• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Dausayin Kauna

MENE NE SO?

DAUSAYIN ƘAUNA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
April 27, 2025
in Dausayin Kauna
0
MENE NE SO?

Mene Ne So?

81
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

MENE NE SO?

 

Related posts

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Shin Wai Akwai So? (1)

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
Mene Ne So?

•••••
So, so, so! Shin wai mene ne so? Shin akwai so ɗin ma, ko kuwa dai tunanin mutane ne kawai yake riya masu batun so a zukatansu? Shin mene ne bambancin so da ƙauna da sha’awa? Waɗannan tambayoyi, har ma da wasunsu za mu duba, tare da yiwuwar amsa su a wannan muƙala. Idan hali ya samu, za mu ɗora da ƙarin bayani tare da sharhi ko tsokaci a kan wannan maudu’i.

Shi dai so wani tsikari ne ko shauƙi mai zurfi da ke shiga cikin ruhin mutum kuma yake samun tasiri sosai a ruhi, har ma ya haifar da wata halayya ta musamman ga mutumin da ya faɗa cikin so. A yayin da wasu kuma suka ce shi so zaɓi ne wanda ke samuwa a zuciyar mutum kuma yana haifar da shaƙuwa da sadaukarwa, kulawa da tattali da kiyayewa da makamantansu.

Haka kuma shi so yana zuwa ne cikin siffofi iri-iri. Akwai so na tarayya, wanda shi ne yake ɗarsuwa saboda sha’awa. Shi ne yake haddasa buƙatar saduwa ko jima’i.

Akwai so na haka nan ba tare da wani dalili ba. Shi irin wannan son yana faruwa ne saboda halayyar ɗan Adam. Haka kawai za ka ga wani ko wata, babu wani dalili sai ka ji kana son ta ko son shi.

Akwai kuma so na dalili. Shi irin wannan son yana sargafuwa ne bisa wani ayyanannen dalili. Misali shi ne so irin na addini ko ƙabila ko saboda wata bajinta ko ƙwarewa a wata sabgar rayuwa, kamar ƙwallon ƙafa da sauran wasanni ko fim da sauransu.

Akwai so na sanayya. Wannan shi ne yake ginuwa saboda sanayya ko nasaba ta jini – ‘yan uwantaka. Wannan shi ne kamar son da ke tsakanin mahaifa da ‘ya’yansu, ɗan uwa da ɗan uwa da sauransu.

Akwai kuma son kai, wanda shi ma nau’in so ne mai zaman kansa. A haka za ka ga wani ko wata da suka siffatu da son kansu fiye da kowa.

So wani irin shu’umin al’amari ne, domin kuwa yana haifar da farin ciki da natsuwa. Yana haifar da ƙalubale a rayuwa, kamar kuma yadda a wasu lokuta yake haifar da ƙunci da matsaloli.
•••••

A rubutu na gaba, za mu duba tambayar da ke cewa, shin akwai SO, ko kuwa dai tunanin mutum ne kawai yake haska batun so a zuciya? Kafin sannan, ku shiga Comment Section ku bayyana ra’ayinku, shin me kuka fahimta game da so?
•••••

Previous Post

A 2027 Talakawan Najeriya Za Su Nuna Wa Tinubu Iyakarsa –  Aminu Waziri

Next Post

UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

Related Posts

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
Dausayin Kauna

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Shin Wai Akwai So? (1)
Dausayin Kauna

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
KANA SON FAHIMTAR MATA?
Dausayin Kauna

KANA SON FAHIMTAR MATA?

November 9, 2023
Next Post
UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

UEFA 2025: WACE ƘUNGIYA CE ZA TA ƊAUKI KOFIN ZAKARU?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

…BUT WHERE IS IFEANYI?

…BUT WHERE IS IFEANYI?

February 26, 2026
YAMTARAWALA Ya Kama Hanyar Lashe Gasar Adabi Ta NLNG

YAMTARAWALA Ya Kama Hanyar Lashe Gasar Adabi Ta NLNG

August 31, 2023
Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

October 27, 2025
Littafin Tunawa Da Ɗanbarno: Ana Gayyatar Marubuta

Littafin Tunawa Da Ɗanbarno: Ana Gayyatar Marubuta

July 3, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.