• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, July 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 11, 2026
in Babban Labari
0
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

Wasu daga cikin ɗaliban da aka ceto daga hannun 'yan ta'adda

17
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026

__________

An kuɓutar da jimillar ɗalibai da malamai 44 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Oriire da ke Jihar Oyo, bayan wani gagarumin aikin tsaro na sama da wata guda da ya haɗa rundunonin tsaro da hukumomin leƙen asiri daban-daban na Najeriya.

An sace waɗannan ɗalibai da malamai ne a ranar 15 ga Mayu, 2026, kafin su samu ‘yanci a jiya Juma’a, 10 ga Yulin bana; sakamakon wani tsari na ayyukan tsaro da aka gudanar bisa ingantattun bayanan sirri domin rushe ƙungiyar ‘yan ta’addar da ta shirya sace su.

Babban Hafsan Runduna ta 2 ta Sojojin Najeriya da ke Ibadan (General Officer Commanding – GOC), Manjo Janar CR Nnebeife ne ya jagoranci wannan aiki tare da sauran hukumomin tsaro da suka gudanar da aikin cikin cikakkiyar haɗin gwiwa.

Bangon Mujallar Taskar Gizago Mai Lamba 59

A cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 2 ta Sojojin Najeriya, Laftanar Kanar Danjuma Jonah Danjuma ya fitar, ya bayyana cewa Sojojin Najeriya sun gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar rundunoni na musamman daga Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA), musamman Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa, rundunonin musamman na Sojojin Ƙasa, Sojojin Ruwa da Sojojin Sama, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Hukumar Leken Asirin Waje ta Ƙasa (NIA), Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) da kuma jami’an sa-kai, mafarauta da ƙungiyar tsaron sa-kai ta  Amotekun.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an tsaron sun gudanar da wani dogon aiki bisa bayanan sirri, wanda ya mayar da hankali wajen gano jagororin ƙungiyar ‘yan ta’addar da suka shirya satar, rushe tsarin ayyukansu, katse hanyoyin samar musu da kayan aiki da tallafi, tare da gano masu ba su bayanai da kuma maɓoyarsu.

“Mafi yawan waɗannan ayyuka sun gudana ne a cikin dajin Old Oyo National Park da ke Jihar Oyo, tare da bazuwa zuwa wasu jihohin ƙasar nan,” kamar yadda jam’in na hulɗa da jama’a ya bayyana.

A yayin gudanar da aikin, jami’an tsaro sun kama mutane da dama a Jihar Oyo da wasu sassan Najeriya. A cewar sanarwar, “jami’an tsaron sun tarwatsa tsarin ƙungiyar, sun raunana ƙarfinta, tare da matsa mata lamba har ta kai ga sakin ɗaliban da malamansu, ba tare da wani sharaɗi ba.”

Mahukuntan soja sun bayyana cewa an tsara tare da aiwatar da aikin cikin matuƙar taka-tsan-tsan, domin kare rayukan waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma kauce wa jikkata fararen hula.

Duk da nasarar da aka samu wajen ceto mutanen, sanarwar ta bayyana cewa wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu ko suka jikkata yayin gudanar da aikin, abin da ke nuna irin sadaukarwar da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A halin yanzu, ɗaliban da malamansu da aka kuɓutar suna karɓar kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba, inda ake duba lafiyarsu tare da ba su magani. Ana sa ran daga baya za a miƙa su ga Gwamnatin Jihar Oyo, domin haɗa su da iyalansu.

Da yake yabawa da nasarar aikin, Manjo Janar CR Nnebeife ya miƙa godiyarsa ga Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunonin Sojojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, bisa jagoranci, goyon baya da kuma samar da dukkan abubuwan da suka taimaka wajen samun nasarar wannan aiki. Haka kuma ya gode wa Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde da al’ummar jihar bisa ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken haɗin kai tun daga farkon lamarin har zuwa ƙarshe.

Babban Hafsan Rundunar ya kuma yaba wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Ministan Tsaro, Babban Hafsan Tsaro, Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, sauran Shugabannin Rundunonin Tsaro, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Daraktocin Janar na DSS da NIA da shugabannin sauran hukumomin tsaro, bisa kyakkyawae haɗin kai da suka nuna, wanda ya tabbatar da gudanar da aikin cikin tsari da nasara.

Har ila yau, ya gode wa kafafen yaɗa labarai da daukacin ‘yan Najeriya saboda haƙuri, fahimta da kuma ci gaba da nuna amincewa da tsarin tsaron ƙasa. Ya buƙaci jama’a su ci gaba da kasancewa cikin shiri, tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri cikin lokaci; domin ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na kare rayuka da dukiyoyi a faɗin Najeriya.

Nasarar wannan aiki na ceto na daga cikin manyan nasarorin haɗin gwiwar hukumomin tsaro da aka samu a baya-bayan nan kuma hakan ya sake nuna muhimmancin amfani da ingantattun bayanan sirri da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro wajen yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a Najeriya.

Mahukunta sun bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da wasu ƙarin ayyuka, domin kamo sauran ‘yan ta’addar da ke da hannu a wannan aika-aika tare da hana aukuwar irin waɗannan hare-hare a nan gaba.

__________

Previous Post

Afirka Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya Na Bana

Next Post

Kofin Duniya: Gobe Za A Fara Fafata Wasan Gab Da Na Ƙarshe

Related Posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
Babban Labari

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria
Babban Labari

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026
Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda
Babban Labari

Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

June 20, 2026
Next Post
Kofin Duniya: Gobe Za A Fara Fafata Wasan Gab Da Na Ƙarshe

Kofin Duniya: Gobe Za A Fara Fafata Wasan Gab Da Na Ƙarshe

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Johann Ya Doke Dangote: Shi Ne Ya Fi Kowa Kuɗi A Afirka

Johann Ya Doke Dangote: Shi Ne Ya Fi Kowa Kuɗi A Afirka

June 21, 2023
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

July 10, 2025
Organized Crime: AANI Calls for Enhanced Collaboration to Combat the Menace in Africa

Organized Crime: AANI Calls for Enhanced Collaboration to Combat the Menace in Africa

October 24, 2023
RANAR HAUSA TA DUNIYA: LITTAFINA NA FARKO DA AKA WALLAFA A 1997

RANAR HAUSA TA DUNIYA: LITTAFINA NA FARKO DA AKA WALLAFA A 1997

August 26, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.