• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sharhi

REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

SHARHIN LITTAFI

Regina Ogechukwu Nwangele by Regina Ogechukwu Nwangele
August 21, 2023
in Sharhi
0
REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

Littafin Girl-Child Education in Biu

45
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

REGINA OGECHUKWU: Abubuwan Da Na Fahimta Daga Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate

Marubuci Dr. Bukar Usman, OON

 

Littafin Girl-Child Education in Biu

~~~~~~~
Sunan Littafi: Girl-Child Education in Biu Emirate (The Early Years)
Sunan Marubuci: Dr. Bukar Usman, OON
Kamfanin Wallafa: Klamidas Communication Ltd. Abuja
Shekarar Wallafa: 2014
Yawan Shafukan: 136
Mai Sharhi: Regina Ogechukwu Nwangele
Lambar ISBN: 978-978-52655-9-0
~~~~~~~

Related posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024

Littafin Girl-Child Education in Biu Emirate (The Early Years), littafi ne da ke ƙunshe da bincike da nazari da sharhi iri-iri, dangane da tarihi, gwagwarmaya da faɗi-tashin da mata suka sha domin samun ilimin zamani, musamman a tsakanin shekarun 1930 zuwa 1950. Kodayake bayanan sun taƙaita ga matan Masarautar Biu da ke Jihar Borno, amma misalai da darussan da aka tattauna za su iya shafar ko’ina a duniyar baƙar fata, ba ma Arewacin Nigeria kaɗai ba.

Littafin ya yi bayanin irin gwagwarmayar da matan suka yi na yaƙi da wariyar jinsi, yaƙi da ko’in kula daga iyaye, dangane da ilimin ‘ya’ya mata da yaƙi da auren wuri, wanda ke takura su, su gaza samun ilimin zamani, kamar takwarorinsu mata.

Ya kuma samar da faffaɗan bayanin yadda matan suka jajirce, suka fuskanci kowane ƙalubale, har sai da suka samu nasarar kasancewa mata na sahun farko da suka samu ilimin zamani a cikin al’ummarsu. Suka samu nasarar zama abin kwatance da misali, wajen kawo canji da ci gaba na alheri a yankunansu. Wasu daga cikin irin waɗannan matan, sun riƙa jure wa tafiya a ƙasa, sukan share tafiyar Kilomita 24 a ƙasa, a duk lokacin da aka yi masu hutu, domin zuwa gida daga makaranta. Sannan kuma idan lokacin komawa makarantar ya yi, haka dai za su taka a ƙasa. Akwai ma labarin wata yarinya daga cikinsu, ‘yar shekara 8, wacce ta abauce wa ra’ayin iyayenta, ta kai kanta makaranta.

Babban dalilin rubuta wannan littafi ya ta’allaƙa ne da irin kishin da Dokta Bukar Usman yake da shi, na ganin cewa mata sun samu ingantaccen ilimin da ya dace da su. Dalili ke nan ma ya samu shaidar kai tsaye daga bakunan wasu daga cikin matan da har yanzu suke raye, inda suka bayyana irin nasarorin da suka samu a rayuwa, biyo bayan ilimin da suka samu. Wannan ke ƙara tabbatar da cewa, lallai babu abin da ya kai ilimantar da mata ƙima, musamman wajen yaƙi da jahilci, yaƙi da talauci kuma domin samar da al’umma mai wayewa, mai arziƙi, mai lafiya da zaman lafiya.

Regina Ogechukwu Nwangele, ɗaliba ce da ba ta daɗe da kammala karatu a Jami’ar Nsukka a farkon shekarar nan ba. Ta samu digirinta na farko a fannin Ilimin Zamantakewar Ɗan Adam da kuma Nazarin Rayuwa da Al’adu. A yanzu haka tana zaune a garin Aba na Jihar Abiya. Ta samu zarafin karantawa tare da nazarin wannan littafi na Girl-Child Education in Biu kuma ya ɗauki hankalinta matuƙa. Dalili ke nan ma ta rubuta taƙaitaccen sharhi dangane da abubuwan da ta fahimta daga gare shi kuma ta aiko wa marubucinsa.

Da gaisuwa ta buɗe sharhin nata, inda ta ce: “Barka da wannan lokaci Dokta, da fatan ka shiga sabon wata cikin ƙoshin lafiya. A yanzu haka ina kan hanya daga Jihar Taraba zuwa Kudu Maso Gabas, kasancewar mun kammala Share Fagen Hidimar Ƙasa (NYSC), a ranar Talata da ta gabata.

