• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, June 23, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

ADABI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 21, 2026
in Adabi
0
Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Dr. Bukar Usman

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Dakta Bukar Usman Zai Gabatar Da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Shahararren masanin al’adun gargajiya, marubuci kuma masanin tarihi, Dakta Bukar Usman, OON, zai gabatar da sharhin wani sabon littafin tarihi mai taken A History of Lassa (Tarihin Al’ummar Lassa).

Related posts

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna

Maryam ‘Yar Aljanna

June 20, 2026

An bayyana littafin a matsayin muhimmiyar gudunmawa ga rubutun tarihi, adana al’adu da kuma ƙara fahimtar ɗimbin gadon al’adun al’ummar Lassa.

Marubucin littafin, Abdulkadir Gambo Gadzama, zai ƙaddamar da shi a hukumance a wani babban taron ƙaddamarwa da ake sa ran halartar jama’a da dama a National Women Development Centre, da ke kan Titin Tafawa Balewa, a Babban Birnin Tarayya Abuja, ranar Asabar, 27 ga Yuni, 2026, da ƙarfe 10:00 na safe.

Dr. Bukar Usman zai gabatar da Sharhin Littafin Tarihin Al’ummar Lassa

Ana sa ran taron zai samu halartar manyan mutane daga gwamnati, cibiyoyin ilimi, sarakunan gargajiya da kuma masana daga fannoni daban-daban na rayuwa.

Dakta Usman, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Nazarin Fasaha Da Al’adun Gargajiya ta Najeriya, wato Nigerian Folklore Society (NFS) na yanzu, an gayyace shi domin ya kasance babban mai sharhi kan littafin, bayan wata wasiƙar gayyata da kwamitin shirya taron ya aika masa, mai ɗauke da kwanan wata 9 ga Yuni, 2026.

A cikin wasiƙar gayyatar, kwamitin ya bayyana cewa gagarumar gudummawar da Dakta Usman yake bayarwa a fannonin binciken tarihi, adabi, al’adu da tattaunawar ilimi ta ƙasa ne suka sa ya zama wanda ya fi dacewa da yin sharhin wannan littafi.

A cikin bayaninsa, kwamitin ya yaba wa marubucin bisa shekaru masu yawa da ya shafe yana gudanar da bincike mai zurfi da kuma samar da wani aiki da ya tattara tarihi, al’adu da ci gaban garin Lassa. Kwamitin ya ce littafin zai zama muhimmiyar madogara ga masu bincike, ɗalibai, masu tsara manufofi da kuma al’ummomin da za su zo nan gaba, masu sha’awar fahimtar yadda al’ummar Lassa suka samo asali da bunƙasa.

A cewar kwamitin, littattafan tarihi irin su A History of Lassa, suna taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihin jama’a da ƙarfafa asalin al’adu. Ya jaddada muhimmancin rubuta tarihin al’ummomi, domin tabbatar da cewa muhimman al’adu, abubuwan da aka fuskanta da nasarorin da aka samu ba su ɓace ba a tsawon lokaci.

Kwamitin ya kuma lura da cewa, littafin ya gabatar da cikakken bayani mai gamsarwa game da al’ummar Lassa da gudummawar da suka bayar wajen ci gaban zamantakewa, al’adu da siyasar yankin.

Haka kuma ya yaba wa marubucin bisa jajircewarsa wajen tabbatar da sahihanci, gudanar da bincike da nazarin tarihi, yana mai bayyana littafin a matsayin wata muhimmiyar gudummawa ga tarin rubuce-rubucen tarihin cikin gida da ke ƙaruwa a Najeriya.

Gwamnan Jihar Adamawa, Mai Girma Ahmadu Umaru Fintiri ne zai jagoranci taron a matsayin Babban Mai Ƙaddamarwa. Gwamnan, wanda kuma yake riƙe da sarautar gargajiya ta Shashilgar Margi, na daga cikin manyan baƙi da ake sa ran za su halarci taron.

Chief Joe Kyari Gadzama, SAN, mai sarautar gargajiya ta Sardaunan Uba, shi ne zai kasance Shugaban Taron, yayin da Manjo-Janar, Dakta Paul C. Tarfa (mai ritaya), mai sarautar gargajiya ta Yeriman Garkida, zai kasance Uban Taro. Haka kuma Uwargidan Asta P. Thahal, mai sarautar gargajiya ta Gimbiyan Garkida, ita ce za ta kasance Shugabar Mata ta Taron, yayin da Uwargida Parmata Ishaya za ta kasance Uwar Taro.

A madadin Kwamitin Shirya Taron, Shugaban Kwamitin Kwamishinan ‘Yan Sanda Samson V. Wudah (mai ritaya) da Sakatare Raymond Gadzama sun bayyana fatansu na samun cikakken goyon baya daga maahalartan da aka gayyata. Sun ce wallafar littafin A History of Lassa, wata muhimmiyar alama ce ta ci gaba a ƙoƙarin adana tarihi da al’adun al’ummar Lassa, domin amfanin al’ummomi masu zuwa.

Ana sa ran taron zai haɗa masu tsara manufofi, masana ilimi, ƙwararrun masana fasaha, sarakunan gargajiya, ƙwararru daga fannoni daban-daban na rayuwa da kuma sauran jama’a, wanda hakan zai sa taron ya zama mai amfani ta fuskar ilimi da kuma muhimmanci ga al’adu.

Shugaban Kwamitin ya ce: “Marubucin ya cancanci yabo bisa rubuta tarihin al’ummar Lassa da kuma bayar da gudummawa ga babban ƙoƙarin adana ɗimbin tarihin al’ummomin Najeriya.” Ya ƙara da cewa nasarar wallafa littafin A History of Lassa na nuna yadda ake ƙara fahimtar muhimmancin tarihin al’umma wajen gina ƙasa da kare al’adu.

Kwamitin ya bayyana fatan cewa wannan littafi zai zaburar da irin wannan yunƙuri a sauran sassan ƙasar nan, domin rubuta tarihin al’ummomin da har yanzu ba a ba da labarinsu yadda ya kamata ba.

Ana sa ran littafin zai kasance wata muhimmiyar madogara mai ɗorewa ga masana da masu karatu da ke neman zurfafa fahimta game da asali, al’adu da kuma ci gaban tarihin al’ummar Lassa.
___________

Previous Post

Matasa Masu Fusata Sun Ƙone Ofishin ’Yan Sanda

Next Post

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Related Posts

Maryam ‘Yar Aljanna (2)
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna (2)

June 22, 2026
Maryam ‘Yar Aljanna
Adabi

Maryam ‘Yar Aljanna

June 20, 2026
Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
Adabi

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
Next Post
Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Maryam 'Yar Aljanna (2)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024

Jajirtataccen Jigo A Fagen Samar Da Nagartaccen Shugabanci: Gabatarwar Littafin Tarihin Dokta Adegoroye

June 30, 2025
Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

November 16, 2023
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo
  • Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa
  • Maryam ‘Yar Aljanna (2)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

Tattaunawar Ɗan Jarida Da Bazawara ‘Yar Tuwo-Tuwo

June 23, 2026
Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

Ilimin Zamani: Babban Ƙalubale Ga Al’ummar Musulmin Arewa

June 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.