ZUWA GA ‘YAN UWA MUSULMI ‘YAN SHI’A: SHIN DA GASKE KUNA KOYI DA ALI (RTA) NE?
• ZO NAN KU JI HALAYENSA A NAHJUL BALAGHA
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

••••••••••
Ɗan uwa, shin da gaske kai ɗan Shi’a ne kuma mai ƙauna da koyi da Sayyidina Ali bin Abi Ɗalib? Kuma shin ka karanta ingantaccen littafin Nahjul Balagha? To zo nan mu ɗan amfani juna dangane da kyawawan halayen wannan jarumin gwarzo, sahihin mutum abin koyi na ƙwarai – Ali Mazan Fama!
Sayyiduna Ali bin Abi Ɗalib (RTA) ɗaya ne daga cikin sahabbai mafiya kusanci da Annabi Muhammad (S.A.W). Shi ɗan kawun Manzon Allah ne, kuma wanda ya fara karɓar Musulunci daga cikin matasa. Halayensa sun kasance ginshiƙai masu ƙarfi da daraja a cikin rayuwar Musulmi. A cikin littafin Nahjul Balagha, Ali (R.A) ya bayyana falsafar rayuwa da ƙa’idojin da suka ginu a kan tsoron Allah, haƙuri, yafiya da sauran kyawawan ɗabi’u da ke tabbatar da irin zurfin imaninsa.
Allah ya ƙara masa yarda, shugaba ɗan Abi Ɗalib ya kasance mutum mai tsananin tsoron Allah. Tun daga yarintarsa har zuwa ƙarshen rayuwarsa, ayyukansa da halayensa sun shaida irin tsantsar tsoron Allansa da kiyaye dokokinsa. Tsoron Allah ya kasance jagoransa a kowane aiki. Ya gina rayuwarsa bisa ladabi da tsoron Mai Duka, yana kauce wa zalunci da son zuciya. A cikin Nahjul Balagha, a wasiyyarsa ga ɗansa Hassan (RTA) yana cewa: “Na ƙarfafa muku tsoron Allah, domin shi ne abin da ke haddasa kyakkyawan tunani, kuma shi ne ginshiƙin alheri.”
Ya kai ɗan uwa ɗan Shi’a, ka ji wasiyyarsa fa. Idan dai har kana koyi da shi ne, to ka kasance mai tsoron Allah, domin ka samu kyakkyawan tunani. Tunanin alheri da zai saita maka rayuwa, domin ka riƙa gudanar da rayuwar kirki da ƙaunar al’umma, ba rayuwar dabbobi ta gaba da ƙiyayya da mutane ba.
Sayyiduna Ali (RTA) ya mallaki gwalagwalan halayen haƙuri da Juriya: A rayuwarsa, ya fuskanci ƙalubale masu tarin yawa, musamman bayan wafatin Annabi (S.A.W). Duk da haka, ya kasance mai juriyar hali da sauƙin kai. Bai kasance mai tsokanar faɗa ko tada tarzoma ba. Bai da tarihin rama cuta da cuta, sai dai yakan yi haƙuri da juriya. Game da amfani da muhimmancin haƙuri a rayuwa, an ruwaito a Nahjul Balagha yana cewa: “Haƙuri tamkar kan mutum ne babu gangar jiki.” Ma’anar wannan kalami shi ne, duk wanda ba ya da haƙuri, to shi ba cikakken mutum ba ne.
Ya kai ɗan uwa, to a ina ka koyi rashin haƙuri game da ƙalubalen rayuwa? Ina ka koyi ƙunduma zagi ko tozarta wanda ya saɓa da fahimtarka? Ina ka koyi jidali da ƙullata ga Musulmin da ya saɓa maka ko kake iƙirarin ya zalunce ka? Ba dai wajen Sayyiduna Ali ba, domin shi mai haƙuri ne kuma mai juriya da halin rayuwa. Idan dai har shi ya jure manyan ƙalubalen da suka bijiro masa a zamaninsa, to kai me zai hana ka yi koyi da shi a naka zamanin?
