Kofin Duniya: Gobe Za A Fara Fafata Wasan Gab Da Na Ƙarshe
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Bayan kammala wasan Kusa Da Na Ƙarshe, ƙasashe huɗu ne suka rage a fafatawar wasan Gab Da Na Ƙarshe (Semi Final) domin lashe kambun duniya, wanda za a fara a daren gobe Talata. Ƙasashen kuwa su ne France, Spain, England da Argentina.
Kamar yadda kafar labarai ta AP News ta bayyana, wannan shi ne karo na farko a tarihin gasar da ƙasashe huɗu mafi girman matsayi a jadawalin FIFA suka haɗu a zagayen Gab Da Na Ƙarshe, abin da ya ƙara nuna irin ƙarfinsu da cancantarsu.
A wasan farko a yau, France za ta kara da Spain. Wannan wasa zai kasance gwaji tsakanin ƙungiyar da ke da saurin kai hari da kuma ƙungiyar da ta shahara wajen riƙe ƙwallo.
Ana sa ran Kylian Mbappé da Ousmane Dembélé da Michael Olise za su jagoranci harin France, yayin da Lamine Yamal da Pedri da Nico Williams za su zama manyan makaman Spain. Idan waɗannan taurari suka taka rawar gani, wasan na iya zama ɗaya daga cikin mafi ƙayatarwa a gasar ta bana.
A ɗaya ɓangaren kuma, England za ta fafata da Argentina a wasan da ake ganin zai cika da tarihi da zazzafar hamayya.
Ingila za ta dogara sosai kan Jude Bellingham, wanda ya yi fice a wasan Kusa Da Na Ƙarshe da cin ƙwallaye biyu a wasa ɗaya, tare da Harry Kane da Bukayo Saka.

Argentina kuwa za ta sa rai kan gogewar Lionel Messi da ƙwazon Julián Álvarez da Lautaro Martínez da Alexis Mac Allister. Wannan wasa na iya kasancewa tsakanin ƙwarewa da ƙuruciya, kamar yadda jaridar The Guardian ta bayyana shi.
Dangane da hasashen ƙasar da za ta iya lashe Kofin Duniya na bana, France tana cikin ƙasashen da suka fi jan hankali saboda irin ƙarfin da ta nuna tun daga matakin rukuni har zuwa wasan Kusa Da Na Ƙarshe.
Jaridar The Guardian ta bayyana cewa, harin da Mbappé da Dembélé suke jagoranta ya kasance cikin mafi haɗari a gasar.
Haka kuma masana da dama suna ganin France tana da babbar dama, sai dai kuma Argentina, mai riƙe da kambun duniya, tana da ƙwarewar manyan wasanni, yayin da Spain da England su ma ba za a raina su ba.
A ganina, idan aka yi la’akari da yadda ƙungiyoyin suka taka rawa zuwa yanzu, France ce ke da ɗan ƙarin damar lashe kofin duniya na bana saboda haɗuwar ƙwararrun ‘yan wasa, ƙwarewar mai horarwa da kuma daidaituwar tsaron baya da na gaba.
Amma idan Argentina ta kai wasan ƙarshe, ƙwarewar Messi da abokan wasansa na iya sauya komai, domin manyan wasanni sau da yawa suna buƙatar gogewa fiye da ƙarfi kaɗai.
Abin da ya sa wasan Gab Da Na Ƙarshe na bana ya zama na musamman, shi ne cewa dukkan ƙasashen huɗu sun cancanci kai wa wannan mataki bisa bajintarsu. Kuma babu wata ƙungiya da za a iya cewa ta fi sauran nisa sosai.
Masoya ƙwallon ƙafa na duniya suna sa ran ganin wasanni masu cike da fasaha, dabara da ƙwazo, waɗanda za su tantance waɗanda za su kai wasan ƙarshe da kuma wanda zai lashe Kofin Duniya na FIFA na bana.
Daga ƙarshe, duk wadda ta yi nasara a wasan Gab Da Na Ƙarshe, za ta shiga wasan ƙarshe ne cikin cikakken ƙwarin gwiwa.
Idan manyan taurari kamar Mbappé da Yamal da Bellingham ko Messi suka ci gaba da nuna bajinta, akwai yiwuwar a tuna da wannan zagayen har zuwa wasan ƙarshe, a matsayin ɗaya daga cikin mafi kayatarwa a tarihin gasar Kofin Duniya.
__________













