• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, August 23, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home

Tsakanin Rarara Da Pantami: Yayin Da Maroƙi Ya Zaci Shi Wani Ƙusa Ne…

TSOKACINMU NA MAKO

Mohammed Bello Doka by Mohammed Bello Doka
August 2, 2026
in Gizago
0
14
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Tsakanin Rarara Da Pantami: Yayin Da Maroƙi Ya Zaci Shi Wani Ƙusa Ne…

Daga Mohammed Bello Doka

Related posts

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

August 13, 2026
Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

July 30, 2026

__________

Lokacin da Davido ya kira Rarara da jahili, a yayin musayar kalamai da suka yi kan sace ɗaliban makaranta a Jihar Oyo, masu kare Rarara sun gaggauta lulluɓe shi da rigar tausayi. “Rarara Musulmi ne,” suka ce. “Rarara ya yi karatun tsangaya,” suka tunatar da jama’a. “Rarara fitaccen mawaƙin Arewa ne da ake girmamawa, don haka bai kamata a kwatanta shi da wani Kiristan Kudancin kamar Davido ba.” Duk wata suka da ake yi wa Rarara, a cewarsu, hari ne kan Musulunci da kuma martabar Arewacin Najeriya.

Sai kuma Rarara ya zauna a gaban kyamara ya yi wa Sheikh Isa Ali Pantami kalamai na cin mutunci waɗanda ba su dace a maimaita su ba.

Mutumin da aka kare da hujjar addini, shi ne yanzu ya tauye martabar addinin da aka jingina wajen kare shi. Muryoyin da suka yi ihu suna zargin Davido da ƙyamar Musulunci, yanzu sun yi shiru yayin da Rarara ke jefa munanan kalamai ga ɗaya daga cikin manyan malamai da ake girmamawa a Arewacin Najeriya. Farfesa ne. Tsohon Minista ne. Mutumin da ya shafe shekaru masu yawa yana hidimar ilimi har ya samu matsayi na musamman a zukatan miliyoyin mutane.

Rarara kamar filfilo ne da ya ɗauka shi tsuntsu ne; maroƙin da yake jiji da kansa, yana tunanin shi wani ƙusa ne a ƙasa. Kuma idan irin wannan ruɗin ya kama mutum, lokacin taɓarɓarewa da faɗuwarsa ce take zuwa, kodayake ba a san yaushe ne ƙarshen nasa zai zo ba.

A al’adar Hausawa, bambanci tsakanin malami da maroƙi ba bambancin sana’a kaɗai ba ne. Bambanci ne mai tushe. Malami yana samun matsayinsa ne ta hanyar ilimi, taƙawa da hidimar al’umma. Darajarsa tana ginuwa ne a kan shekaru na koyo da koyarwa da kuma shiryar da al’umma zuwa ga kyawawan ɗabi’u. Maroki kuwa, a gefe guda, mai nishaɗantarwa ne, wanda sana’arsa ita ce yabon masu mulki kuma rayuwarsa tana dogara ne da kyautar masu iko.

A ma’anarta ta tarihi, maroƙi mai bara ne. Ba a matsayin zagi ba, amma a matsayin ma’ana. Ba ya rera waƙa domin gaskiya, sai domin abin da zai samu. Muryarsa ba tasa ba ce gaba ɗaya.

Wannan bambanci ya daɗe yana tabbatar da daidaiton al’ummar Arewa tsawon zamani. Malamai sun gina iyalai da al’umma, sun koyar da tawali’u, ladabi, ɗa’a da tsoron Allah. Tasirinsu ya samo asali ne daga ilimi da kyawawan halaye, ba daga tafi ko kusanci da masu mulki ba. Saboda haka babban take haƙƙi ne, idan maroƙi ya kuskura ya zagi malami. Suka wani abu ne, rashin girmamawa kuma wani abu ne daban. Lokacin da Rarara ya tunkari Sheikh Pantami da shaguɓe, ba wai yana sukar wani fitaccen mutum ba ne kawai; yana ɓatanci ne ga cibiyar ilimin Musulunci da masu kare shi suka ce shi ma yana wakilta.

Sheikh Pantami yana da daraja ba saboda wani muƙamin siyasa da ya taɓa riƙewa ba, sai saboda shekaru masu yawa da ya sadaukar wajen ilimin Musulunci, koyarwa da gudunmowar ilimi. Tasirinsa ya wuce siyasa. Matsayinsa ya samo asali ne daga ilimi da ɗabi’a, ba daga tafi ko kusanci da iko ba. Wannan girmamawa ba za a iya rushe ta saboda waƙa ko saɓanin siyasa kawai ba. Lokacin da Rarara ya zagi Sheikh Pantami, ya zagi duk Musulmin da ke kallon malamai a matsayin jagororin ɗabi’a. Ya zagi kowane ɗalibin da ya zauna a gaban malamai yana neman ilimi. Ya kuma zagi kowane iyali da ya taɓa neman shawarar malamai a lokacin ƙunci.

Ka yi la’akari da wannan abin mamaki. Mahaifiyar Rarara ma ta taɓa faɗawa hannun ‘yan bindiga. Ya biya kuɗin fansa. Bai yi wata magana kan gwamnati ba. Ya yi shiru yayin da iyalinsa ke cikin wahala. Amma lokacin da Davido ya yi magana kan yaran makaranta da aka sace daga birnin Los Angeles, Rarara ya fusata ƙwarai. Ya kira fitaccen mawaƙin da ɗan ta’adda. Ya zarge shi da tona asiri. Ya yi alfahari da kusancinsa da Shugaba Tinubu.

