PSG DA ARSENAL: ZARATAN ‘YAN WASAN DA ZA SU BA DA MAMAKI
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

A wasan kusa da na ƙarshe na cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai (UEFA Champions) da za a fafata a yau, tsakanin ƙungiyar Arsenal da PSG, ga zaratan ‘yan wasan da ake sa zan za su taɓuka abin kirki:
√ Bukayo Saka (Arsenal): Yana ba da gudunmowar ƙwallaye, kamar kuma yadda yake ba da taimako a wasanni sama da 25 a kakar bana kuma ya ƙware sosai wajen kai hare-hare.

√ Martin Ødegaard: Shi ne kyaftin ɗin Arsenal. Yana da tsinkaye da hangen nesa sosai, kamar kuma yadda yake da fasaha wajen raba ƙwallo a tsakiya.

√ Declan Rice: Ɗaya ne daga cikin ginshiƙan masu tsaron tsakiya na Arsenal. Yana taimakawa wajen hana abokan hamayya kai hare-hare da kuma raba ƙwallo daidai.

√ Ousmane Dembélé (PSG: Muhimmin ɗan wasan gaba ne kuma yana yawan taimakawa wajen zura ƙwallo da kuma haddasa matsala ga abokan hamayya a gefen fili.

√ Khvicha Kvaratskhelia: Sabon ɗan wasan PSG ne kuma yana da ƙwarewa da fasaha wajen ƙirƙirar dama da sauya salon wasa domin rikita abokan hamayya.

√ Bradley Barcola (PSG): Yana daga cikin ’yan wasa da suka fiye ba da taimako wajen jefa ƙwallaye a Turai a bana, kuma yana iya karya garkuwar kowace ƙungiya.

_____
Baya ga waɗannan, ko akwai ƙarin ‘yan wasan da kuke ganin za su ba da mamaki a wasan yau? Ku bayyana a Comment Section:
_____
👇













