DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau
~~~~~~~
A yayin da daminar bana ta fara nisa, Taskar Gizago ta tuntuɓi Malam Idris Ibrahim Kubau (Barden Kubau), manomi a Ƙaramar Hukumar Kubau,
Jihar Kaduna, domin jin hali da yanayin da damina take a yankin nasu. Baya ga cikakken bayani, manomin ya ƙalubalanci matasa, musamman na karkara da su kama harkar noma da gaske, domin neman abin rufin asiri.
~~~~~~~
Yanayin Daminar Bana:
Da farko Alhamdu lillahi, yanayin noman bana musamman a yankinmu na Ƙaramar Hukumar Kubau da ke Jihar Kaduna sai godiya ga Allah. Yankinmu ana noma sosai don a faɗin Jihar Kaduna muna sahun gaba-gaba wajen noma tun daga noman damina har noman rani ba a bar mu a baya ba saboda muna da rafuka.
Daminar ta zo wa talakawa yadda suke so, watau yanayin ruwan sama ba a yi kowane lokaci sosai yadda zai takura wa shuka. Yawan ruwa sosai ta yadda zai riƙa zama a cikin gona, yana kawo wa shuka matsala, musamman amfani irin su masara, wakensoya, wake da makamantansu. Shinkafa ce mai buƙatar ruwa sosai don tana son jin ta a cikin ruwa, musamman ta kaka.
Zan ba da misali da gonata. Gaskiya noman bana mun gode wa Allah. A bara an samu akasi na ruwa sosai, yadda wasu amfanin ruwa ya yi musu yawa fiye da yadda suke buƙata. Gonata ta yi kyau, domin duk abubuwan da na shuka sun yi kyau. Yanayin yadda na yi shukar ya saɓa da yadda nake yi a baya. Rayuwa tana tafiya da zamani, shi ya sa duk shekara muke binciken sabbin dabarun noma kafin ruwa ya sauka.
Wasu suna cewa na cika ƙalƙale-ƙalƙale duk shekara a harkar noma kuma suna ganin canji har su ma yanzu suna koya daga irin dabarun da suka gani a gonata.
Na biyu shi ne, bana na shuka abubuwa guda biyu ne saboda samun zarafin kula sosai da abin da na shuka.
Abubuwan Da Ka Noma?
Abubuwan da na shuka su ne shinkafa ta tudu watau `yar damina da kuma ta kwari watau `yar Kaka. Ita ta tudu ana shuka ta ne a tudu, watau kan ƙasa ba ta fadama ba. Ita kuma ba ta wuce kwanaki100, in sha Allahu take nuna. Tana zuwa cikin damina, domin a cikin watan shida ake shukawa zuwa watan tara ta nuna, sai yankewa.
Kamar tawa shinkafar, na shuka ta a watan shida kuma in sha Allahu a watan tara zan yanke ta. Ke nan tana zuwa kafin ruwa ya ɗauke kuma idan ana son ajiyewa sai an shanya don ta bushe sosai. Wata kuma tana jinkiri zuwa watan goma, lokacin da ruwan sama yake ɗaukewa. Ya danganta da lokacin da manomi ya yi shuka ne.
Ita kuwa ta kaka, kusan sai ruwa ya ɗauke ake yankewa cikin watan goma. Tana buƙatar ruwa sosai, domin da zarar ta fitar da kai tana son jin ta cikin ruwa tsamo-tsamo don samar da ƙwaya.
Sai kuma wakensoya, abu na biyu ke nan da na shuka a bana kamar yadda kuka gani a hoto. Gaskiya yabanya ta samu da shinkafar da wakensoya.
Shi wakensoya nomansa yana da sauƙi fiye da noman sauran amfanin gona saboda yanayin aikinsa. Yanayin yadda na yi shukar bana ya bambanta da yadda ake yi a baya. Na zo da sabon tsari ne, duk da tsarin shukar yana da wahala amma kawai na lokacin shukar ne. Wasu suna ganin wahala muke yi amma da shukar ta fita, an ga tsarin yana da kyau.
Sauƙin noman wakensoya shi ne, ko babu taki zai yi idan Allah Ya so kuma an kula da gyara shi. Yabanyar wakensoya da shinkafa sun yi kyau. Wakensoya yana son shuka kusa-kusa ba kamar yadda wasu suke shuka shi ba, yadda suke shukar masara ko dawa. Ita shinkafa ba a shuka ta kamar hatsi kuma kada a cika takure ta kamar yadda ake yi wa wakensoya.
Ƙalubale A Daminar Bana:
Ana samun wasu yanayi na matsaloli ko ƙalubale. Matsalar da aka fuskanta a noman bana ita ce yadda waɗanda suka yi shuka a farkon ruwa suka yi asara saboda bayan amfanin ya tsira sai ruwa ya ɗauke. Wannan dalilin ya sanya dole bayan ruwa ya juyo, suka sake shuka.
Sai kuma wasu ƙwari da suka riƙa cin iri a gonakin da suka yi shuka, ba tare da wanke irin da magani ba. Sannan a tsakiyar damina, an samu ‘yar ƙamfar ruwa, wadda sanadiyyar haka wasu amfanin da suka riga suka yi girma sosai suka samu matsala, domin lokacin da suke buƙatar ruwa sai Allah da ikonSa ruwan ya ɗan tsahirta. Bayan ruwan ya dawo amfanin ya ci gaba amma wasu ba za su samu amfanin da ya kamata a samu ba saboda wannan tsaikon ya rage wa amfanin aukin da ya kamata a samu.
