• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, July 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Wasanni

UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

WASANNI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 28, 2025
in Wasanni
0
UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

Wace ƙungiya za ta ɗauki kofin zakaru?lxge

18
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Akwai Yiwuwar Spain Za Ta Lashe Kofin Duniya Na Bana

Akwai Yiwuwar Spain Za Ta Lashe Kofin Duniya Na Bana

July 18, 2026
Jiya Lamine Yamal Ya Yi Wasan Kura Da Mbappé

Jiya Lamine Yamal Ya Yi Wasan Kura Da Mbappé

July 15, 2026
Wace ƙungiya za ta ɗauki kofin zakaru?

 

                          __________
Ya zuwa yanzu dai ƙungiyoyi huɗu ne suka fito matakin kusa da na ƙarshe, a Gasar Kofin Zakarun Nahiyar Turai ta bana. Waɗannan kuwa su ne, Paris Saint-Germain (PSG), Arsenal, Inter Milan da kuma Barcelona. A yayin da ƙungiyoyin za su kara a gobe (29) da jibi (30), shin wace ƙungiya ce a cikinsu za ta iya ɗaukar wannan mashahurin kofi a bana?

√ Paris Saint-Germain (PSG):
Kungiyar PSG tana ƙarƙashin jagorancin Luis Enrique kuma ƙungiya ce mai ƙarfi da haɗin kai. Duk kuwa da cewa fitaccen ɗan wasa Kylian Mbappé ya bar ta, sabbin ‘yan wasa kamar Vitinha, Neves, da Pacho sun ƙarfafa ƙungiyar sosai. A wasanninsu na baya-bayan nan, sun lallasa manyan ƙungiyoyi daga Ingila.
A nazari, ƙungiyar PSG tana da daidaito da ƙarfi a kowanne ɓangare. Salonsu na wasa mai burgewa da nuna ƙwarewa ne kuma sun yi dacen ƙwararrun ‘yan wasa. Hakan yana haska su a matakin farko da albishir cewa kofin bana zai iya kasancewa mallakinsu.

√ Arsenal:
A gasar bana, Arsenal ta ba da mamaki sosai ta hanyar fitar da babbar ƙungiya, Real Madrid, wacce take riƙe da kambin tarihin ƙungiyar da ta lashe kofin na Zakarun Turai har sau 15. A bana Arsenal ta yi wajerod da ita, ta lallasa ta da ci 5-1 a jimilla, wanda ya sa suka kai wasan kusa da na karshe karo na farko cikin shekaru 16.

Duk da samun rauni a Gasar Firimiya, ƙungiyar a ƙarƙashin jagorancin Mikel Arteta ta nuna juriya da fasaha a matakin Turai. ‘Yan wasa kamar Bukayo Saka da Gabriel Martinelli, suna taka rawar gani.

√ Inter Milan:
A bana, Inter Milan tana taka leda cikin tsari da tsaro sosai. Sun bari ƙwallo biyu kacal ta shiga ragarsu, a cikin wasanni 10, a gasar ta bana. Ɗan wasa Lautaro Martínez yana taka rawar gani sosai, inda ya zama ɗan wasan farko da ya ci ƙwallo a wasa 5 a jere a gasar ta bana. Tsarinsu da ƙwarewarsu sun sanya su cikin jerin manyan ƙungiyoyin da ke fafatawa a gasar ta bana, inda ake kallon za su iya lashe kofin.

√ Barcelona:
Barcelona mai gayya mai aiki, wacce take ƙarƙashin jagorancin Hansi Flick, ta canza zuwa salo mai sauri da kai farmaki sosai. Ƙungiyar ta ci gaba da lallasa manyan ƙungiyoyi kamar Real Madrid da Bayern Munich. Haziƙan ‘yan wasa kamar Lamine Yamal, Robert Lewandowski da Raphinha sun haɗa kai, sun kai farmaki da cin ƙwallaye sosai a kakar bana. Suna da ƙarfi a kai farmaki, amma ana iya samun ɗan rauni a ɓangaren tsaro.

Daga ƙarshe, cikin waɗannan zaratan ƙungiyoyi huɗu, kowacce na da damar da za ta ɗauki kofin nan, musamman idan suka jajirce amma dai an fi kallon ƙungiyoyin PSG da Bercelona da cewa cikinsu ɗaya za ta ɗau kofin nan.

Jama’a, mene ne ra’ayinku a kan waɗannan ƙungiyoyi huɗu kuma wacce kuke ganin za ta ɗauki kofin nan na bana? Ku bayyana a Comment Section.
______
👇

Previous Post

MENE NE SO?

Next Post

PSG DA ARSENAL: ZARATAN ‘YAN WASAN DA ZA SU BA DA MAMAKI

Related Posts

Akwai Yiwuwar Spain Za Ta Lashe Kofin Duniya Na Bana
Wasanni

Akwai Yiwuwar Spain Za Ta Lashe Kofin Duniya Na Bana

July 18, 2026
Jiya Lamine Yamal Ya Yi Wasan Kura Da Mbappé
Wasanni

Jiya Lamine Yamal Ya Yi Wasan Kura Da Mbappé

July 15, 2026
Kofin Duniya: Gobe Za A Fara Fafata Wasan Gab Da Na Ƙarshe
Wasanni

Kofin Duniya: Gobe Za A Fara Fafata Wasan Gab Da Na Ƙarshe

July 13, 2026
Next Post
PSG DA ARSENAL: ZARATAN ‘YAN WASAN DA ZA SU BA DA MAMAKI

PSG DA ARSENAL: ZARATAN 'YAN WASAN DA ZA SU BA DA MAMAKI

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026

PHOTO GALLERY: Hajia Rabi Attends UNICEF Training

October 27, 2023
I Will Tackle Banditry Head-on – Governor Radda

I Will Tackle Banditry Head-on – Governor Radda

August 24, 2024
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.