• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Shanshani

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Mukhtar Mudi Sipikin by Mukhtar Mudi Sipikin
August 13, 2023
in Shanshani
0
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Kamun Ludayin Jemage

51
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

Daga Mukhtar Mudi Sipikin

Related posts

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

December 22, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023

~~~~~~~
A yau SHANSHANI ya kamu da mura, dalili ke nan ya makara, bai kai ziyara gidan Malam Na Fagge ba da wuri. Don haka koda ya isa, ba tare da ɓata lokaci ba aka miƙo masa ambulon mai ɗauke da Shaguɓen KAMUN LUDAYIN JEMAGE na wannan makon. Ga abin da yake cewa:
~~~~~~~

Kurciya ta yi tagumi ta yi jugum tana tunani. Ga ƙwalla na zuba. Kowa ya kalle ta ya san tana cikin mayuwacin hali.

Tattabara cikin damuwa ta ce: “Kurciya lafiya dai? Irin wannan tagumi haka har da ƙwalla; wani abu ne ya faru?”

Kurciya ta ja dogon numfashi game da ajiyar zuciya sannan ta amsa da cewa: “Ƴar uwa meye ma bai faru ba? Kullum shugabannin Dajin nan cikin ƙoƙarin jefa mu wani hali suke da sunan gyara. Ɗazu na je sheƙar Duba Lafiya, abin da na gani ya ba ni tsoro. Na ga marasa lafiya birjik amma ba mai duba su. Wai Tsuntsaye masu duba lafiya ne suka tafi yajin aiki.”

Bainu wadda ke can gefe amma tana jiyo abin da su Kurciya ke cewa, ta kada baki ta ce: “Kawuna jiya ya cika saboda ba mai duba shi. Allah Ya ji ƙan shi.”

Sauran tsuntsaye suka amsa da “Amin!”

Waje ya yi tsit, can Gado ya ɗaga murya ya ce: “Zaman nan fa da sake, kullum ƙara takure ƙananan Ttsuntsaye ake. Na ji labarin wai za a ƙara kuɗin sinadarin makamashin zirga-zirga, ga farashin tsaki kullum hauhauwa yake; har ta kai tsuntsaye yanzu yin ƙoto sau biyu a yini sai mai tsananin rabo.”

Kanari ta ce: “Ni ba abin da ya daɗe yana mun raɗaɗi a zuciya irin maganar da Shugaban Majalisar Ragon-Maza ya yi, har ya bayyana a majigi yana ce wa ‘yan uwansa su kwantar da hankalinsu, an tanadar musu sulalla masu ɗimbin yawa don su more hutun da za su tafi. Wato dai mu an ɗauke mu bayi ke nan ko?”

Hazbiya ta numfasa ta ce: “Ga kuma yaƙi da ake ta ƙoƙarin sai an assasa tsakaninmu da ‘yan uwanmu kuma maƙwabtanmu. Muna cikin wannan ƙangin za a ƙaro mana wata musibar. Kaico!”

Cakwaikwaiwa ta ce: “Jemage ke nan ake faɗa muku! Shi ai kullum sama yake hangowa, ba ruwansa da lura da halin da na ƙasa ke ciki. Na ji an cire sunayen tsuntsaye uku, ciki har da Yautai, wanda aka tura Majalisar Ragon-Maza don a tantance su ko?”

Bainu ta amsa da cewa : “Eh, an ce wai bai iya bakinsa ba. Allah Ya kyauta. Ita kuma ‘yar uwarmu dangin Agwagwa, Ungulu ce ta ba da umarnin a sauya ta.”

Da yake dare ya tsalla, Tsuntsaye suka buƙaci Alhudahuda ya yi addu’a ga tsuntsayen da iccen sheƙar ibada ya yi sanadiyyar su tafiya gidan gaskiya. Ai ko ya ja addu’a, aka shafa, aka yi sallama.
~~~~~~~
Malam Mukhtar Mudi Sipikin, marubuci, sha’iri, ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa; ya rubuta wannan shaguɓe a ranar 12-08-2023.
~~~~~~~

Previous Post

NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

Next Post

Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

Related Posts

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU
Shanshani

SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU

December 22, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Shanshani

KAMUN LUDAYIN JEMAGE (26-08-2023 da 02-09-2023)

September 2, 2023
KAMUN LUDAYIN JEMAGE
Shanshani

KAMUN LADUYIN JEMAGE (19-08-2023)

August 20, 2023
Next Post
Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana’a – In Ji MAK

Ƙuncin Rayuwa: Matasa Ku Tashi Ku Nemi Ilimi Da Sana'a - In Ji MAK

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Dokta Bukar Usman: Garkuwan Adabi Ya Cika Shekara 80

Dokta Bukar Usman: Garkuwan Adabi Ya Cika Shekara 80

May 29, 2023
TATTAUNAWAR KHALID IMAM: Zuwa Ga Malam Bashir

TATTAUNAWAR KHALID IMAM: Zuwa Ga Malam Bashir

October 22, 2023
Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Idris

October 28, 2023
Sheikh Abduljabbar Ya Kusa Samun ‘Yanci

Sheikh Abduljabbar Ya Kusa Samun ‘Yanci

June 5, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.