• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 17, 2023
in Babban Labari
1
Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

Injiniya Tukur Hassan Tingilin

105
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

 

Related posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026

Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur

Taskar Gizago ta tattauna da sabon Babban Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, Injiniya Dokta Tukur Tingilin, inda ya bayyana irin babban ƙalubale da matsalolin da ya iske a hukumar da kuma tsare-tsare da matakan da zai ɗauka domin ganin ya samu nasarar shawo kansu:

Allah Ya ba ka ikon zama Babban Darakta na Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, yaya ka iske hukumar bayan ka shiga ofis ka kama aiki?

A matsayina na sabon Babban Darakta na Hukumar Samar Da Ruwa ta Jihar Katsina, na tarar da matsaloli katutu da yawa da suka cunkushe wannan ma’aikata, ta yadda ta koma kamar ma ba ta da wani amfani a faɗin jihar.

Waɗanne irin matsaloli ne ka samu?

Na samu matsalar da ta shafi sinadaran tsarkake ruwa. Akwai kuma rashin issssar wuta mai ƙarfi da ta ke ba manyan tashoshin ruwanmu guda biyar na Jihar Katsina, watau, Ajiwa, Zobe, Funtua, Malumfashi da Jibia da sauran tasoshi, kamar Sabke a Daura da sauransu. To wannan matsala ita ce ta fi ci mana tuwo a ƙwarya. Ita ce ke sa Gwamnatin Jihar Katsina take kashe maƙudan kuɗaɗe domin ganin ta tace ruwan da za a ba al’umma, kasancewar ganin man gas ya yi tsada. Ga shi ita kanta wutar, za ka tarar wani lokaci akwai ta amma ƙarfinta ba ya kai wa inda injinan za su iya ɗauka. Wani lokaci kuma sai ƙarfin nata ya fi adadin da su injinan suke buƙata, kasancewar an yi su don su zama masu ɗaukar wutar kai tsaye (automatic), sai su kashe kansu su ƙi aiki. Kan haka sai ka ga akwai wutar amma ba ta da amfani.

Akwai matsalar wasu wurare inda aka samu ɓatagari suka lalata a Sabke, a Daura ke nan. Da kuma ɓarnar da ruwa da iska ta yi a wasu wuraren kuma ba a gyara ba.

Ta ɓangaren ma’aikata kuma fa, ko akwai abin da ka gano?

Ƙwarai kuwa, akwai ƙarancin ma’aikata da kuma batun horo na ma’aikatan da ke akwai, domin ma’aikatan wucingadi sun ninninka na dindindin. Idan an lura, ma’aikacin wucingadi ba lallai ne ya yi maka abin da kake bukata ba, kasancewar
ya san cewa shi ba cikakken ma’aikaci ba ne.

Waɗannan su ne matsalolin da muka samu amma in sha Allahu za mu tunkare su ɗaya bayan ɗaya domin magance su.

To, ta yaya za ka tunkari magance waɗannan matsaloli, a matsayinka na Shugaba a wannan hukuma?

Misalin matsalar tsadar man gas, ina shigowa ofis, mai girma Gwamna ya umurci mataimakinsa ya ba mu damar tunkarar matsalarmu da ta shafi man na gas, cewa mu tunkari sayen shi kai tsaye. Game da maganar wuta kuwa sai muka zauna da Mataimakin Shugaban Ma’aikata na gidan gwamnati, tare da Hukumar Wutar Lantarki ta Kano, wacce ita ce ke ba mu wutar nan, aka tattauna, aka kafa kwamiti. Don haka daga makon nan za mu fara zagayawa, domin tabbatar cewa mun gano matsalar, an warware ta da gaggawa, domin a taimaki gwamnati wajen rage maƙudan kuɗin da take kashewa wajen sayen man gas.