Wasu kuma sun fuskanci matsalar rashin taki ne. Bayan sun yi shuka ta fita an yi gyara, yabanya ta samu amma yanayin yadda tsadar rayuwa ta zo a wannan lokaci, dole ta sanya ba su da halin sayen takin da za su sanya wa amfanin gona. Sun shirya noman sosai amma tsadar rayuwa ta takura musu, dole amfanin ya samu matsala. Sai kuma musamman a wannan zamani na amfani da magungunan feshi na zamani. Nan ma an samu matsala saboda akwai maha`inta, waɗanda suka yi jabun magani. Mutum ya saya da tsada ya fesa amma bai yi masa amfani ba. Da yawan manoma sun yi asara a wannan ɓangare na feshi saboda rashin ingancin magungunan
Wasu kuma yanayin irin da suka shuka ne ba mai kyau ba. Mutum ya shuka iri mara kyau sai amfanin ya tsira tsilli-tsilli ba ko`ina ba. Dole sai an yi ƙwafi don maye gurbin inda ba su fita ba. Yana da kyau mutane su riƙa tantance iri mai kyau, tun da wuri kafin faɗuwar damina. Mutum ya kasance ya tanadi iri mai inganci. Haka ma maganin feshi, a riƙa saye wuraren da aka san maganinsu yana da kyau.
Duk da waɗannan matsaloli, amfanin gona bana sai sanbarka. Mu Alhamdu lillahi, a yankinmu babu matsalar tsaro wanda wasu wurare suke fama da ita.
Jan Hankali Ga Matasa:
Daga karshe ina bai wa matasa musamman waɗanda suke zama a karkara da su ƙara tashi tsaye su rungumi harkar noma, domin a ciki suka taso saboda an fi sanin karkara da noma. Haƙiƙa ana ƙoƙari sosai, sai dai abin takaici wasu matasa suna zaune a karkara, ga gonaki na noma amma ba su son yin noma. Sun gwammace yin maula, wasu su taso daga birni kullum suna hanya zuwa karkara suna noma don ruafa wa kai asiri. Amma su jira suke yi idan na birni ya zo ya ba su kuɗi, su ba za su tashi su yi wa kansu ba.
Manoma sun samu arziƙi sosai a `yan shekarun da suka gabata zuwa yanzu. A ƙididdigar da Hukumar Alhazai ta fitar a 2017, ta ce kashi 70% na mahajjatan da suka fi biyan kuɗin Hajji, manoma ne daga karkara. Jaridar Daily Times ta ranar 28/4/2017, ta ruwaito cewa kashi 90% na waɗanda suka biya kuɗin aikin Hajji na shekarar 2017, manoma ne daga Jihar Taraba. Ita kuma jaridar Daily Trust ta ranar 4/2/2017, ta bayyana cewa kashi 70% na manoma suka biya kuɗin ajiya zuwa sauke farali a ƙasar Saudiyya.
Ashe wannan abin kwatanci ne da koyi ga matasa, su ƙara zare damtse wajen yin noma.
Idan matashi ba shi da kuɗin taki, sai ya noma abubuwa waɗanda ba su buƙatar taki sosai, watau ko an sanya musu ko ba a sanya ba amfanin zai yi, kamar su farin wake, dankali, dawa, wakensoya, kuɓewa, makani ko gwaza ko walahan, rogo, doya, gyaɗa, rake da sauransu. Waɗannan amfanin gona ko babu taki idan aka gyara su sosai, in sha Allahu za a amfana. Ba hujja ba ce matashi yana zaune a karkara ya ce saboda rashin taki ba zai yi noma ba.
Magidanci matashi idan ya zaɓi ɗaya ko biyu cikin abubuwan da ko babu taki za su yi, idan ya noma sai ya sayar ya sayi masara da shinkafa da sauran abubuwan da yake buƙata na abinci, ya ajiye a riƙa ci a gida har na tsawon lokaci. Wasu wai dole saboda ba za su iya sayen taki ba sai su ɓuge da wannan uzurin, su ƙi yin noma. Wannan ba uzuri ne karɓaɓɓe ba, matuƙar yana da lafiyar da zai iya aiki. Matasa a rungumi harkar noma don kare mutuncin kai da wadata.
Allah Ya sanya wa amfaninmu albarka, Ya ciyar da ƙasarmu da wadataccen abinci da zaman lafiya, domin komai sai da lafiya.~
~~~~~~~
















Alhamdulillahi haƙiƙa daminar bana sai sam barka. Amfani ya yi kyau, muna rokon Allah Ya ƙarawa rayuwa albarka gaba Ya ciyarmu da halal.
Malam Bashir Yahuza Malumfashi ina godiya da wannan ƙoƙari naka da kake yi. Allah Ya kara daukaka da arziƙi da gamawa da duniya lafiya..
Ma sha Allah. Allah Tabbatar da alheri. Ya sa albarka a kasarmu. Allah Ya kare mu daga sharrukan zamani. Amin.
Nice post! You have written useful and practical information. Take a look at my web blog Webemail24 I’m sure you’ll find supplementry information about Website Design you can gain new insights from.