Akwai Yiwuwar Spain Za Ta Lashe Kofin Duniya Na Bana
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
A yau Asabar da gobe Lahadi ake kammala Gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa ta Duniya ta bana. Wace ƙasa ake ganin za ta ɗau na uku, tsakanin England da France kuma wacce ce za ta ɗau kofin na bana, tsakanin Argentina da Spain? Waɗanne ‘yan wasa za su yi abin kirki a filin daga a fafatawar ƙarshe?
A wasan neman matsayi na uku tsakanin England da France, wanda za a buga da daren yau Asabar, ana kyautata zaton ƙasar France tana da ɗan rinjaye kaɗan saboda ƙwarewar ‘yan wasanta a manyan wasanni da kuma ƙarfin tsaron bayanta.
Duk da haka, ƙasar England ma tana da matasa masu saurin kai hari kuma za ta iya ba da mamaki. Hasashen mutane da dama shi ne, France za ta lashe matsayi na uku, inda za ta doke England da tazarar ƙwallo ɗaya.
A babban wasan ƙarshe kuwa tsakanin ƙasar Spain da Argentina, wanda za a fafata a gobe Lahadi, ana hasashen zai kasance wasa mai tsananin ƙayatarwa. Idan Spain ta ci gaba da buga wasan mallakar ƙwallo da taka-tsan-tsan kamar yadda ta riƙa yi a dukkanin gasar, tana da damar lashe kofin. Amma Argentina tana da gogewa da ƙwarin gwiwar manyan ‘yan wasa. A nan, Spain tana da ƙaramin rinjaye. A kan haka, ana hasashen za ta iya lashe kofin na bana amma da ƙyar.
A tarihin Gasar Cin Kofin Duniya, ƙasar Argentina ta taɓa lashe kofin sau uku kafin wannan gasar, wato a shekarun 1978, 1986 da kuma 2022.

Ita kuwa Spain ta taɓa lashe kofin sau ɗaya ne kacal, wato a shekarar 2010, bayan ta doke Netherlands a wasan ƙarshe.
Saboda haka, idan Argentina ta yi nasara a bana, zai zama ta lashe shi a karo na huɗu ke nan. A yayin da idan Spain ce ta yi nasara, zai zama ta lashe shi a karo na biyu ke nan.
A wasan ƙarshe na wannan gasa ta bana, akwai ‘yan wasa da ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa. A ɓangaren Spain, Lamine Yamal, Nico Williams da Pedri, suna iya zama ginshiƙan nasara saboda saurin kai hari da fikira da kaifin basira da ƙirƙira da dubara da kuma iya sarrafa wasa a tsakiyar fili.
A ɓangaren Argentina kuma, Julián Álvarez da Enzo Fernández da Alexis Mac Allister, suna da damar haskawa, ta hanyar ƙirƙirar damammaki da kuma zura ƙwallaye.
Waɗannan sunaye ne na zaratan ‘yan wasan bal, waɗanda ake sa ran za su fi jan hankali, idan suka buga wasa yadda suka saba.
Abin da zai iya raba gardama shi ne, yadda kowace ƙungiya za ta fara wasan. Spain za ta yi ƙoƙarin mallakar ƙwallo da gina kai hare-hare cikin natsuwa. A yayin da Argentina kuma za ta yi amfani da ƙwarewarta wajen kai farmaki cikin sauri da kuma amfani da kuskuren abokan hamayya. Ƙungiyar da ta fi rage kurakurai, ta kuma yi amfani da damar da ta samu, ita ce za ta fi kusantar ɗaga kofin.
Kodayake hasashe ne kawai, ina ganin masu kallo za su shaida ɗaya daga cikin mafi kyawun wasannin ƙarshe na Gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa na Duniya, wanda Hukumar FIFA take shiryawa.
Daga ƙarshe, ana kyautata hasashen cewa ƙasar France za ta ɗauki matsayi na uku, sannan ƙasar Spain ta zama zakarar duniya ta bana; bayan fafatawa mai zafi da Argentina. Duk da haka, a wasan ƙarshe komai na iya faruwa kuma ƙaramin kuskure ko hazaƙar ɗan wasa guda na iya sauya sakamakon gaba ɗaya.
___________













