• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 15, 2023
in Babban Labari
1
Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

Malam Muhammad Aminu Kabir

47
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

Muhammad Aminu Kabir, a yayin taron Katsina Facebook Connect

 

Related posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026

~~~~~~~
MAK mutum ne mai himma da ƙoƙarin yi wa al’umma hidima. Baya ga fashin baƙi da faɗakarwa da yake kullum a soshalmediya, ya kuma kasance jagoran nema wa marasa ƙarfi tallafi. Taskar Gizago ta tattauna da shi game da rayuwarsa, taron zumunci na Katsina Facebook Connect da kuma al’amuran da suka shafi yanayin matsi da al’umma ke ciki a Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
~~~~~~~

TG: Za mu fara da tarihinka a taƙaice. Shin wane ne MAK?

MAK: Alhamdu lillah. MAK na nufini Muhammad Aminu Kabir. An haife ni a Jihar Katsina cikin Ƙaramar Hukumar Katsina, a shekarar 1982, a Unguwar Sararin Tsako da ke birnin Katsina. Kamar kowane yaro, bayan shekarun haihuwa da na yaye, an sanya ni makarantar koyon karatun Alƙur’ani mai girma da kuma makarantar firamare, a wajen shekarar 1987 zuwa 1988. Daga nan na wuce zuwa Kwalejin Horon Malamai ta Katsina (KTC), wadda daga baya ta koma Katsina College Katsina. Bayan kammala karatuna a cikin shekarar 2001, sai na samu gurbin karatu a Makarantar Koyon Aikin Jinya da ke Kankia, inda na koyo Kimiyya da Fasahar Gwajegwajen Lafiyar ɗan Adama. Daga nan na yi aiki a Babban Asibitin Jihar Katsina na wani lokaci.

A cikin Shekarar 2007 na bar Jihar Katsina zuwa Abuja, inda na yi aiki da wani kamfanin da suke da ƙwarewa a fannoni daban-daban da suka haɗa da sayar da kayan asibiti da kuma ɓangaren ginegine, fasahar kwamfuta da sauransu. Na yi aiki da su na tsawon shekara 10, su ma na bar su bayan na samu aiki da Ma’aikatar Shari’a ta Najeriya. A halin yanzu nan nake aiki. Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihina.

TG: Kana ɗaya daga cikin marubuta masu fashin baƙi kan al’amuran yau da kullum, musamman a Soshiyalmidiya. Tun yaushe ka fara rubuce-rubuce kuma me ya ja ra’ayinka ga haka?

MAK: Eh, inavdai ɗaya daga cikin masu karambani (dariya). To a halin gaskiya dai na fara amfani da wannan kafar ce tun wajen shekarar 2007, lokacin ina aiki a wani kamfani, akwai wani matashi ɗan ƙasar Isra’ila da yake yawan amfani da soshalmediya, yana gaisawa da iyalinsa, da ke can ƙasarsu. Shi ne na fara sha’awar ni ma in mallaki shafina na kaina, wanda daga nan ne na fara rubuce-rubuce. A wancen lokacin ma sai ka yi rubutu ka ga bai fi mutum goma ko ƙasa da haka ba ne za su kula ka; har ta kai ga yanzu za ka yi rubutu har ya ja hankalin jama’a da yawa.

Lallai wannan wani abu ne da nake yi saboda samar da nishaɗi tare kuma da samar da bayanai ga al’umma, domin ta sanadiyyar yin hakan an samu haɗuwa da mutane daban-daban, an kuma sadar da zumunci, Alhamdu lillah. Wannan kafar ta yi sanadiyyar abubuwan alheri da daman gaske, waɗanda lallai ni ba zan Iya misaltawa ba.

TG: Kana jagorantar wata cibiya da ke tallafa wa marasa galihu. Wane ƙalubale kake fuskanta a wannan al’amari?

