• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Noma Da Kiwo

SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 17, 2023
in Noma Da Kiwo
0
SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

Sharif Almuhajir cikin gonarsa

46
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

~~~~~~~
A yayin da daminar bana ta fara nisa, Mujallar Taskar Gizago ta tuntuɓi Dokta Sharif Almuhajir, manomi a Jihar Yobe, domin jin hali da yanayin da damina take a yankin nasu. Haka kuma a matsayinsa na matashi, malamin jami’a, masanin tattalin arziki, za mu ji shawarwari daga gare shi, da zai ba matasan Arewa, dangane da noma da kiwo.
~~~~~~~

Related posts

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024
DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau

DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau

September 2, 2023
Sharif Almuhajir, a bakin aikin gona
Attarugu a gonar Almuhajir

TG: Ko za mu fara da gabatar da kanka a taƙaice?

ALMUHAJIR: Farko dai sunana Sheriff Muhammad Ibrahim, wanda aka fi sani da Dokta Sheriff Almuhajir. Ni Associate Professor (Ɗangaladiman Farfesa) ne a bangaren Ilimin Tattalin Arzikin Addinin Musulumci (Islamic Financial Administration). Ina karantarwa a Jami’ar Jihar Yobe, sannan kuma a yanzu haka ni ne Shugaban Bankin Tallafa wa Ƙananan Masana’antu na Jihar Yobe (Yobe State Microfinance Bank).

Na yi karatun Alƙur’ani mai girma a matakin farko a makarantar Alƙur’ani da mahaifina ya assasa a garin Maiduguri. Sannan na je School for Higher Islamic Studies. Na yi sakandare, na yi digiri na farko a Jami’ar Maiduguri, na biyu a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato. Na yi wani digirin na biyu a Jami’ar Almadina International University. Sannan na yi digirin-digirgir (PhD) a University of Islamic Sciences da ke Malaysia. Kuma na kai shekaru goma sha biyar ina karantarwa a Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu ya zuwa yanzu.

TG: Tun yaushe ka fara noma kuma yaya yanayin abubuwan da ka noma a bana, ko akwai alamar haske?

ALMUHAJIR: Da farko na fara noma ne ta ɓangaren kiwon dabbobi, musamman kajin Turawa tun ina ɗalibin a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2001. Sannan na buɗe gona mai girma da nake sarrafawa a shekarar 2013. Daga bisani na bari na koma karatu a Malaysia, inda bayan na dawo na ci gaba da harkar noma tun a shekarar 2016 kuma har zuwa yanzun nan ban daina ba.

Sai dai bayan da aka naɗa ni Shugaban Yobe Microfinance Bank na fara muamala da ƙananan manoma, waɗanda muke bai wa ƙananan jari su yi noma, sannan su biya daga baya. Dayake muna bibiyar manoman domin tabbatar da cewa sun yi amfani da kuɗaɗen da muka ba su daidai, a hankali har na fara tunanin cewa lallai sana’ar noman abinci da sauran tsirrai tana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar talaka, musamman ma ma’aikacin gwamnati. Saboda harkar noma za ta ba shi lokaci isassshe da zai yi aikinsa na gwamnati kuma ya kula da gonar tasa. Dalilin haka sai na fara shiga noman sosai.

Daga farko na fara ne da noman damuna. Na shuka gero a shekarar 2020, duk da ban tsaya na ba da kulawa irin yadda ya dace sosai ba, an samu albarka daidai gwargwado. A hankali har na dawo noman rani. A shekarar farko na noma alkama, daga baya na koma noma abubuwa da dama kamar shinkafa, masara, gero, gyaɗa, gangala, zoɓo, attarugu, tattasai da barkono. Kuma na shuka irin dabino guda dubu ashirin, sannan ina da burin zuwa gaba in ƙara shuka wasu abubuwan.

TG: Waɗanne irin ƙalubale kai kanka da manoman Jihar Yobe suke fuskanta, musamman a daminar bana?

ALMUHAJIR: Ƙalubale yana nan a harkar noma kamar yadda yake a kowacce harka amma ma fi girman ƙalubalen na manoma a Jihar Yobe ya ƙunshi jarin sana’ar noma, ƙarancin ruwan sama da na ƙasa a wasu wurare, ko’inkula na ma’aikatan gona, ambaliyar ruwa a wasu wurare, rashin ma’ajiyar kayan gona ingatacce da yake jawo lalacewar kayan gona, tsadar kayan aiki da kuɗin ma’aikata da kuma karyewar farashin kayan gona, musamman lokacin rani.

TG: A matsayinka na matashi, manomi, masanin tattalin arziki kuma malamin jami’a, ko za ka ba matasan Arewa shawarwari dangane da noma da kiwo domin jawo hankali da ƙarfafa gwiwa?

ALMUHAJIR: Shawara ta ga matasa ita ce, kowa yayi ƙoƙari ya rungumi aikin noma ko a matsayin sana’a ko a matsayin noman abinci, domin noma shi ne zai hutar da mu daga kukan hauhawar kayan abinci. Noma sana’a ce da kan iya riƙe mutum tsawon rayuwarsa, ba tare da ya nemi aiki a wajen wasu ba. Wanda ba shi da kuɗin mallakar gona sai ya nemi ta haya. Wanda ba shi da jarin noma ya je ya yi ƙwadago, a hakan zai koya kuma zai samu kuɗin noma tasa gonar nan gaba.

A ƙarshe, ina so in yi kira ga attajiranmu na yankin Arewa da su dawo da hankalinsu wajen ƙarfafa gwiwar matasa a kan abin da ya shafi harkar noma, saboda babu shakka wannan hanya ce da za ta samar da ayyukan yi, kuma ta sake bunƙasa tattalin arzikinsu da na ƙasa baki ɗaya.
~~~~~~~~

Previous Post

Batun Tsaro A Malam Madori: Jan Hankali Ga Hukumomi Da Al’umma

Next Post

RABON MUƘAMAN SHUGABA TINUBU: Kuskure Kan Kuskure

Related Posts

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA
Noma Da Kiwo

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024
DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau
Noma Da Kiwo

DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau

September 2, 2023
NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano
Noma Da Kiwo

NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

August 22, 2023
Next Post
RABON MUƘAMAN SHUGABA TINUBU: Kuskure Kan Kuskure

RABON MUƘAMAN SHUGABA TINUBU: Kuskure Kan Kuskure

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SHIRIN GWAMNA ABBA GIDA-GIDA NA RABA TALLAFIN AWAKAN KIWO YANA KAN DAIDAI

SHIRIN GWAMNA ABBA GIDA-GIDA NA RABA TALLAFIN AWAKAN KIWO YANA KAN DAIDAI

January 23, 2025
INSECURITY IN NORTHERN NIGERIA: AN OPEN LETTER TO NSA NUHU RIBADU

TAƁARƁAREWAR TSARO A AREWA: BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MALAM NUHU RIBADU

August 8, 2025
General Buratai Wears New Status As Patron of Institute of Security…

General Buratai Wears New Status As Patron of Institute of Security…

November 24, 2024
TSOKACINMU NA YAU (15)

TSOKACINMU NA YAU (15)

March 15, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.