• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, May 3, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Gwamna Raɗɗa Ya Kusa Kammala Tashar Mota Mafi Girma A Najeriya

Gwamna Dikko Zai Kafa Babban Tarihi - Injiniya Muntari Sagir

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 30, 2025
in Babban Labari
0
Governor Radda Builds Nigeria’s Largest Motor Park

Babbar Tashar Motar KTSTA ta Zamani

34
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gwamna Raɗɗa Ya Kusa Kammala Tashar Mota Mafi Girma A Najeriya

• Gwamna Dikko Zai Kafa Babban Tarihi – Injiniya Muntari Sagir

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

                                •••••••

Babbar Tashar Mota ta Zamani ta KTSTA: Gwamna Radda zai kafa tarihi a fannin sufuri a Najeriya

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa yana gab da kafa wani babban abin tarihi a jihar dangane da abin da ya shafi harkar sufuri. Wannan kuwa shi ne kammala ginin babbar tashar mota ta zamani, mallakin Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA).

A wata ganawa da Babban Manajan Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina, Malam Haruna Musa Rugoji, ya bayyana wa wakilinmu cewa, tun da farko, a zamanin mulkin Gwamna Aminu Bello Masari ne aka fara aikin gina tashar, a babbar harabarta da ke kan titin Katsina zuwa Kano, a Unguwar Ɗanɗagoro. Ya ce ya zuwa yanzu an kammala katange ilahirin tashar kuma dukkan gine-ginen sassanta sun kai tsawon linta.

Malam Haruna Musa Rugoji, Janar Manaja na KTSTA

Wakilinmu ya gana da Shugaban Kamfanin Gine-Gine na Muntasarab, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi, wanda shi ne ke aikin gina wannan babbar tasha ta KTSTA. Ya bayyana ƙima da muhimmancin da ke tattare da wannan tasha. A cewarsa: “Wannan tasha, idan aka kammala ta, za ta zama irinta ta farko ta zamani a duk faɗin Najeriya. Domin a lokacin da ake shirin fara gina ta, sai da muka zagaya sassan ƙasar nan, domin ganin ko akwai samfurin da zai yi mana jagora. Amma duk tashar da aka gaya mana, idan muka je sai mu ga cewa ba ta dace da irin wadda muke so ba. Akwai ma wata babbar tasha da ake magana a Jihar Nasarawa, amma ko kaɗan ba ta kai girma da kyau da ingancin wannan ta KTSTA ba.”

“Babu shakka, idan aka kammala wannan tasha, mai girma Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa zai kafa babban tarihi, domin kuwa ita ce za ta zama babbar tashar mota ta zamani ta farko irinta a duk faɗin Najeriya.” In ji Injiniya Muntari.

Injiniya Muntari Sagir Malumfashi, Shugaban Kamfanin Gine-Gine na Muntasarab

Wakilinmu ya tambaye shi, ko me ya sa aikin ya tsaya, har yanzu ba a ci gaba ba? Ya amsa da cewa: “Ka san harkar gwamnati ‘yar bi a hankali ce, kuma tana buƙatar natsuwa ba tare da garaje ba. A yanzu da muke maganar nan, mai girma Gwamna Dokta Dikko Umar Raɗɗa ya gama shirinsa na kammala wannan aiki, har ma ya ba da umurnin a ci gaba. Don haka, in sha Allahu nan ba da daɗewa ba za a ci gaba da aikin, tare da fatan kammala komai nan da ƙarshen shekarar nan, in Allah ya yarda.”

Injiniya Muntari Sagir ya yaba wa Babban Manajan Hukumar KTSTA, Malam Haruna Musa Rugoji, wanda ya ce babu shakka shi mutum ne da ya ƙware a harkar sufuri. “Malam Haruna mutum ne mai gaskiya da amana, wanda ya kawo ci gaba a wannan hukuma. Kuma mai girma Gwamna yana yaba masa, kamar yadda mu ma muke ganin ƙoƙarinsa a wannan harka ta sufuri.” In ji Injiniya Muntari.

Samfurin Tashar

Da Malam Haruna yake zagayawa da wakilinmu domin gane wa idonsa yadda ginin tashar ke gudana, ya jaddada muhimmancin da ke tattare da wannan babban aiki. “Harkar sufuri tana ɗaya daga cikin ginshiƙan bunƙasa harkokin al’umma. Babu wani al’amari da bai da alaƙa da sufuri.” In ji Malam Haruna.

