• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

ƊAN BELLO: Tambarin Gwagwarmaya

ƘASIDA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 7, 2025
in Adabi
0
ƊAN BELLO: Tambarin Gwagwarmaya

Ɗan Bello: Tambarin Gwagwarmaya

677
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ƊAN BELLO
Tambarin Gwagwarmaya

Ɗan Bello: Tambarin Gwagwarmaya

__________
Wannan ƙasida daga Bashir Yahuza Malumfashi, sadaukarwa ce ga zaƙaƙurin ɗan gwagwarmayar tabbatar da mulkin gaskiya da adalci a Nigeria, Bello Galadancih, wanda aka fi sani da laƙanin Dan Bello.
                                                       __________

Related posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026

Ya Allahu, ga ni gare ka.
Na sallama kaina, a bautarka.
Na yabi Manzo, Badadinka.
Baban Fatima, ‘yar gatan Makka.
Roƙo a gare ka, ba zan gajiya ba.

Nai nufin kirari da muryata.
Wani gwarzo mai kishin ƙasata.
Ba ya gajiya wurin sassaita,
Al’amurra, bankaɗo zaluman ƙasata.
Wannan gwarzo, ba za ka ji kunya ba.

Malam Ɗan Bello, kana burge ni.
Bello Galadanchi, kai nai nufi ni.
Kai ke tsage gaskiya a ƙasar ni.
Zalunci ƙarara, duk ya firgita ni.
Jinjina a gare ka, ba zan fasa ba.

Mulaka’un ƙasarmu sun raina mu.
Sun mallake komai, suna dukan mu.
Sun raba kawuna, don su k+she mu.
Sun jirkita komai, har ma addininmu.
Shin hauka ake, a ce ba zan koka ba?

Sun zare subsidy a man gadonmu.
Sun maka haraji a dukkan lamurranmu.
Sun ƙukunce ‘yan adawa a ƙasarmu.
Ga shi sun bari ana ta k+she mu.
Shin jama’a, wai ba za mu farka ba?

Wai! A yau talaka ya bani.
An mai da shi ɗan-ba-ni-ba-ni.
An rarraba shi a sansani,
Cikin talauci da tsanani.
Lallai kam, ba za mu yafe ba.

Yau mulaka’u, kunya ta ƙaurace su.
Ba su san ta ba sam, rayuwarsu.
Cin amana, shi ne muradinsu.
Sai firgici, shi ne ruwan shan su.
Sun bar Allah, ba za su gane ba.

Dukiyar ƙasarmu, sun kwashe ta.
Sun rarrabe sassa, ko ko dukkanta.
Ga iyalai da karuwansu kwata.
Sun bi ƙasar, sun rarake ta.
Ba su san mutuwa na nan zuwa ba.

Ciwon kansu, sun ruga Ingila.
Ko ko Jamus, Faransa suna jigila.
Bikinsu ko bushasha, sai su shilla.
Dubai ko Amurka, ka ji gilla.
Ba su san hisabi na nan zuwa ba.

Masu mulki da attajiranmu,
Sun kashe ilimi a ƙasarmu.
Yara sai ragaita a titunanmu.
Babu aiki, ba sana’a garinmu.
Shin jama’a, ba za mu miƙe ba?

Sun ɗaukaka mawaƙi da Naira.
Ga Farfesa, an bar shi tsirara.
Gidansa, ruwan talauci ke kwarara.
Ɗalibai, an saka su fitsara.
Kaiconmu, in ba mu buɗe ido ba.

Ya ku jama’a, lallai mu tashi!
Mu ɗau aniya, babu fashi.
Mu ceto ƙasa daga ‘yan fashi.
Mu zaƙalƙale aiki da kishi.
‘Yancin ƙasarmu ba zai rushe ba.

Ku zo mu jera SABUWAR TAFIYA!
Ga Malam Bello mai aniya,
Da kyawun ƙuduri, gangariya.
Ku mu kamo rago, mu ƙyale akuya.
Nasararmu kam, ba za ta gaza ba.

Ya Allahu, ka ga ƙasarmu.
Ka ga yadda suka kassara mu.
Sun ƙwace komai, mallakarmu.
Sun murƙushe duk yunƙurinmu.
Kukanmu gare ka, ba za mu gaza ba.

Allah ka ceto mana ƙasarmu.
Ka yassare dukkan rayuwarmu.
Ka magance zaluncin nahiyarmu.
Ka murƙushe dukkan azzalumanmu.
Ka share hawayenmu, ya Rabba!
__________
© Bashir Yahuza Malumfashi
Juma’a-Eidil Kabir
10-12-1446 (Hijiriyya)
06-06-2025 (Miladiyya)
__________

Previous Post

Shin Wai Akwai So? (1)

Next Post

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

Related Posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

March 1, 2026
Next Post
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (7)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Najeriya

Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Najeriya

October 4, 2023
TASKAR GIZAGO NA TARE DA AHMAD MUSA

TASKAR GIZAGO NA TARE DA AHMAD MUSA

September 27, 2023
RAMADAN KARIM: 13-1447

RAMADAN KARIM: 13-1447

March 2, 2026
Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering… Under Review

Global Standards and Regional Realities: The Evolution of Anti-Money Laundering… Under Review

November 28, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.