• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (2)

RAHOTON MUSAMMAN

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 27, 2025
in Gizago
0
KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (2)

Harkar sufuri a hannun gwani

38
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (2)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Harkar sufuri a hannun gwani

 

 

 

 

√ Wane Ne Malam Haruna Musa Rugoji?

A rahotonmu na farko, mun tsaya ne daidai inda muka yi wannan tambaya ta sama, domin neman sanin mutumin da a yanzu haka, yake shugabantar wannan hukuma mai matuƙar muhimmanci ga al’umma – KTSTA. Ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar a ranar 30 ga Oktoba, 2018 har zuwa yau da muke haɗa wannan rahoto 27-07-2025.

Masu iya magana dai suna cewa, a san mutum a san cinikinsa, ko kasuwa a san dillali. Kamar kuma yadda suka ce, da mai kamar zuwa kan aika, da itace mai gwafa ake yin ƙota. Kamar yadda aka ambata dai, sunansa Malam Haruna Musa Rugoji, (CTN, NPOM, FICEN, FIICA, FlnsTA) – lambobin girma ne da ya mallaka da suka danganci ƙwarewa a fagagen ilimi da sana’a.

An haifi Malam Haruna a garin Malumfashi Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 1973. Ya yi karatun firamare a Dudi Primary School Malumfashi, sakandare a Government Day Secondary School Malumfashi, daga nan kuma ya halarci Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic Zaria, inda ya samu Difiloma a Harkokin Kasuwanci.

Malam Haruna Musa Rugoji

Ilimi abokin tafiya, Malam Rugoji bai huta ba, bayan Nuhu Bamalli Polytechnic, sai kuma ya tafi Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Jihar Kano, inda ya samu shaidar Babbar Difiloma a Ilimin Tsimi Da Tanadi, Hadin Gwiwa da Shugabanci.

Haka kuma ya yi karatun Difiloma ta Musamman a Ilimin Shugabanci, a Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi. Daga nan bai huta ba, duk dai domin bunƙasa iliminsa, Malam ya je Jami’ar Bayero Kano, inda ya samu shaidar Digiri Na Biyu, a Ilimin Gudanar Da Sana’a (tare da ƙwarewa a fannin Kasuwanci). Himma ba ta ga raggo – ya sake tafiya Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, har ila yau, inda ya ƙara yin wani karatun Digirin na Biyu, a Ilimin Harkokin Sufuri Da Dakon Kaya (2020-2024).

Daga waɗannan manyan makarantu da ya halarta, Malam Haruna ya samu wadataccen ilimin tafiyar da kowace irin sana’a da harkokin kasuwanci, musamman ma harkar sufuri – inda ya fi ƙwarewa a baɗini da kuma aikace. Haka kuma ya samu ƙwarewa a harkar gudanar da shugabanci da mu’amala da mutane. A yanzu haka kuma yana kan ci gaba da nazari da bincike ta fuskar sufuri, dakon kaya, kasuwanci, haɗin gwiwa, bunƙasa sana’a da gudanarwa a zamanance, ta fuskar amfani da fasahar zamani, kamar yadda ake gudanarwa a manyan ƙasashen da suka ci gaba. Wannan ke ƙara tabbatar da cewa, an ajiye ƙwarya a daidai burminta, da aka ba shi shugabancin wannan hukuma ta sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA).

A can baya, kafin Malam Haruna ya kama aiki a matsayin Shugaban Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina, ya yi aiki da sana’o’i, ko dai na ƙashin kansa ko kuma na gwamnati. Misali, Malam Rugoji ya yi aikin koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic kuma babu shakka ya cika dukkan sharuɗɗa da ƙa’idojin aiki, tsakaninsa da hukumar makaranta da ɗalibai da sauransu – sai san barka.

Mutumin mutane: Malam Haruna tare da Marigayi Dokta Ali Muhammad Garba na BUK tare da wasu mutane, a yayin wani taro, shekarun baya

Haka kuma, daga ranar 13 ga Agusta, 2018 zuwa 30 ga Oktoba, 2018, Gwamnan Jihar Katsina a lokacin, Alhaji Aminu Bello Masari ya naɗa shi muƙamin Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA). A nan ma, tabbatattun shaida sun shaida yadda ya gudanar da aikin hukumar cikin nagarta, gaskiya da adalci, inda a cikin ƙankanen lokacin da ya shugabanci hukumar, aka ga gagarumin canji da biyan buƙata. A ɓangaren kasuwanci kuwa, ya taɓa zama Janar Manaja na gidan man Loyal Abdul Son Petroleum Nig. Ltd. na Shiryar Gombe (2010-2015).

In sha Allahu a rahoto kashi na 3, za mu ƙarƙare bayani game da Shugaban Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina, Malam Haruna Musa Rugoji, daga nan kuma mu shiga batutuwan da suka shafi hukumar kai tsaye. A ci gaba da biyo mu.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

YAU MALUMFASHI MUN YI RASHI

Next Post

BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
BINCIKE:  Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ta’aziyyar Ngũgĩ wa Thiong’o: Zakaran Adabin Afirka (1938-2025)

Ta’aziyyar Ngũgĩ wa Thiong’o: Zakaran Adabin Afirka (1938-2025)

May 29, 2025
SASSANYAN AMINCI (1)

SASSANYAN AMINCI (1)

September 4, 2025
Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

February 13, 2026
TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (5)

TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (5)

July 24, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.