Mutumin da bai iya kare mahaifiyarsa ba ya tsaya yana biya wa fitaccen tauraron duniya darasi kan tsaro. Mutumin da fadar mulki ke mallakar muryarsa, ya kai hari ga mutumin da ya yi magana cikin ‘yanci. Arewa ce ta fi shan wahalar rashin tsaro. Hankalin duniya kan matsalar sace mutane a Najeriya zai iya zama alheri. Amma Rarara ya ga hakan a matsayin barazana, ba ga mutanensa ba, sai ga masu ɗaukar nauyinsa.

Rayuwar Rarara ita kanta tana nuna labarin mutumin da ke ƙoƙarin samun matsayin da bai cancanta ba. Iƙirarinsa na samun digirin girmamawa daga wata jami’a ya gamu da ƙaryatawa daga ita kanta cibiyar da aka ce ta ba shi, abin da ya bayyana cewa lamarin ya kasance na yaudara. Ga wani mutum mai matsananciyar neman karɓuwa, amma daga ƙarshe ya gamu da abin kunya. Wannan hoto ne mai cike da takaici na maroƙin da ke neman rawanin da ba a tanadar masa ba.

Ko addininsa ma ba zai iya kare shi ba. A wasu tsauraran fahimtocin fiƙihun Musulunci, kiɗa da bara, ana kallonsu a matsayin haram. Mutumin da ke iƙirarin zurfin sanin Alƙur’ani amma ya gina rayuwarsa gaba ɗaya kan waƙoƙin yabo da dogaro da siyasa, yana rayuwa cikin saɓo. Ya kai hari ga malamin da hidimarsa ga Musulunci ta shafe rayuwa baki ɗaya, alhali shahararsa tasa ta ɗan lokaci ce. Yana alfahari da sanin sirrika, amma bai iya kare mahaifiyarsa ba. Yana kiran wasu ‘yan ta’adda, alhali yankinsa na ci gaba da zubar da jini.

Rarara ya ruɗu da siyasa a matsayi na dindindin. Ya ɗauki kusanci da iko a matsayin iko kansa. Ya manta cewa fadar da ke ciyar da shi a yau, tana iya watsar da shi gobe. Shahara ta ɗan lokaci ce. Daraja kuwa ana samunta ne bayan rayuwa mai cike da hidima. Lokacin da fitattun masu sana’ar samar da nishaɗi suka yi watsi da al’adu da ƙa’idojin addini da suka daɗe suna riƙe al’umma, suna aika wa matasa saƙo mai haɗari game da yadda ya kamata a riƙa mu’amala da manya, malamai da masu ilimi, lamarin ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Arewacin Najeriya ya daɗe yana ware wa malamansa matsayi na musamman. Bambancin ra’ayi abu ne da ba makawa. Amma bai kamata ya rikiɗe zuwa izgili ko cin mutuncin waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen neman ilimi da shiryar da al’umma ba. Rarara yanzu ya aikata babban kuskure a sana’arsa. Ya juya wa ginshiƙan da suka ɗora al’ummarsa baya. Ya zagi malami. Ya kare gwamnatin da ta gaza kare mahaifiyarsa. Kuma da hakan, ya bayyana kansa a matsayin abin da yake a zahiri: maroƙin da ya ruɗu da ɗan abin da ya samu na wucin gadi a matsayin ɗaukaka.

Waɗanda suka lulluɓe shi da rigar Musulunci domin kare shi daga Davido, yanzu dole su fuskanci gaskiya. Mutumin da suka kare, shi ne yanzu ya ci mutuncin ilimin Musulunci kansa. Asalin Musuluncin da suka ɗaga tutarsa wajen kare shi, shi ne yanzu ya tauye martabarsa. Ba za su iya riƙe bangarorin biyu lokaci guda ba. Idan za a kare Rarara saboda shi Musulmi ne, to dole kuma a hukunta shi a matsayin Musulmi saboda zagin ɗaya daga cikin manyan malaman Musulunci da ake girmamawa.

Lokacin da maroƙi ya ruɗu da amfanin da ake da shi na ɗan lokaci a matsayi na dindindin, lokacin da mai bara ya ɗauka shi wani jan wuya ne, rushewar ɗaukakarsa tabbas ce. Ƙasa ma ta riga ta fara zamewa daga ƙarƙashin ƙafafunsa. Ruwa a cokali dai, ya ishi mai hankali wanka!

_________

Mohammed Bello Doka

E-mail: bellodoka82@gmail.com

Previous Post

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

Next Post

Still Around

Related Posts

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?
Gizago

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

August 13, 2026
Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?
Gizago

Ko Yaya Za A Fassara Wannan Kallon?

July 30, 2026
Saƙon Godiya Da Bangajiya
Gizago

Saƙon Godiya Da Bangajiya

July 22, 2026
Next Post
Still Around

Still Around

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

Hukuma Ta Kafa Sabbin Sassa Domin Bunƙasa Al’umma A Jihar Katsina

August 8, 2026
BAKIN JAƁA (5)

BAKIN JAƁA (5)

September 24, 2025
YAU TAKE SALLAH!

YAU TAKE SALLAH!

March 20, 2026
IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu
  • Musulunci Ba Addinin Tsauri Ko Sakaci Ba Ne…

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon

August 23, 2026
Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

August 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.