Sayyidina Ali ya kasance babban mai ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin danginsa da al’umma gaba ɗaya. A cikin Nahjul Balagha, yana cewa: “Sada zumunci na ƙara arziki kuma yana jinkirta ajali.” Wannan yana nuna yadda Ali ya fahimci muhimmancin haɗin kai da girmama dangi. To ya kai ɗan uwa mai koyi da Ali (RTA), a ina ka samo halayyar wariya da tawaye wa ‘yan uwa Musulmi da tona masu asiri da cin zarafi?
Wata babbar ɗabi’ar Sayyiduna Ali, ita ce ta yafiya. Ya kasance mai yawan yafiya ga waɗanda suka zalunce shi. Yana ganin yafiya tamkar daraja ce ta mutum mai ƙarfi ba mai rauni ba. Da yake bayani game da “Yafiya” a littafin Nahjul Balagha, yana cewa: “Ramuwa ba ita ce jarumta ba, mutumin da ya yafe a lokacin da yake da ƙarfin ramuwa, shi ne jarumi mai ƙarfin zuciya.”
Ya kai ɗan uwa masoyin Ali, to ka ji irin halinsa dangane da yafiya. To kai ina ka samo ɗabi’ar ramuwa? Ina ka samo halayyar cewa ba za ka yafe wa wane ba, saboda kaza da kaza, duk kuwa da cewa ya mutu? Ina ka samo halayyar bibiyar rayuwar Sahabban da suka yi zamani da Manzon Allah cikin salama, ka ce za ka yi gaba da su, da rama masu wani saɓani da suka yi, duk da cewa sun yafi juna?
Tarihi ingantacce ya tabbatar mana da cewa Ali Bin Abi Ɗalib (RTA) mutum ne mai son zaman lafiya a rayuwarsa. Ya zaɓi zaman lafiya fiye da yaƙi, duk da cewa shi gwarzo ne a fagen fama. A cikin wata wasiƙarsa da ya aika zuwa ga Malik al-Ashtar, yana cewa: “Ka zama mai son zaman lafiya fiye da yaƙi, muddin hakan zai tabbatar da adalci da kare marasa ƙarfi.” Ali ya fahimci cewa zaman lafiya shi ne mafita ga al’umma, kuma babu ci gaba idan babu zaman lafiya.
Ya kai ɗan uwa ɗan Shi’a, a ina ka samo halayyar zanga-zanga da neman jafa’i? Ina ka samo halayyar ƙuntata wa al’umma da tare masu hanyoyi da sunan zanga-zanga? Ni kuwa na ce ba dai daga Ali mazan fama ba (RTA). Shi sahihin mutum ne mai so da jaddada zaman lafiya.
Sayyiduna Ali (RTA) ya kasance gwani mai kishin Musulunci. An ruwaito a Nahjul Balagha yana cewa: “Ku kasance kariya ga addinin Allah, kamar yadda kuke kare gidajenku daga gobara.” Ali ya ɗauki Musulunci a matsayin abin da ya fi rayuwarsa daraja, ya sadaukar da komai don kare addini.
Haka kuma shi ɗin dai, Sayyiduna Ali ya kasance a kodayaushe mai ƙoƙarin tabbatar da haɗin kan Musulmi. A tarihi, akwai lokacin da aka tauye masa haƙƙi, bayan wafatin Manzon Allah (saw) amma maimakon ya tashi ya ƙwaci haƙƙin nasa da ƙarfi – duk kuwa da cewa yana da ƙarfin, sai bai yi haka ba. Maimakon ya tayar da fitina tsakanin ‘yan uwa Musulmi, sai ya ce: “Zaman lafiya da Musulmai ya fi mini daraja fiye da mulki tare da rikici.”
Aliyu Mijin Fatima (rta), mutum ne tsayayyen adali, wanda ba ya yin gaba. A rayuwarsa, bai taɓa nuna ƙiyayya ga wanda ya saɓa masa ba, musamman idan addini ko gaskiya ce ke cikin lamarin. An ruwaito daga gare shi yana cewa: “Adalci ne mafi girman sadaka, kuma wanda ya fi kowa ƙarfi, shi ne wanda ya fi kowa adalci ga maƙiyansa.”
To ya kai ɗan uwa da kake tutiya da shi, ina ka samo baƙar halayyar rashin adalci da ƙin gaskiya? Ina ka samo ɗabi’ar takalar faɗa da hukuma kuma idan ta raunata ka, ka ishi kowa da raki? Na tabbata dai ba daga zakin fama, Ali sadauki ba!
