• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sharhi

A Daina Rufa-Rafa Ga Matsalar Ruwa A Sakkwato

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 7, 2023
in Sharhi
0
A Daina Rufa-Rafa Ga Matsalar Ruwa A Sakkwato
175
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Yusuf Dingyaɗi, Sakkwato

Muddin aka ci gaba da rufa-rufa, ba a ɗauki shawara masana aikin sanin makama a kan samar da ruwan sha b a Sakkwato, to tabbata, har yanzu akwai matsaloli tattare da samar da ruwan issashe ga al’umma.

Related posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024

Rashin ɗaukar shawarwarin da tsoffafin kwamishinonin ruwa suka bayar, mussaman irin su Hon UMAR BATURE don sake fasalta aikin gidan samar da ruwa da farfaɗo da tsarin gyara da inganta bututun ruwa na gidan ruwan Sakkwato da maido da darajar ma’aikatan gidan ruwa na Sakkwato; tabbata duk wani gyara na yanzu tamkar wucin gadi ne.

Daga cikin tsarinsa har da neman gwamnati ta gina ƙananan tashoshin samar da ruwan sha a cikin manyan unguwani, waɗanda za su samar da ruwa daga manyan bore-hole bore-hole da za a gina irin na zamani don aikawa ga unguwanin da ke da nisa da gidan ruwa ko tashoshinsu.

Haka ma akwai ƙara kuɗaɗen tallafi na mussaman kai tsaye daga ofishin gwamna zuwa hukumar samar da ruwan sha ta jiha da gina ƙananan rijiyoyin burtsatse g al’umma.

Haka ma akwai matakin hukunci ga waɗanda suka gina reservoir na tara ruwa a gidajensu, don tasu biyan buƙata, inda suka hana talakawa samun issasun ruwan da ake turawa na fanfo daga tashoshin samar da ruwan na Old Market, Ali Aƙilu, Tasha Illela da Runjin Sambo.

Kwamishinonin ruwa Hon. Bature da Hon. Yabo duk sun mayar da hankali kacokan ga bin tsarin hanyoyin bunƙasa samar da ruwa da aiki kafaɗa-kafaɗa da ƙwararrun ma’aikatan gidan ruwa da suka yi wa Water Board aiki a baya, don samun shawarar bunƙasa wannan aikin na samar da ruwan sha a Sakkwato cikin ɗan lokaci.

Daga galan miliyan biyu zuwa huɗu yanzu ana buƙatar fiye da galan miliyan goma don amfanar da jama’a; sai kuma buƙatar bunƙasa aikin gidan ruwa na Asari, wanda tun farko ake zargin Gwamnatin Wamakko ta yi coge gare sa, da sake faɗaɗa gidan ruwa na Runjin Sambo. Waɗannan duk muhimman ayyuka ne da ke da tasiri ga samar da ruwan sha ga al’ummarmu.

Ya dace Hukumar Samar da Ruwan Sha ta dawo da karɓar kuɗaɗen ruwa ta amfani da hanyoyin zamani, a maimakon dogara ga kuɗin shiga daga ma’aikatan gwamnati da kamfanoni kaɗai.

Yana da kyau kamin Gwamna ya naɗa Kwamishina da zai kula da ma’aikatan ruwa, ya yi garambawul baki ɗaya ga Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Sakkwato, ya sake fasalta aikinta, ya ɗauko masu ‘Contract ‘ tsoffafin ma’aikatan da suka yi hoɓɓasa a baya, don ganin sun maido da darajar hanyoyin inganta samar da ruwan sha a birni da ƙauyuka.

Haka ma a rushe gine-gine da aka yi a kan manyan bututun da ke kai ruwan sha a cikin gari da sake sabunta wasu daga ciki da tsufa ya hana su aiki.

Tsarin nan na Hon. Umar Bature da Injiniya Shehu Mafara, su ne muhimman hanyoyin da za su ceto Jihar Sakkwato daga ci gaba da fuskantar barazanar ƙarancin ruwan sha a Sakkwato.

A yanzu da lamarin ɗumamar yanayi ke ƙara ta’azzara ga duniya baki ɗaya, lokaci ya yi da za mu aje mummunar fahimta ta ɗora laifi ga gwamnati ita kaɗai, a kan abin da ya shafi ƙarancin ruwan sha, don kuwa yanzu ya zama darasi a kan waɗanda suke zargin Gwamnatin Tambuwal da zama dalilin haka.

Zancen biyan kuɗaɗen bashi na NEPA, wannan duk buge ce. Muhimmin abin da ya dace, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta gaya wa al’umma gaskiya a kan matsalolin da ke tattare da aikin samar da ruwan sha da rarraba shi.

Matsalar yanayi da rashin isasshen ruwa daga ainihin gulaben da ke kawo ruwan kamin tace shi; tsadar kayan gyara da ƙarancin kuɗaɗen tallafi na aiki ga Hukumar Samar da Ruwa da sauransu na daga cikin ababen da ya dace a yi wa jama’a bayani dalla-dalla.

Su kansu al’umma suna da nasu laifi a kan rashin biyan kuɗaɗen ruwa da na tallafi da ake nema, wasa da ruwan sha da yin ko oho ga gyaran bututu a unguwanninsu da sauran matsalolin da ke barazana ga samun ruwan sha.

Allah Ya kawo MAFITA

Malam Yusuf Dingyaɗi Sakkwato, shi ne Mashawarci ga tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Waziri Tambuwal

Previous Post

Rusau A Kano: An Fara Kama Ɓarayin Kayan Mutane

Next Post

Ɓarawo Ya Sakar Masa Mata

Related Posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)
Sharhi

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi
Sharhi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024
SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi
Sharhi

SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi

November 16, 2023
Next Post
Ɓarawo Ya Sakar Masa Mata

Ɓarawo Ya Sakar Masa Mata

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Hotunan Mako

Hotunan Mako

May 29, 2023
Horror and Terror

Horror and Terror

September 4, 2024
SASSANYAN AMINCI (2)

SASSANYAN AMINCI (2)

September 5, 2025
SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

SUBHANALLAHI: ‘Yan Sanda Sun Kulle Danladi Haruna

October 7, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.