jira a gani dai shi ne, ko Jam’iyyar ADC za su ɗauki waɗannan shawarwari? Haka kuma, idan sun amince da hakan, ko za su iya nasarar kayar da Shugaba Tinubu, kamar yadda Malam Aminu Hassan ya hasaso? Gare ku jama’ar ƙasa, yaya kuke ganin za ta kaya a zaɓen baɗi, idan Allah ya kai mu, rai da lafiya? Ku bayyana ra’ayoyinku a Comment Section.
______












