Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta ƙaddamar da Kwamitin Asusun Tallafi, domin bunƙasa ilimi, ƙarfafa tattalin arziki da rayuwar al’umma a faɗin Arewacin Najeriya.
Kwamitin yana ƙarƙashin jagorancin tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Dakta Muhammad Dahiru Abubakar, CFR da tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata Simon Bako Lalong.
An ɗora wa kwamitin alhakin samar da jagoranci na dabaru da kuma tabbatar da nasarar aiwatar da manufofin asusun na tallafi.
Da yake jawabi yayin bikin ƙaddamar da kwamitin, Shugaban Kwamitin Amintattu na ACF, Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yaba wa mambobin ƙungiyar bisa ci gaba da nuna sadaukarwa, goyon baya da kuma jajircewa ga manufofi da ƙimar ƙungiyar. Ya bayyana cewa asusun wani babban mataki ne na ƙarfafa damar ilimi, tallafa wa shirye-shiryen raya al’umma da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a dukkan sassan Arewacin Najeriya.
Alhaji Dalhatu ya jaddada cewa ACF za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki, abokan hulɗar ci gaba da shugabannin al’umma domin inganta zaman lafiya, haɗin kai, shugabanci nagari da ci gaban ƙasa baki ɗaya. A cewarsa, asusun zai kasance wata muhimmiyar hanya ta magance ƙalubalen ci gaba da ke fuskantar yankin Arewa.

Shugaban na ACF ya tuna cewa ƙungiyar ta ƙaddamar da asusun tallafi na Naira biliyan 100 a lokacin bikin cika shekaru 25 da kafuwar ta. Ya bayyana cewa duk da cewa mutane da ƙungiyoyi daban-daban sun yi alƙawarin bayar da jimillar Naira biliyan 7.8, an samu biyan kusan Naira biliyan 3.9 ne kawai, wanda yanzu haka suke ajiye a asusun ACF da ke bankin Jaiz.
Ya tabbatar wa mambobi da masu ruwa da tsaki cewa kuɗaɗen da aka tara suna cikin tsaro da kariya, tare da ƙarfafa sabon kwamitin da ya fara aiwatar da shirye-shiryen tallafin jin ƙai da ci gaban al’umma a faɗin Arewacin Najeriya. Haka kuma ya yi kira ga waɗanda suka yi alƙawarin bayar da gudunmawa da su cika alkawurransu, domin a cin ma manufofin da aka kafa asusun domin su.
A cewarsa, “Kyakkyawan aikin da za mu yi da kuɗaɗen da muke da su yanzu, tabbas zai jawo ƙarin tallafi da goyon baya daga mutane da ƙungiyoyin da suka himmatu wajen ci gaban Arewacin Najeriya.”
Alhaji Dalhatu ya kuma nuna matuƙar godiya ga dukkan mutane, kamfanoni da ƙungiyoyin da suka bayar da gudunmawa ga asusun tallafin. Ya yi kira ga sauran fitattun ’ya’yan Arewacin Najeriya da su mara wa wannan shiri mai albarka baya, ta hanyar bayar da gudunmawar kuɗi domin gina Arewa mai ci gaba da wadata.
Ya jaddada cewa haɗin kai da ci gaba da bayar da goyon baya su ne ginshiƙan cin ma manufofin asusun, musamman a fannoni kamar ilimi, ƙarfafa matasa, bunƙasa shugabanci da inganta walwalar al’umma.
Shugaban na ACF ya kuma tabbatar wa masu bayar da gudunmawa da sauran masu ruwa da tsaki cewa za a yi amfani da dukkan kuɗaɗen da aka samu cikin hikima da riƙon amana wajen aiwatar da ayyuka masu amfani da tasiri ga al’umma. Ya ce asusun zai mayar da hankali kan inganta ilimi, ƙarfafa matasa, tallafa wa al’umma masu rauni da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a fannin tattalin arziki da zamantakewa a Arewacin Najeriya.
A cewarsa, ƙoƙarin da mambobin ACF ke ci gaba da yi ya taimaka matuƙa wajen gina ƙasa da kuma dawo da kyawawan ɗabi’u da ƙimomin da ke haifar da ci gaba, zaman lafiya da wadata ga dukkan ’yan Najeriya.
Ana sa ran sabon asusun tallafin zai kasance wata kafar gaskiya da riƙon amana wajen tara albarkatu domin tallafa wa shirye-shiryen ilimi, ƙarfafa matasa, bunƙasa shugabanci da sauran muhimman ayyuka da za su inganta walwala da ci gaban tattalin arzikin al’ummomin Arewacin Najeriya.
__________











