• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Dausayin Kauna

Shin Wai Akwai So? (1)

DAUSAYIN ƘAUNA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 5, 2025
in Dausayin Kauna
0
Shin Wai Akwai So? (1)

Shin Wai Akwai So?

34
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Shin Wai Akwai So? (1)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
MENE NE SO?

MENE NE SO?

April 27, 2025
Shin Wai Akwai So?

A kwanakin baya, mun gabatar da muƙala, inda muka amsa tambayar ma’anar so, inda a ƙarshe muka yi tambayar cewa; shin akwai so, ko kuwa dai tunanin mutum ne kawai yake haska batun so a zuciya? To, a yau idan Allah ya yarda, za mu amsa wannan tambaya.

Tun da farko dai, ya kamata mu numfasa, mu yi tsam da ranmu sannan mu zurfafa tunani. Mu yi amfani da tunanin zuciyarmu da ƙwaƙwalwarmu domin amsa wannan tambaya, tun kafin ma mu nemi ƙarin bayani daga masana da magabata. Kuma babu shakka, mu shaida ne, cewa lallai akwai so kuma yana yin tasiri a rayuwarmu.

Dalili ke nan ma muke saka masoyanmu a zukatanmu, muke tarayya da su a cikin lamurranmu na rayuwa. Saboda akwai so, shi ya sa muke ji a ranmu cewa muna son wane ko wance. Muna ƙin wane ko wance.

Saboda akwai so, shi ya sa muke auren wane ko wance kuma muke ƙin auren wane ko wance. Saboda akwai so, shi ya sa muke sadaukar da kanmu ko abin hannunmu ga wane ko wance. Don haka, a bisa tunanin kanmu da nazarinmu, lallai akwai so!

To, bari kuma mu matsa gaba, domin tantance wannan tambaya. Shin me masana ko magabata suka ce? Manzon Allah, Muhammadu (saw) lallai ya tabbatar mana da cewa akwai so kuma akwai ƙi. Za mu gane haka ne ta hanyar bibiyar zantuttukansa da suka shafi lamarin so ko ƙi.

Hadisin Imam Bukhari, mai lamba 13 da na Imam Muslim, mai lamba 45, an ruwaito Manzon Allah (saw) yana cewa: “Ɗayanku ba zai kasance mai imani ba, har sai ya so wa ɗan uwansa, abin da yake so wa kansa.”

Daga wannan hadisi, za mu gane cewa, lallai akwai so. Abin da babu shi, babu yadda za a ce har Manzon Allah (saw) ya yi maganarsa.

A wani hadisin kuma, na Sahih Muslim, mai lamba 2566, Manzon Allah (saw) ya ce: “A Ranar Sakamako, Allah zai ce, ina waɗannan mutanen da suka so juna saboda girmana? Yau zan saka su cikin imuwata, ranar da babu wata inuwa sai dai tawa.”

Wannan babbar shaida ce da ke ƙara tabbatar mana cewa lallai akwai so, tun da Manzon Allah ya tabbatar mana da cewa Allah ya yi magana game da kalmar so.

Bari mu ƙara da Sunan Abi Dawud, hadisi mai lamba 5124, wanda aka ruwaito Manzon Allah (saw) yana cewa: “Idan wani ya ji a ransa cewa yana son ɗan uwansa, to ya sanar da shi cewa yana son shi.”

Ke nan ta tabbata akwai so, wanda kan ɗarsu a zukatan mutane. Wannan hadisi ya ƙara sanar da mu cewa mutum kan ji a ransa cewa yana son wani ko wata. Amsa dai ta tabbata, cewa lallai akwai wani abu mai suna so a rayuwar ‘yan Adam. Ga shi ma har Manzon Allah (saw) ya ba mu umurni da cewa, da zarar mun ji son wani ko wata ya kama mu, to mu sanar masa ko mata.

Jama’a, a nan za mu dakata, sai kuma a muƙala ta gaba, inda za mu tuntuɓi wasu masana, mu ji bayanansu kan cewa ko akwai so? Kafin sannan, ku shiga Comment Section, ku faɗa mana; shin ka taɓa kamuwa da son wata? Haka ke ma ‘yar uwa, kin taɓa son wani?
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (6)

Next Post

ƊAN BELLO: Tambarin Gwagwarmaya

Related Posts

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
Dausayin Kauna

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
MENE NE SO?
Dausayin Kauna

MENE NE SO?

April 27, 2025
KANA SON FAHIMTAR MATA?
Dausayin Kauna

KANA SON FAHIMTAR MATA?

November 9, 2023
Next Post
ƊAN BELLO: Tambarin Gwagwarmaya

ƊAN BELLO: Tambarin Gwagwarmaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

HARKAR TSARO A JIHAR KATSINA: Ƙarin Haske Kan Ƙudurorin Gwamna Raɗɗa

HARKAR TSARO A JIHAR KATSINA: Ƙarin Haske Kan Ƙudurorin Gwamna Raɗɗa

February 12, 2024
GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

November 27, 2025
Taron COP28: Shugaba Tinubu Da Ayarinsa Ba Sharholiya Ta Kai Su Dubai Ba – Minista Idris

Taron COP28: Shugaba Tinubu Da Ayarinsa Ba Sharholiya Ta Kai Su Dubai Ba – Minista Idris

December 6, 2023
I was a security guard – Tinubu addresses Nigerians in India

I was a security guard – Tinubu addresses Nigerians in India

September 8, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki
  • Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
  • ALHAMDU LILLAH

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

May 18, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.