Ya ‘yan uwa ‘yan Shi’a, lallai Sayyiduna Ali (rta) ɗaya ne daga cikin nagartattun Sahabban Manzon Allah Muhammadu (saw). Sun taimaki Musulunci da dukkan ƙarfinsu da dukiyarsu. Sun yi zumunci da juna, sun ƙarfafi juna, sun yi auratayya da juna. Ba su yi gaba ko ƙiyayya da juna ba, duk kuwa da cewa a matsayinsu na ‘yan Adam sun yi sabanin fahimta da juna. Allah (swt) ya tabbatar da tsarkin halayen Sahabban Manzon Allah a Alƙur’ani, Suratul Fathi, aya ta 29):
مُّحَمَّدٌ رَّسُولُ اللَّهِ ۚ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ ۖ تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا ۖ سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِم مِّنْ أَثَرِ السُّجُودِ ۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمْ فِي التَّوْرَاةِ ۚ وَمَثَلُهُمْ فِي الْإِنجِيلِ كَزَرْعٍ أَخْرَجَ شَطْأَهُ فَآزَرَهُ فَاسْتَغْلَظَ فَاسْتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِ يُعْجِبُ الزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ الْكُفَّارَ ۗ وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِنْهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا
Ma’ana: “Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waɗannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganinsu suna ruku’i masu sujada, suna neman falala daga Ubangijinsu, da yardarsa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujada. Wannan shi ne siffarsu, a cikin Attaura. Kuma siffarsu a cikin Injila, ita ce kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’annan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa’annan ya daidaita a kan ƙafafunsa, yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin (Allah) ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah ya yi wa’adi ga waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gafara da ijara mai girma.”
Daga ƙarshe, ya kai ɗan uwa ɗan Shi’a, ka sani cewa Sayyiduna Ali bin Abi Ɗalib (R.A) madubi ne na kyawawan halaye. Mutum ne da tsoron Allah, haƙuri, yafiya, sada zumunci da kishin Musulunci duk suka mamaye rayuwarsa. Duk Musulmin kirki zai yi koyi da ɗabi’unsa, domin kuwa sun ginu ne a kan koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W). Littafin Nahjul Balagha, yana ɗauke da hikima da fahimta da misalan rayuwar Sayyiduna Ali (rta) da za su haskaka rayuwar duk mai neman gaskiya. Idan ka saɓa daga waɗannan kyawawan halaye na Sayyiduna Ali, to kai ba masoyinsa ba ne kuma ba mabiyinsa ba ne na ƙwarai.
Ya Allah ka kyautata rayuwarmu, ka ɗora mu bisa shiriyar manzonka da sahabbansa managarta. Ka sa mu zama masu rahama da yafiyar juna, ka sa mu cika da kyau da imani.
__________
Bashir Malumfashi, marubuci/sha’iri, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online).














Slm malam inaganinka kamar wayaiye ammaga tambaya shin aduniya kaji yan shia nakashe rayuwa yanzu shekaru 40 dasuka wuce kaji zakzaky yace adaukifansar zaluncinda akemasa koko kai din irin yan shiar gwamnatine kuma bakada wata alaqa takusa konesa da malam yakubu yahya tuntuni munsan irinku kumada dai dai allah zairusa ireirenku
Salam malam kacanja tunani zuwaga sonrai IDANHAR YAN SHIA.BASAKOYI DA IMAM ALI YA.AKAI AKETAKASHESU KAJISUNRAMA AMMAYANZU AKWAI MASUCEWA MAHAIFAN ANNABI(S)NAWUTA MI AKAIMASU AMMADA ANCE ZURIYAR MA.AIKI SUNFI SAHABBAI YANZU ANJIKUKUNA IHU KUNATAFADIN AKASHESU TAMBAYA GAREKU DA SAHABBAI DA IYAYEN MANZO WANENE YAFI WANI AWURINKU? MU YANSHIAR ALI MUNCE IYAYEN ANNABI DA IYALANSA SUNFI ABU DA UMAR SANDA DA USMAN SAIKUYITA HAUSHINKU KAFIN QARFIN ALLAH YASAUKA GAREKU