• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, August 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

MATSALAR TSARO: Saƙo Na Musamman Ga Jigajigan Arewa A Gwamnatin Tinubu

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 5, 2023
in Babban Labari
0
MATSALAR TSARO: Saƙo Na Musamman Ga Jigajigan Arewa A Gwamnatin Tinubu

Arewa Ana Kashe Mu

38
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

MATSALAR TSARO: Saƙo Na Musamman Ga Jigajigan Arewa A Gwamnatin Tinubu

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026

~~~~~~~
Assalamu alaikum. Da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya.

Bayan gaisuwa da girmamawa, wannan saƙo ne na musamman ga Jigajigan Arewa, waɗanda ke riƙe da ragamar TSARO a Gwamnatin Mai Girma Shugaban Ƙasa Alhaji Ahmad Bola Tinubu, wato mai girma Malam Nuhu Ribadu (Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Ta Fuskar Tsaro) da Alhaji Badaru Abubakar (Ministan Tsaro) da Alhaji Bello Matawalle (Ƙaramin Ministan Tsaro).

A yau dai Arewa tana cikin matsalar tsaro mafi muni. A kullum sai an kashe al’umma. A kullum sai an sace mutane. A kullum sai an kassara mutane.

Rahotanni daga Jihar Sakkwato, ba su da daɗin ji ko kaɗan, domin kuwa ‘yan ta’adda sun kafa sansani, a kullum sai ɗaukar mutane suke, suna kashe wasu, suna amsar kuɗin fansa ga wasu. Ko a shekaranjiya, sun shiga Jami’ar Usman Ɗanfodiyo, sun saci kayan abinci kuma sun yi barazana ga rayukan ɗalibai.

A Jihar Zamfara kuwa, abin ya zama sai ‘lahaula walaƙuwwata…’ domin kuwa babu safiya, rana ko daren da ‘yan ta’adda ba su sacewa, kashewa da yi wa mata fyaɗe da cin zarafi. Ko a makon jiya, sai da suka shiga Jami’ar Tarayya ta Gusau, suka sace ɗalibai mata fiye da dozin ɗaya.

A Jihar Katsina ma al’amarin ya zama gagarabadau. Ƙananan hukumomin Faskari, Ɗandume, Sabuwa, Funtuwa, Malumfashi da Ƙafur da Ƙanƙara da Dutsin-ma, kullum suna fuskantar barazanar ‘yan ta’adda. A yanzu maganar da ake Allah ne kaɗai ya san adadin mutanen da ke hannun ‘yan ta’adda.

Ko a asubahin Talatar da ta gabata, ‘yan ta’adda sun shiga gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma, suka sace ɗalibai mata guda biyar.

A sanadiyyar rashin tsaro a Arewa, tattalin arziƙinmu na noma da kiwo da kasuwanci duk sun ɓalɓalce. An kassara harkar ilimi, domin kuwa ɗalibanmu maza da mata suna cikin barazana. Al’amura sun durƙushe.

Ya masu girma shugabannin tsaro, don Allah ku yi abin da ya dace, ku haɗa kan Gwamnonin Arewa da Sarakuna da Malaman Addinai da Manyan Attajirai da dukkan shugabannin Arewa domin tattauna hanyar kawo ƙarshen wannan babbar matsala. Shin haka za ku zuba ido ANA TA KASHE MU?
~
A’A – wajibi ne ku yi abin da ya dace, domin kawo mana ƙarshen wannan fitina. Ku ne idanunmu da kunnuwanmu a wannan gwamnati ta Shugaba TINUBU. Allah Ya ba ku ikon yin abin da ya dace. Amin-summa-Amin!

~~~~~~~
Daga Bashir Yahuza Malumfashi,
Babban Editan Mujallar Taskar Gizago
~~~~~~~

Previous Post

Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Najeriya

Next Post

Related Posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara
Babban Labari

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami
Babban Labari

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026
Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama
Babban Labari

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

July 30, 2026
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

BAKIN JAƁA (3)

BAKIN JAƁA (3)

September 9, 2025
GODIYA DA JINJINA GA BABANA: Bashir Yahuza Malumfashi

GODIYA DA JINJINA GA BABANA: Bashir Yahuza Malumfashi

September 27, 2025
Akwai Yiwuwar Spain Za Ta Lashe Kofin Duniya Na Bana

Akwai Yiwuwar Spain Za Ta Lashe Kofin Duniya Na Bana

July 18, 2026
Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida

Ƙungiyar Marubutan Nahiyar Afirka (PAWA) Ta Buƙaci Marubuta Su Koma Yin Rubutu A Harsunan Gida

March 21, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu
  • Musulunci Ba Addinin Tsauri Ko Sakaci Ba Ne…

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon

August 23, 2026
Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

August 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.