TARON MALUMFASHI FACEBOOK CONNECT: YUNKURIN BUNKASA MALUMFASHI DA KEWAYE (5)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Kamar yadda rahoton baya ya gabata, a wannan karon, wanda shi ne kashi na biyar, za mu zayyano kaɗan daga cikin jawabin da ɗaya daga cikin ginshiƙan matasan da suka assasa wannan muhimmin taro. Wannan kuwa shi ne Sardaunan Matasan Galadiman Katsina, Abdul’aziz Bin Abdul’aziz. Domin kuwa bayan da Dokta Aminu Waziri ya kammala ta’aliƙin muƙalar da Malam Haruna Musa Rugoji ya gabatar, sai aka gabatar da Sardauna, domin nasa jawabin na musamman.
√ Wane Ne Sardaunan Matasa?
Malam Abdul’aziz ɗaya ne daga cikin zaƙaƙuran matasan Malumfashi masu himma da kishin yi wa al’umma hidima. An haife shi a garin Malumfashi a ranar 29 ga watan Mayu, 1980. Ya yi karatu har matakin Digiri a Kimiyyar Siyasa.
Ta fannin aiki kuwa, shi ƙwararre ne ta fuskar sufuri, musamman jigilar kaya daga Kudancin Najeriya zuwa Arewa da sauran sassan ƙasa. Haka kuma ɗan kasuwar motocin ne da kayan gyaransu. Ga shi kuma ɗan siyasa, mai kishin gina al’umma.

Sardauna mutum ne mai matuƙar ƙoƙari a kan duk wani abu da ya shafi al’umma. Misali, kamar aikin gayya ko faɗakarwa da makamantansu. A yanzu haka yadda al’amarin tsaro ya taɓarɓare a yankin Malumfashi da kewaye, yana daga cikin jajirtattun da ke taimakawa da lokacinsa da dukiyarsa wajen tsaron gari.
√ Jawabin Sardauna A Zauren Taro:
A yayin jawabinsa, Sardaunan Matasa ya maida hankali ne kacokan zuwa ga al’amuran da suka shafi al’ummar Malumfashi da kewaye, da yadda za a magance matsalolin da ke addabar mutane, musamman kamar matsalar tsaro, bunƙasa harkokin kasuwanci da samar wa matasa ayyukan yi.

Ta fuskar inganta tsaro a Malumfashi da kewaye, Sardauna ya koka da yadda ake ja da baya wajen bayar da taimako ga jami’an sa-kai ta fuskar tsaro. Ya ba da misali da wasu wurare da aka ci gaba, inda al’umma ke haɗuwa su ba da agaji sosai domin inganta harkar tsaro. Dalili ke nan ya ba da shawara da cewa ya kamata a kafa wata babbar gidauniya, inda magidanta za su riƙa bayar da aƙalla Naira 500 a wani ayyanannen lokaci. Ya ce daga wannan gidauniya za a riƙa samun abin da za a riƙa bayar da ɗan alawus ga jami’an sa-kai da suke ba da lokacinsu domin aikin tsaron gari.

Haka kuma, ya yaba da ƙoƙarin Injiniya Muntari Sagir ta ɓangaren taimakon ‘yan sa-kai, domin tabbatar da tsaro a Malumfashi da kewaye. Ya ba da misalin yadda shi Injiniya ya fitar da miliyoyin Naira ya samar da na’urorin oba-oba da rigunan ruwa da takalma da fitilu da sauransu ga ‘yan sa-kai, domin inganta tsaron gari. A kan haka ya yi kira na musamman ga attajirai da ‘yan kasuwa da su yi koyi da shi Injiniya ta wannan fanni na taimakon inganta tsaro.

A jawabin nasa, Sardauna ya koka da rashin kamfanoni da ƙananan masana’antu a garin Malumfashi da kewaye. Ya ce lallai lokaci ya yi da ya kamata attajirai da ‘yan kasuwa su zuba jari domin samar da irin waɗannan masana’antu da kamfanoni. A cewarsa, samar da masana’antun zai magance zaman banza da ɗinbin matasa ke yi, zai bunƙasa tattalin arziƙin yankin kamar kuma yadda garin zai ƙara bunƙasa.
Bayan haka, Sardauna ya buƙaci manyan ‘yan boko na yankin Malumfashi da kewaye da su taimaka wajen ganin an kafa manyan makarantu a garin. Ya ce, a can baya an samu damarmaki masu yawa domin haka, amma aka yi sakaci suka kuɓuce. “Muna gani sai a ɗauki babbar makaranta a kai wasu yankuna, alhali a nan ya kamata a kafa su.” In ji shi.
A rahoto kashi na 6, za mu karkata zuwa ga muhimman mutanen da aka karrama a yayin wannan taro. Za mu fara da Injiniya Muntari Sagir, wanda shi ma ya gabatar da jawabi, a yayin da aka karrama shi.
_______________
Bashir Malumfashi shi ne Editan Mujallar Tsakar Gizago (online)













