Maryam ‘Yar Aljanna (2)
__________
Gabatarwa:
Wannan shi ne kashi na biyu kuma na ƙarshe na wannan ƙirƙirarren labari, wanda muka samu daga haziƙin adibi, Malam Nasiru G. Ahmad. Labari ne mai mai cike da abin tausayi da kuma darussa masu yawa. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:
__________

Aka yi sa’a, kuɗin da ake bin mutumin nan daidai suke da abin da ke hannunta, na ladan aikin da ta yi wa malamin nan mai ibada. Nan take ta fitar da kuɗin ta ba su, ta ‘yanta mutumin.
Mutumin da ta ‘yanta ya tambaye ta wace ce ita? Da ta habarta masa labarinta, sai ya ce in za ta amince zai kasance tare da ita, su nemi arziƙi tare. Ya ce duk abin da suka samu sai su riƙa rabawa tsakaninsu. Ya kuma ce kamata ya yi su hau jirgin ruwa su bar garin.
Matar ta amince, suka nufi bakin kogi.Yayin da suka isa bakin kogi, sai wannan mutum ya ce ta fara shiga jirgin ta zauna. Ya ce mata yana dawowa yanzu. Sai ya je ya sami masu jirgin ya ce musu ga wata baiwarsa can yana son sayar da ita. Suka yi ciniki ya karɓi awalajar, ya arce ya bar ta nan.
Har jirgi ya tashi ba ta ga abokin tafiyarta ba. Masu jirgi suka zo suna duba ta, har suna tattaɓa ta. Da ta yi magana sai suka ce ai sun riga sun saye ta daga wajen ubangidanta, don haka ta ba da kai kawai bori ya hau. Ita kuwa ta ce sam ba ta san wannan zance ba. Suna cikin wannan taƙaddama ne wata guguwa ta tashi cikin kogin, igiyar ruwa ta murɗa, nan take jirgin ya kife. Duk ilahirin mutanen da ke cikin jirgin suka nutse cikin kogi, in ban da wannan baiwar Allah da ta yi sa’ar kama wani allon jirgi, ya yi ta iyo da ita bisa ruwa.
A daidai wannan lokaci sarkin garin ya fito shan iska bakin kogi. Ya kuma ga tasowar guguwar ba a lokutan da ta saba tashi ba. Can sai ya hangi wannan mata tana ta walagigi bisa ruwa. Nan da nan ya ba da umarni, wasu fadawa suka je aka fito da ita. Ya sa aka tafi da ita gidansa. Ya umarci likitansa da ya kula da ita.
Yayin da ta farfaɗo, sarki ya tambaye ta labarinta. Ta zayyana masa duk abin da ya faru gare ta, tun daga ƙazafin ɗan uwan mijinta gare ta, har zuwa azzalumin da ya sayar da ita a matsayin baiwa.
Sarkin ya yaba da halinta da kuma kaifin basirarta. Ya nemi ya aure ta, ta kuwa amince. Saboda kaifin hankalinta, duk abin da sarkin nan zai yi sai ya nemi shawararta.
Labarinta ya yi tambari a duk sassan ƙasar da sarkin ke mulki. Ana nan kan haka, har cutar ajali ta kama sarki, ya faɗi ya mutu. Manyan ƙasa suka zauna shawarar wanda za su naɗa sarki, ra’ayinsu ya haɗu kan ba wanda ya fi cancanta kamar matar sarkin nan. Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa suka naɗa ta sarauniyar wannan ƙasa.
Wata rana sarauniya ta yi wani zama a ƙofar fada. Ta nemi a taro mata duk mazajen da ke ƙasar, a bijirar da su gabanta. Nan da nan kuwa kowa ya hallara. Mazaje suka shiga wucewa tana ganin su ɗaya bayan ɗaya. Can sai ga tsohon mijinta wanda ya sake ta ya kuma kore ta. Sai ta sa a tsayar da shi can gefe guda. Ƙanensa da ya yi mata sharri ma ya zo wucewa, ta sa aka tsayar da shi can kusa da ɗan uwansa. Mai ibadar da ta yi wa aiki da hadiminsa da ya kashe ɗan mai ibadar ma haka. Can kuma sai ga azzalumin da ya sayar da ita, shi ma ta sa aka tsayar da shi. Aka ware su can gefe guda.
Bayan an gama bijirar da mazajen, sai ta sa aka kawo waɗancan mutane da ta sa aka tsayar da su zuwa gabanta. Babu wanda ya gane ta daga cikinsu. Ta bayyana musu ko ita wace ce, sannan ta ce da tsohon mijinta: “Haƙiƙa kai ba ka da laifi, ɗan uwanka ne ya ha’ince ka.” Ta sa aka sallame shi. Ta dubi ɗan uwansa ta ce: “Kai kuma za a yi maka bulala tamanin, domin ƙazafin da ka yi wa matar ɗan uwanka.”
Ta sa aka sallami Malam mai ibada tare da yi masa sha tara ta arziƙi. Hadiminsa kuwa ta sa aka fille kansa, domin ya yi kisan kai ga ɗan mai ibadar nan. Shi kuma mutumin da ta ‘yanta amma ita ya sayar da ita, ta sa a ɗaure shi a kurkuku saboda cin amana da ya yi.
Allah shi ne Musawwiru! Tabbas, duk wanda ya dogara ga Allah, zai isar masa sharrin duk wani mai sharri!
__________













