• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Noma Da Kiwo

NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 22, 2023
in Noma Da Kiwo
0
NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

Alhaji Shehu Musa Ɗankano

138
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

~~~~~~~
Masu iya magana suna yi wa NOMA kirari da “na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zaka duniya kai ya tarar.” Wasu kuma suna ƙarawa da “noma yanke talauci.” Koma dai yaya lamarin yake, Ɗan’iyan Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi, Alhaji Shehu Musa Ɗankano, shaida ne sahihi ga waɗannan batutuwa game da noma, kasancewar shi manomi ne na haƙiƙa, wanda yake gudanar da shi a zamanance – bisa ilimi da fasahar zamani.
~~~~~~~

Related posts

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024
SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

September 17, 2023
Irin dabinon Gonar Musa Ɗankano
Goro da aka noma a Gonar Musa Ɗankano
Yabanyar waken soya a Gonar Musa Ɗankano

Tun a shekarar 1986 ya kafa kamfanin noma mai suna Musa Ɗankano Farms Limited (Kamfanin Gonakin Musa Ɗankano). Kamfanin ya samu rijista daga Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rijista ta Nigeria a shekarar 1992. Gona ce mai faɗin sama da eka 300 da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina. Gona ce ko kamfani mai ƙunshe da ma’aikata masu yawa, waɗanda ke aiki a sassa daban-daban da suka haɗa da noman hatsi, noman kayan marmari, noman ciyayi da ganyaye masu amfani ga ‘yan Adam da dabbobi.

Haka kuma ana kiyon dabbobi da tsuntsaye da kaji da kifi da sauransu. Kamar kuma yadda suke koyar da dubarun noma a aikace ga masu bukata, musamman ta hanyar shirya tarukan bita ga hukumomin noma da makarantu. Gonar na gudanar da cinikayya da kasuwancin kayan gona, wanda haka ke tabbatar da cewa kamfanin yana samar da ayyukan yi da sana’o’i ga al’umma marar adadi, yana samar da abinci, kamar kuma yadda yake damar da kuɗin shiga ga gwamnati.

Noman Fadama:
Babu ko raba ɗaya biyu, kayan marmari da ake samarwa a fadamu, kamar gwaiba, lemu, mangwaro, ayaba da sauransu, suna taimakon jikin ɗan Adam sosai, ta hanyar bunkasa lafiya. Gonar Musa Ɗankano na noma nau’ukan ‘ya’yan itatuwa daban-daban, kamar yadda ya kamata, a sashin fadama mai girman sama da eka 20. Gonar na samar da nau’ukan kayan marmari, kimanin ton 100 a duk shekara, kamar yadda Shugaban Kamfanin Gonar Musa Ɗankano, Alhaji Shehu Musa ya bayyana.

Noman Kayan Lambu Da Ciyayi:
Game da noma kayan lambu da rainon ciyayi a gonar kuwa, Ɗan’iya ya ce: “Muna noma kayan lambu da suka haɗa da kayan iri-iri, ta hanyar amfani da takin gargajiya da muke samu daga kashin dabbobi. Muna amfani da hikimomi da dabarun noman lambu na zamani, ta yadda muke samar da kayan lambu masu ɗandano da inganta lafiyar ɗan Adam, ba tare da gurbata lafiyar ƙasa ba.

“Haka kuma muna nomawa da sayar da ganyaye da kayan miya iri-iri da suka haɗa da gurji, albasa, kabeji, tumatiri, burokuli. Mafi yawan abokan cinikayyarmu sun haɗa da gidajen abinci da ɗaiɗaikun mutane kai tsaye ko kuma ‘yan sari.”

A wani ɓangaren gonar kuwa, an kebe wuri na musamman, inda ake renon itatuwa, fulawoyi da nau’ukan ciyayi iri-iri, musamman waɗanda ake amfani da su wajen ƙawata muhalli. Kamar yadda Shehu Musa ya ce, “Muna aikin kwangilar ƙawata muhalli. Mun samu gaggarumar nasara ta wannan fanni, musamman gonarmu ce ta yi aikin ƙawata muhallai da yawa a Abuja. Waɗannan sun haɗa da harabobin tsoho da sabon ginin Babban Bankin Nigeria (CBN), ɓangaren Shugaban Ƙasa na Filin Jirgin Saman Ƙasa-da-Ƙasa, ginin NNPC, ginin Babbar Kotun Ƙasa, ginin Ma’aikatar Ayyuka da na Ma’aikatar Al’amuran Kasuwanci. Mun yi aiki da manyan kamfanonin gine-gine, kamar Julius Berger, Bouygues da G. Cappa. Saboda ingancin aikinmu, mun samu shaidar yabo da dama. Ɗaya daga cikin irin wannan yabo, shi ne yadda aka karrama ni da Lambar Yabo ta Ƙasa daga Gwamnatin Tarayyar Jamus.”

Noman Dabino:
Allah Ya albarkace Nigeria da ƙasar noma mai kyau. Musamman Arewa na da yanayi mai kyau, wanda ya dace da noman dabino mai yawa, wanda har za a iya fitar da shi zuwa wasu ƙasashen waje. Za a iya noma tan dubu 250 na dabino a duk shekara, kamar yadda STD Media ta tabbatar, a rahotonta na bana. A yadda bincike ya tabbatar, idan za a yi noman dabino da gaske a Arewa, Nigeria za ta iya samar da kashi 70 cikin 100 na dabinon da ake buƙata a dukkan Afirka ta Yamma.

Gonar Musa Ɗankano a yanzu ta duƙufa wajen noman dabino. Ɗan’iyan Galadima ya ce a shekarar 1986 ya fara jaraba noman dabino, ta amfani da irin dabinon gargajiya. Daga baya ya samu wani irin dabino na musamman mai aure, wanda ke yin ‘ya’ya a ɗan takaitaccen lokaci.