MAK: Wato shi wannan wani al’amari ne daga Allah. Haka kawai na fara abun kamar da wasa, zan iya cewa wajen shekarar 2012. Wani bawan Allah ne ya kawo mani ƙorafin cewa wata ƙanwarsa ta haifi wata yarinya tana da wani tarin tsokar nama a kanta, lamarin da ya sanya har mijinta ya nemi ya sake ta a kan wannan lamarin. Daga nan ne ni kuma na yi amfani da shafina na Facebook na nema masu taimakon jama’a, aka samu kuɗin da aka yi masu aiki kuma yarinyar ta samu lafiya ta warke. Alhamdu lillah, to fa daga nan abun ya fara har kawo inda ake yanzu. An samu nasarori sosai da ƙalubale kalakala yayin gudanar da wannan aikin.

Ƙalubale da ake fuskanta suna da yawa, kasancewar abu ne ake yi a soshalmediya. Akwai wasu mutane masu satar fasaha da kai kana ƙoƙarin ka nema wa mutane taimakon jama’a, su kuma suna ɗaukar rubutun su sauya bayanai su yaɗa kuma a riƙa tura masu kuɗaɗe. Wannan ba ƙaramin ƙalubale ba ne.

Sai kuma ƙalubale na rashin kuɗi, domin duk abin da za ka gudanar idan babu kuɗi ba zai yi yu ba. Amma Alhamdu lillah, ina matuƙar alfahari tare da godiya ga ɗaukacin mutanen da suke taimakawa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, kuma Alhamdu lillah, yanayin yadda nake gudanar da tsarin ne yavsa mutanen suke da tabbas a kaina har suke ba da gudunmuwarsu kuma na gode ƙwarai da gaske da irin amincin da suke da shi a kaina.

TG: Ka jagoranci gabatar da taron zumunci na Katsina Facebook Connect har sau uku, cikin nasara. Ta yaya ka faro wannan al’amari?

MAK: To shi wannan al’amari sa kai ne kawai. Duk abin da ka sa kanka kuma ka yarda da abin da kake yi mai kyau ne, to Allah zai taimaka maka ka gudanar da shi cikin nasara. Alhamdu lillah, wannan al’amari ne daga Allah, domin ni dai na san cewa dukkanin nasarorin da muke samu daga gare Shi ne. Shirya taro irin wannan mai ƙunshe da mutane daban-daban dole akwai ƙalubale da yawan gaske. Alhamdu lillah, Allah Ya taimaka mana tun daga karin farko har zuwa yanzu muna samun nasara. Akwai abokanin da muke gudanar da wannan taron tare da su suna matuƙar bavda gagarumar gudunmuwa wajen gudanar da wannan taron, tun daga lokacinsu da aljihunsu da sauransu. Ba zan iya bayyana irin gudunmuwar da suke bayarwa ba wajen ganin an yi nasara wajen gudanar da wannan taron, domin mafi akasari kuɗaɗen da ake samu na rajistar mahalarta taron ba su isar mu ko kama ɗakin taron mu yi da su, balle kuma abincin da ake samarwa da abin sha da sauransu.

Yana daga cikin ƙalubale da muke fuskanta wurin mutanen da suke kallon abin daga waje, gani suke kamar wasu kuɗaɗe muke samu da taron amma abin ba haka yake ba. Kusan duk lokacin da muka yi taron nan muka kammala, sai mun kwana da bashi, saboda kuɗin da muke amsa ba su taka kara sun karya ba amma duk da haka mun gode Allah, domin muna yin taron lafiya mu tashi lafiya kuma ba mu taɓa kai wa kowa kukanmu ba. Alhamdu lillah.

TG: Ga shi ana shirin gudanar da taron karo na 4, ko za ka ƙara mana bayani kan abin da ake ciki?

MAK: Alhamdu lillah, gaskiya ne an buɗe ƙofar fara sayar da tikitin shiga wannan taron karo na huɗu, a ranar ɗaya ga watan Augustan nan kuma Alhamdu lillah, mutane yanzu haka suna ci gaba da yin rajista domin halartar taron. Dama dai mukan ɗauki tsawon lokaci muna shirye-shirye domin samar da taro mai inganci, wanda duk wanda ya halarta zai ji nishaɗi da jin daɗin halartar taron.

