• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, September 21, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati Ta Nemi Google Ya Daƙile Bazuwar Bayanan Da Ka Iya Wargaza Najeriya

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
October 14, 2023
in Labarai
0
Gwamnati Ta Nemi Google Ya Daƙile Bazuwar Bayanan Da Ka Iya Wargaza Najeriya

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da tawagar Google a ofishinsa

25
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamnati Ta Nemi Google Ya Daƙile Bazuwar Bayanan Da Ka Iya Wargaza Najeriya

Daga Wakilinmu

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026

~~~~~~~
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya roƙi kamfanin taskace bayanai a intanet, wato Google, da ya daƙile bazuwar dukkan saƙwannin da ka iya zama haɗari da barazana ga ɗorewar dunƙulalliyar al’umma a ƙasa ɗaya.

Ministan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar manyan jami’an Google na Afrika ta Yamma, bisa jagorancin daraktansu, Mista Olumide Balogun.

Tawagar ta kai masa ziyarar ne a ranar Alhamis, a Abuja.

Ya ce: “Akwai matuƙar muhimmanci a ga cewa an tantance tasiri da kuma illolin manhajojin yaɗa bayanai ta intanet. Ina ganin ku ne aikin hana yaɗuwar abu mai illa ya fi wajaba a kanku.

“Gwamnati ba ta da aniya ko tunanin ƙaƙaba wa ‘yancin faɗar albarkacin baki ko ‘yan jarida takunkumi. Shugaban Ƙasa ba mai so ya ga ana tauye ‘yancin faɗar albarkacin baki ba ne.

“To sai dai kuma idan har aka ce bayani mai haɗari ne, zai iya zama babbar matsala kenan a gare mu. Zai tarwatsa haɗin kanmu tare da haifar mana da ruɗu a cikin ƙasa.

“Mun san cewa isar da saƙwannin bayanai ta intanet na da muhimmanci sosai wajen ɗorewar ƙasa har ta tsaya da gindinta a matsayin ƙasa. Don haka akwai buƙatar samun ‘yancin bayyana ra’ayi a kafar da kowa zai ji ba a tauye masa haƙƙi ko ‘yanci ba.

“Saboda haka muddin aka samu fahimta ta hanyar isar da saƙwannin bayanai a cikin jama’a, to za a rage ɗarɗar da ambaliyar labarai na bogi. A kula, ‘yanci yana tafiya ne tare da sanin ƙa’idoji da ya kamata.”

Minista ya ƙara da cewa, Google na da gagarumin haƙƙi na ganin cewa haƙƙin da aka bai wa mutane suna watsa bayanai a soshiyalmidiya bai zama musabbabin haifar da hargitsi ga ‘yan Nijeriya ba.

Da yake nasa jawabin tun da farko, Mista Balogun ya shaida wa ministan cewa cikin shekaru uku da suka gabata zuwa yanzu kamfanin ya horas da ‘yan jarida 3,500 a Nijeriya.

Ya ce an horas da su ne dabarun amfani da hanyoyin fasahar zamani wajen tantance sahihan labarai, da tace labaran bogi da sauransu.

Previous Post

Some Communication Techniques During Crises

Next Post

KHALID IMAM: Tattaunawa Da Marubuci Mai Hannu Da Yawa

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
KHALID IMAM: Tattaunawa Da Marubuci Mai Hannu Da Yawa

KHALID IMAM: Tattaunawa Da Marubuci Mai Hannu Da Yawa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (8)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (8)

March 19, 2026
General Aliyu Commends Nigerian Army Depot for Relentless and Continuos Excellence

General Aliyu Commends Nigerian Army Depot for Relentless and Continuos Excellence

March 4, 2024
RANAR HAUSA TA DUNIYA

RANAR HAUSA TA DUNIYA

August 26, 2023
MUHAMMADU (SAW)

MUHAMMADU (SAW)

October 3, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.