A cewar Alhaji Shehu Musa, “Ni mutum ne mai sha’awar itatuwa, don haka a wajajen shekarar 1986, lokacin da na fara gina gidana, sai na dasa dabino irin namu na gargajiya tushe huɗu. Daga baya aka gano cewa tushe biyu ba su yin ‘ya’ya, don haka aka sare su. Tushe ɗaya cikin biyun da suka rage kuma sai Injiniyan da ke aikin ginin ya sare shi. Shi kuma tushe ɗaya da ya rage, sai da ya shekara 30 da dasawa, sannan ya fara yin ‘ya’ya.”

Ya ce wannan al’amari ne ya ƙara masa himma da sha’awar noman dabino. Akalla dai ya karya camfin nan da ake yi, na cewa “duk wanda ya dasa dabino, ba zai rayu ya ci ‘ya’yansa ba.”

Ya ƙara da cewa, “A cikin shekarar 2000 ce na je Jigawa, ina wucewa ta Dutse sai na ga wani allon sanarwa da aka rubuta “Makarantar Binciken Itatuwa (Dabino).” Ni kuma sai na shiga makarantar, inda na gana da wata Farfesa mace, wadda ita ke shugabantar wurin. Na buƙaci in sayi dashen itatuwan dabino masu aure, nau’uka daban-daban amma sai ta sanar da ni cewa gwamnatocin Jihohin Borno da Yobe da Jigawa sun saye su duka. Sai dai ta ba ni kyautar tushe bakwai. Na zo gidana na dasa su.”

Ya ce wadannan tushen dabino mai aure da ya dasa, sai da suka shekara 18, sannan suka fara yin ‘ya’ya, wanda haka ya nuna cewa sun share shekara biyu a matakin reno, kafin a sake dasa su.

Noman Hatsi:
Kasancewar Allah Ya albarkacin garin Malumfashi da ƙasar noma mai kyau, wacce ake noma masara da dawa da waken soya da shinkafa, Gonar Musa Ɗankano ta shafe sama da shekara 30 tana noma nau’ukan hatsi iri-iri. Duk da ƙalubalen tsadar taki da sauran magungunan noma, wakilinmu ya fahimci cewa a bara, gonar ta samar da ton 50 na masara, inda aka riƙa gurbata ton biyu a kowace eka guda. Haka kuma sun girbi ton 40 na waken soya, ton 70 na shinkafa da kuma ton 130 na dawa. Don haka a bana za su fadada noman na hatsi, musamman domin wadata sabon kamfanin samar da abincin kaji na gonar, wanda zai fara aiki nan ba da jimawa ba.

A rahoton da Hukumar Abinci Da Albarkatun Noma Ta Duniya (FAO) ta fitar, ta ce a tsakanin shekarar 2000 da 2005, Nigeria ce kan gaba wajen fuskantar barazanar ƙaratowar hamada a duniya, domin kuwa ita ce mai kaso 55.7 cikin ɗari. Kuma wannan babbar barazana ce ga lafiyar al’umma, domin kuwa hamada na haddasa ɗumamar yanayi, wajen yawaita fitar da sinadarin cabilon dioxide, wanda ke lalata sinadaran da ke kare ‘yan Adam daga cutar hasken rana.

Wani babban al’amari da ke ƙara ta’azzara kwararowar hamada a Arewacin Nigeria, shi ne yadda ake yawan sare itatuwa domin makamashi. Hakan kuma ke ƙara haifar da barazana ga itatuwa masu amfani ga al’umma, waɗanda a kullum suke ƙara ɓacewa.

Saboda kishinsa ga al’umma kuma da sanin amfanin irin waɗannan itatuwa wajen inganta ƙasa, shi ya sanya Shehu Musa ya dasa muhimman itatuwa fiye da nau’uka goma a sassa daban-daban na gonarsa. “Wasu daga cikin irin waɗannan itatuwa, suna samar da magunguna ga ɗan Adam, musamman itatuwan kaɗanya, tsamiya da sauransu,” in ji shi.

A matsayinsa na babban manomi kuma ɗan kasuwar albarkatun gona, Ɗan’iya ya ja hankalin matasa da su shiga harkar noma, domin za ta sama masu ayyukan yi da kuma magance masu matsalolin abinci.

A cewarsa, “Abinci dai dole ne ga ɗan Adam. Irin yadda ake da tsananin buƙatar abinci a duk duniya, ya kamata matasa su koyi dabarun noma, su shigo a dama da su. Kuma ba ka bukatar lallai sai ka mallaki gona, sannan za ka yi harkar noma. Akwai ɓangarori da yawa kuma daban-daban na noma.
~~~~~~~

Previous Post

REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

Next Post

RANAR HAUSA TA DUNIYA

Related Posts

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA
Noma Da Kiwo

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024
SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir
Noma Da Kiwo

SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

September 17, 2023
DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau
Noma Da Kiwo

DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau

September 2, 2023
Next Post
RANAR HAUSA TA DUNIYA

RANAR HAUSA TA DUNIYA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

A Daina Rufa-Rafa Ga Matsalar Ruwa A Sakkwato

A Daina Rufa-Rafa Ga Matsalar Ruwa A Sakkwato

June 7, 2023
Shugaba Tinubu Ya Sauke Shugabannin Rundunonin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Sauke Shugabannin Rundunonin Tsaro

June 19, 2023
GOBARA TA TASHI A KASUWAR MADALLA

GOBARA TA TASHI A KASUWAR MADALLA

January 29, 2024
Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

July 17, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.