• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

Ɗanjuma Katsina by Ɗanjuma Katsina
August 9, 2023
in Gizago
2
KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

Shugaban Gwamnatin Soja ta Nijar, Abdourahamane Tchiani da Sarkin Kano (murabus), Muhammadu Sanusi II, a ziyarar da ya kai Nijar

215
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KUSKUREN MASU JUYIN MULKIN KASAR NIJAR

…Yanzu kasar na tsaka mai wuya

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

Danjuma Katsina

1. Kuskuren farko shi ne juyin mulkin da soja suka yi wa gwamnatin da jama’a suka zaba, kuma juyin mulkin na cin amana. Domin kuwa wanda aka amince masa ya amshi gwamnatin saboda kwadayin mulki.

Nijar kasa ce mai arziki, mutanen ta masu gaskiya ne, kuma jajirtattu ne, amma daya daga cikin abin da ya hana kasar cigaba da bunkasa akwai yawan juyin mulki.

2. Kuskure na biyu shi ne, daga tutar Rasha da masu juyin mulkin suka yi. Da masu juyin mulkin ba su danganta kansu da kowace kasa ba, sukan fifita kishin kasarsu sama da kowace kasa.

3. Kuskure na uku shi ne, muryar da aka ji shugaban sojan haya na Wagner yana goyon bayan juyin mulkin, kuma sojan da suka yi juyin mulkin ba su barranta kansu da muryar ba.

4. Kuskure kin sauraren tawagar da gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta tura, suka hana su shiga kasar, suka killace su a bakin filin jirgin kasar. Kamata ya yi masu juyin mulki su bude kafofin tattaunawa ta ko’ina, su tura wakilai kasashen makwabta da na duniya su yi bayanin abin da ya kai su ga juyin mulkin.

5. Kulle sararin samaniyar kasarsu, wanda wata babbar hanyar zirga-zirga ce ta jiragen kasashen duniya. Jiragen yaki da na fasinja sun sha bamban. Mali, Burkina Faso da Guinea suna goyon bayan juyin mulkin, amma sararin samaniyarsu a bude yake, me ya sa Nijar za ta rufe nata?

6. Na shida gayyatar sojan hayar kasar Rasha na Wagna a kasarsu don su taimaka masu. Sojan Wagna ana masu daukar ‘yan ta’adda a Yammacin Turai. Don haka gayyatar su kamar fito-na-fito ne kai tsaye da Yammacin Duniya.

7, Na bakwai shi ne, amincewa da wata hadakar soja tsakaninsu da kasashen Mali da Barkina Faso. Wannan zai zama wani karin kalubale ga Yammacin Turai da ECOWAS, wanda sai sun ga abin da zai ture wa buzu nadi.

8. Na takwas shi ne, hana Wakilin Majalisar Dinkin Duniya da na kasashen Afrika da na ECOWAS damar shiga kasar. Wannan ya nuna sun kulle duk wata kofar magana. Sun ki su saurara, ya za a saurare su?

Makwabciyarmu kasar Nijar na cikin halin tsaka mai wuya, wanda matsalarta za ta iya shafar Afrika baki daya, amma kasar Nijar ce za ta fi tagayyara.

Ko da ECOWAS ba ta kai hari ba, in dai ba sulhuntawa aka yi ba, Yammacin Turai ba za su taba bari kasar ta zauna lafiya ba, in dai kasar na samun goyon bayan kasar Rasha da sojan Wagna, Mali da Barkina Faso a cikin ta.

Wannan wani halin gaba kura baya siyaki, kuma mugun tsaka mai wuya kasar take a ciki.

Ko sojan da suka amshi kasar za su bari kasar ta zama wajen gwada karfin Turawan Yamma da na Gabashi? Ko tattaunawa da sulhu da hangen nesa za su yi aiki? Wannan lokaci ne zai tabbatar.

~~~~~~~

Muhammad Danjuma Katsina, Dan jarida ne, mawallafin jaridun Katsina City News da jaridar Taskar Labarai da ke bisa yanar gizo (08057777762, 07043777779)

~~~~~~~

Previous Post

Shugabanci A Aikace: Gwamna Raɗɗa Ya Jagoranci Jami’an Tsaro Wajen Farautar ‘Yan Ta’adda

Next Post

Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne - Dr. Bala Nuhu

Comments 2

  1. Abdulrashid I. Ahmed says:
    3 years ago

    Babban kuskure da sojoji maciya amana na Nijar suka yi a gani na shi ne ikirarin da suka yi cewa zasu kashe shugaba na halal, Mohammad Bazoum Idan har aka nemi Kawar da su daga kan mulki. Ina goyon bayan Kawar da wadannan sojoji domin ya zamo darasi a gaba.

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Wannan gaskiya ne. Sai dai idan ka lura, wannan tsokacin an rubuta shi ne kafin masu juyin mulkin su furta wannan matakin. Shi ya sa marubucin bai ambata shi ba cikin jerin kurakuran da ya zayyano

      Muna godiya sosai da wannan bayani naka. Muna fata za a ci gaba da bibiyar mu kuma ana yi mana tsokaci irin wannan.

      Ka huta lafiya.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

November 7, 2025
JIHAR KATSINA/MALUMFASHI MUN YI BABBAN RASHI

JIHAR KATSINA/MALUMFASHI MUN YI BABBAN RASHI

February 24, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

March 1, 2026
A Review of “Leadership in the Nigerian Civil Service…”

A Review of “Leadership in the Nigerian Civil Service…”

July 8, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki
  • Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447
  • ALHAMDU LILLAH

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

Turning Point Against Terror: The Fall of Abu-Bilal Al-Minuki

May 18, 2026
Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

Barkanmu Da Shiga Watan Dhul-Hijjah 1447

May 18, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.