Ta ɓangaren ma’aikata kuwa, za mu tantance na wucingadi, domin ba gwamna shawara, a duba su domin ganin sun zama ma’aikata na dindindin. Su kuma ma’aikatan da muke da su, za mu ɓullo da hanya ta gaggawa domin ganin cewa mun sake ba su horo domin su samu ƙwarewa da damar yin gogayya wajen aiki na zamani.

Ta ɓangaren al’ummar Jihar Katsina, ko wane haɗin kai kake buƙata daga gare su?

Daga ɓangaren al’ummar Jihar Katsina kuwa, haɗin kai da muke nema daga gare su shi ne, su sani cewa ita wannan ma’aikata ta dogara ne daga kuɗaɗen da suke biyan ta, a dalilin ruwan da suka sha, domin biyan albashi da gudanar da harkokinta na yau da kullum. Don haka muna kira ga jama’a da su yi la’akari da canjin da aka samu, yadda ake kawo ruwa a yanzu haka. Don haka su maida wa gwamnati karimcin da ta yi masu, su riƙa biyan kuɗin ruwa a kan lokaci. Abu na biyu kuma shi ne, ruwan nan in Allah Ya yarda zai inganta, a ci gaba da bayar da shi, kamar yadda mutane suke ganin shi a kai-a kai. Ina kira ga waɗanda ba su da kan famfo da su yi azama su je ofishin hukumar ruwa a inda suke domin yin rijista, domin su ma su riƙa amfana daga wannan tagomashi na Gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa dangane da ruwan sha.

Game da kayan hukumar kuma, waɗanda ake lalatawa da ɓarnatawa a wasu wurare, muna kira ga al’ummar Jihar Katsina da su taimaki wannan hukuma, domin tabbatar da cewa, duk inda aka ga irin wannan ɓarna ko kan famfo ya karye yana zubar da ruwa, su yi gaggawar sanar da ita. Inda kan fanfunan suke tsaye kuwa, a taimaka a sa ido a hana yara da suke ɓarna da kuma ɓarayin fanfunan nan, ‘yan bolabola ke nan, domin kuwa dukkan waɗannan abubuwa na su ne kuma domin jin daɗin su ne gwamnati ta samar da su. Ke nan sai mu ma mun maida hankali wajen kare su. Muna ba da albishir cewa in sha Allahu wannan ci gaba zai ɗore domin amfanin kowa.

Previous Post

A Mako Ɗaya Kacal: Jami’an NDLEA Sun Yi Wawan Kamun Muggan Ƙwayoyi A Abuja, Lagos Da Sassan Nigeria

Next Post

Shekara 30 A Inuwar Aure: Fatan Alheri Ga Editan Rfi Hausa

Related Posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna
Babban Labari

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin
Babban Labari

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci
Babban Labari

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Next Post
Shekara 30 A Inuwar Aure: Fatan Alheri Ga Editan Rfi Hausa

Shekara 30 A Inuwar Aure: Fatan Alheri Ga Editan Rfi Hausa

Comments 1

  1. pwwkbqtqoj says:
    2 years ago

    Za Mu Tunkari Matsalolin Ruwa Da Gaske A Jihar Katsina – Injiniya Tukur – Taskar Gizago
    apwwkbqtqoj
    [url=http://www.g62mvgb5a6xo7p457z2n067c493spga3s.org/]upwwkbqtqoj[/url]
    pwwkbqtqoj http://www.g62mvgb5a6xo7p457z2n067c493spga3s.org/

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

An Kammala Jana’izar Shugaba Buhari Cikin Jimami Da Alhini

An Kammala Jana’izar Shugaba Buhari Cikin Jimami Da Alhini

July 16, 2025
Janar Magashi Bai Mutu Ba

Janar Magashi Bai Mutu Ba

June 24, 2023
Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Nijeriya Ta Ba Amurka Tabbacin Ci Gaba Da Riƙo Da ‘Yancin ‘Yan Jarida

November 27, 2023
ALLAH YA JI ƘAN HAUWA ƘAMSHI

ALLAH YA JI ƘAN HAUWA ƘAMSHI

October 2, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.