“Na yi katarin karance littafinka mai taken Girl-Child Education in Biu Emirate: The Early Years, a yayin da nake kan tafiya zuwa gida. Babu shakka wannan littafi ƙayatacce ne, gwanin daɗin karantawa. Sai dai ni a nazarin da na yi kuma a ra’ayina, sunan Viyu ya fi kyau kuma ya fi daɗin faɗa, idan aka kwatanta da Biu.

“Wannan littafin ya fayyace girma da ƙimar Masarautar Biu. Babu shakka ingantattu kuma sahihan bayanan da aka fayyace a littafin gamsassu ne kuma na yaba matuƙa da aikin. An yi namijin ƙoƙari wajen tattaro sahihan bayanai, kai tsaye daga matan da suka fara samun ilimin zamani a Biu da ma wajen Jihar Borno. Haka kuma an bayyana irin ƙoƙari da jajircewar da matan suka yi, a hanyarsu ta neman ilimi.

“Haka kuma, wani abin da na fahimta shi ne, har a rayuwarmu ta yau, ana samun wannan yanayi na nuna ƙyama da bambanci ga karatun mata, a yankunan karkara. Sai dai kuma matsalar ta fi ƙamari ga yara maza da mata, a inda aka samu gwamnati da iyayen da ke nuna halin ko’in kula da ilimi.

“A cikin jaruman matan nan 21 da aka baje kolin bayanansu a littafin nan, hankalina ya fi ɗaukuwa ga waɗannan jajirtattun. Su ne Hadiza Shettima Pindar da Caca Betara Garga Biu da Sindiwa Tasiwa da kuma Jummai Diggira. Gaba ɗayan matan 21 sun jajirce, sun sanya himma domin neman ilimi, duk kuwa da irin ƙalubalen da al’ummarsu suka gindaya masu.

“Ya zama wajibi in jinjina maka kuma in yi maka godiya, bisa himma da ƙoƙarinka na ganin mata sun samu ilimi. Haka kuma da irin yadda ka gano irin ƙima da mutuncin matan Biu da ma na Nigeria baki ɗaya. Ina roƙon Allah Mai Girma da Ɗaukaka Ya ci gaba da sanya wa kyakkyawar zuciyarka albarka, Ya ƙara maka hikima da basira da ingantattar lafiyar zuciya da ta jiki. Na gode matuƙar gaske da karimcinka, da ka ba ni kyautar wadannan littattafai naka.

“Ni ce mai yi maka fatan alheri. – Regina Ogechukwu Nwangele.”

Game da marubucin kuwa, Dokta Bukar Usman, D.Litt, M.IoD, OON, an haife shi a garin Biu, Jihar Borno a ranar 10 ga watan Disamba, 1942. Ya yi karatun zamani tun daga Firamare har zuwa Digiri a fannin tafiyar da gwamnati da hulɗa da ƙasashen waje, a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ya yi aikin gwamnati tun daga ƙaramin ma’aikaci daga 1965, har ya kai muƙamin Babban-Sakare a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya kammala aiki a shekarar 1999. Ya rubuta littattafai sama da guda 40 a fagagen ilimi daban-daban. Shi ne Shugaban Gidauniyar Bukar Usman, wacce ya kafa domin jin ƙan raunana, bunƙasa ilimi da sauransu. Haka kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Nazarin Al’adun Gargajiya ta Najeriya (NFS).

~~~~~~~

Previous Post

KAMUN LADUYIN JEMAGE (19-08-2023)

Next Post

NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

Related Posts

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)
Sharhi

SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA: ZUWAN KA TA’AZIYYAR BUHARI KOYI NE DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW)

July 18, 2025
Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi
Sharhi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024
SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi
Sharhi

SAI AN YI DA GASKE: Littafin Wasan Kwaikwayo A Mizanin Nazari Da Sharhi

November 16, 2023
Next Post
NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

November 24, 2025
Army, other operatives bust criminal conclaves

Army, other operatives bust criminal conclaves

September 9, 2023
Marubutan Hausa Na Buƙatar Haɗin Kai – Zakariyya Haruna

Marubutan Hausa Na Buƙatar Haɗin Kai – Zakariyya Haruna

June 30, 2023
Neman Hanyar Gaskiya A Addini

Neman Hanyar Gaskiya A Addini

October 17, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.