Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
• An Buƙaci A Yi Bincike
Daga Wakilinmu
__________
Ƙungiyar Gamayyar Kare Haƙƙin Mata ta Najeriya (Nigerian Women International Alliance – NWIA) ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da an gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaskiya da adalci game da mutuwar wata budurwa kuma ƙwararriyar mai aikin tausar jiki (Physiotherapist) mai suna Mary Habila.
Kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito, budurwar dai ta rasu ne a gidan Ministan Ayyuka Dave Umahi, lamarin da ya haifar da damuwa a tsakanin jama’a.
A cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 13 ga Yuli, 2026, wadda Shugabar ƙungiyar, Misis Omolara Abike, Mataimakiyarta Misis Ogonna Chiedum da Sakatariyar ƙungiyar, Dr. Mariam Adeosun suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, yanayin da mutuwar Mary ta faru na buƙatar cikakken bincike mai zaman kansa, cikin gaskiya da ƙwarewa domin ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin shari’a.

Ƙungiyar ta jaddada cewa ba ta zargi kowa da aikata wani laifi ba, tana mai cewa kowane ɗan Najeriya yana da haƙƙin a ɗauke shi mara laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka, tare da ba shi cikakkiyar kariyar doka da bin ƙa’idojin shari’a.
A cewar ƙungiyar, “Rahoton mutuwar Mary Habila, wata ƙwararriyar mai aikin tausar jiki da gyaran jiki, a gidan Mai Girma Ministan Ayyuka ya haifar da matuƙar damuwa a tsakanin jama’a kuma ya cancanci a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, na ƙwararru kuma cikin gaskiya da bayyana komai ga jama’a.”
Ta ƙara da cewa, “Wannan wasiƙa ba yunƙuri ba ne na ayyana wani a matsayin mai laifi. Kowane ɗan Najeriya yana da haƙƙin tsarin mulki na a ɗauke shi mara laifi har sai an tabbatar da laifinsa, tare da kariyar bin ƙa’idojin shari’a. Sai dai kuma, duk wanda yake riƙe da babban muƙamin gwamnati, yana da ƙarin nauyin amincewa da cikakken bincike cikin gaskiya da bayyana gaskiya.”
Ƙungiyar ta NWIA, ta bayyana cewa damuwarta ta samo asali ne daga wasu ƙorafe-ƙorafe da zarge-zargen jama’a da aka daɗe ana dangantawa da ministan, sai dai ta jaddada cewa ba a tabbatar da waɗannan zarge-zarge a matsayin gaskiya ba.
Ƙungiyar ta ce, “Ba mu gabatar da waɗannan zarge-zarge a matsayin tabbatattun hujjoji ba. Maimakon haka, mun yi imanin cewa idan aka samu yawaitar damuwa ko ƙorafe-ƙorafe kan wani jami’in gwamnati, abin da ya dace shi ne hukumomin da abin ya shafa su binciki duk wani ƙorafi mai inganci cikin adalci da ‘yancin kai.”
Ƙungiyar ta bayyana cewa gudanar da bincike cikin gaskiya kan batutuwan da suka shafi jami’an gwamnati zai ƙarfafa hukumomin gwamnati ne, maimakon ya raunana su.
Ta yi gargadin cewa rashin gudanar da bincike mai inganci kuma abin amincewa, zai iya rage amincewar jama’a da hukumomin gwamnati, ya sa waɗanda aka zalunta ko masu bayar da shaida su ji tsoron kai rahoton abin da suka sani, ya ɓata sunan Najeriya wajen kyakkyawan shugabanci da bin doka, ya rage amincewar masu zuba jari, tare da ƙara rarrabuwar kawuna a siyasa.
Ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar cewa binciken mutuwar Mary Habila ya gudana ba tare da katsalandan daga kowa ba kuma bisa tanadin doka. Haka kuma ta yi kira da a tabbatar an kiyaye dukkan shaidu na kimiyyar binciken laifuka (forensic evidence), ciki har da rahoton gwajin gawa (autopsy), a ba da kariya ga shaidu da masu ƙorafi daga tsoratarwa ko barazana, a mutunta haƙƙoƙin kundin tsarin mulki na dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, sannan a bayyana sakamakon binciken cikin gaskiya.
Da take kira ga Shugaba Tinubu, ƙungiyar ta ce: “Abin da zai zama abin tarihi a mulkinka, ba wai ko an yi zarge-zarge a lokacin gwamnatinka ba ne. Abin da za a auna shi ne ko gwamnatinka ta tabbatar cewa doka ta yi aiki iri ɗaya ga kowa, ba tare da la’akari da muƙami ko tasiri ba.”
Yayin da ƙungiyar ta sake tabbatar da goyon bayanta ga ƙoƙarin Gwamnatin Tinubu na bunƙasa ci gaban ƙasa, ta buƙaci shugaban da ya nuna cewa babu wani jami’in gwamnati da ya fi ƙarfin ɗaukar alhaki kuma rayuwar kowane ɗan Najeriya tana da daraja ɗaya a gaban doka.
__________