Ana yin rajista ne a kan Naira dubu ukku kacal ga kowane mahalarcin taron. An ba mu shawarar mu ƙara kuɗin rajistar amma dai duba da yanayin da ake ciki ya sa muka ce ba za mu ƙara kuɗin rajistar ba, domin a bai wa al’umma damar samun halartar taron.

TG::Me za ka ce game da shirya Arewa Facebook Connect?

MAK: Wato wannan wani yunƙuri ne mai kyau, wanda wasu matasa su ma suke ƙoƙarin assasawa, domin ƙara samun haɗin kai, musamman ma a Arewacin Najeriya, ganin cewa a sauran sassan ƙasar nan akwai ƙungiyoyin matasa da suke da faɗa a ji amma mu a nan Arewa kusan kawuna a rarrabe suke. Kowa ya yi gabansa. Samun wata ƙungiya mai kauri irin wannan, wadda zavta iya haɗa kan mutane a wuri ɗaya, zai taimaka ƙwarai da gaske.

TG: Me za ka ce game da halin ƙunci da ake ciki a Najeriya?

MAK: To wannan al’amari ne wanda kusan ya shafi ko’ina da ko’ina a duniya, amma dai mu a wannan yanki namu abin ba ya rasa nasaba da rashin kula da fitar da haƙƙin Allah a cikin dukiyoyin da al’umma suke da shi. Sau da yawa za ka tarar da cewa mutane ba su son fitar da Zakka. Mai ƙaramin jari gani yake kuɗinsa ba su isa ya fitar da Zakka ba, don haka jira yake sai ya tara wasu maƙudan kuɗaɗe kafin ya fitar, alhalin kuma ba haka abin yake ba.

Babu tausayi a tsakanin al’umma, gaskiya tana neman ta yi ƙaranci. Mutane yanzu babu aminci kusan kowa ta kansa yake, babu taimakekeniya a tsakanin al’umma, ba kamar a baya ba wanda za ka ga ana musayar abinci a tsakanin maƙwabta ko kuma masu gidaje suna fito da abinci a ƙofar gida suna ci, har ma wani ya samu shi ma ya ci wanda bai da shi.

TG: Ko kana da wasu shawarwari ga matasa, a wannan zamani?

MAK: Shawarata ga matasaita ce, su dage su nemi ilimin addini da na zamani. Ilimin yana da matuƙar amfani a rayuwa ta kowane ɓangare, domin shi ne zai zama fitilar rayuwa. Duk mai Ilimi kowane iri ne za ka ga tsarin rayuwarsa ya sha bamban da wanda ba ya da ilimi. Sannan matasa su dage wajen neman na kansu a kodayaushe, su riƙa duba da abubuwan da suke faruwa a cikin rayuwar al’umma na yau da kullum. Za su samu darasin rayuwa.
~~~~~~~

Previous Post

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Next Post

PDP Ta Naɗa Yusuf Dingyaɗi Sabon Muƙami

Related Posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna
Babban Labari

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin
Babban Labari

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci
Babban Labari

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Next Post
PDP Ta Naɗa Yusuf Dingyaɗi Sabon Muƙami

PDP Ta Naɗa Yusuf Dingyaɗi Sabon Muƙami

Comments 1

  1. Audu shehu says:
    7 months ago

    Gaskiya mungode sosai Malam mak nima ynz haka ina fama da matsalar rashin sana a

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TASKAR GIZAGO NA TARE DA AHMAD MUSA

TASKAR GIZAGO NA TARE DA AHMAD MUSA

September 27, 2023

Bakan Gizo

August 27, 2023
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
PDP Ta Naɗa Yusuf Dingyaɗi Sabon Muƙami

PDP Ta Naɗa Yusuf Dingyaɗi Sabon Muƙami

August 15, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.