Ya ƙara da cewa, “Idan ana maganar noma da bunƙasa shi, akwai gudunmuwar sufuri. Idan ka ɗauki aikin al’umma na yau da kullum da ya shafi harkar lafiya, ilimi, sana’a da harkokin kasuwanci, duk ba su gudanuwa cikin nasara sai da taimakon sufuri a ciki. Saboda haka, idan aka bunƙasa harkar sufuri, za ta inganta rayuwar al’umma gaba ɗaya. Don haka idan aka kammala aikin wannan babbar tasha, za ta samar da ayyukan yi kuma ta bunƙasa ci gaban al’ummar Jihar Katsina, da ma ƙasa baki ɗaya.”

Wani Sashi na Tashar da ake kan ginawa

Wakilinmu ya yi tattaki zuwa harabar sabuwar tashar, wacce ita ce za ta zama babbar hedkwatar Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina – KTSTA, inda ya gane wa idonsa yadda aikin ginin yake gudana. Tasha ce mai girma da faɗi, wacce aka kafa a wuri na musamman da ya dace da ita, watau bakin babban titin shiga Babban Birnin Jihar Katsina.

Tashar tana da yalwa da faɗi, sannan kuma an karkasa ta zuwa sassa daban-daban masu muhimmanci. Akwai babbar rumfar ajiye motoci yalwatatta, wacce za ta ɗauki motoci Masu yawa. Akwai gidan mai, inda motocin za su riƙa shan mai, mallakar hukumar. Haka kuma akwai garejin gyaran motocin na musamman, wanda sashi ne na musamman wanda ke ƙunshe da wurin gyara, ofisoshin makanikai da suto na ajiye kayan gyara da kuma ɗakunan ba-haya.

Sashen Ajiye Motoci

Duka dai a cikin babbar tashar, akwai babban masallaci da wurin alwala da ɗakunan ba-haya wadatattu na maza da na mata, domin fasinjoji da sauran mutanen da za su yi harkokinsu a cikin tashar. Akwai sashi na musamman domin sayar da abinci. Wuri ne wadatacce wanda ya haɗa da ɗakunan girki daban-daban, da ofisoshin ma’aikatan wurin da kuma faffaɗan ɗakin cin abinci ga fasinjoji. A nan sashin ma, akwai ɗakunan ba-haya na musamman, domin ma’aikata da masu sayen abinci.

Wasu Ofisoshin Hukumar

Haka kuma, domin samar da tsaro, akwai sashi na musamman da aka tanadar ga jami’an tsaro – madaidaicin ofishin ‘yan sanda wanda shi ma aka inganta da dukkan abin da ya kamata. Wannan ya haɗa da ofisoshi da ɗakunan ba-haya da sauransu. Haka kuma akwai sashi na musamman domin ma’aikatan kashe gobara.

Haka kuma, a cikin babbar tashar, an samar da sashi na musamman, inda aka gina ɗakunan saukar baƙi. A nan fasinjoji za su iya kwana cikin aminci a farashi mai rahusa, wanda haka zai hutar da su shiga gari domin neman wurin kwana, musamman idan su baƙi ne da suka zo Katsina daga wurare masu nisa. Haka kuma akwai sashi na musamman da aka gina shaguna wadatattu, domin ‘yan kasuwa da za su riƙa sayar da kayayyakin buƙata ga fasinjoji. Komai an shirya shi a kintse.

Samfurin Tashar

Shi kuwa Sakataren Hukumar KTSTA, Malam Ibrahim Ahmad, yaba wa Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya yi, saboda ƙudirinsa na kammala aikin babbar tashar. Haka kuma ya nuna gamsuwa da tsarin tafiyar da hukumar da Babban Manaja, Haruna Musa Rugoji yake gudanarwa.
_______________

Previous Post

HAƊIN KAI: SHAWARA TA MUSAMMAN GA ƊAUKACIN MARUBUTAN HAUSA

Next Post

NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 27-1447

RAMADAN KARIM: 27-1447

March 16, 2026

TURBANIN CEREMONY OF SARKIN GABAS OF TUMBU:

October 10, 2024
SOKOTO to MATAZU: A Journey Through Time and Turmoil

SOKOTO to MATAZU: A Journey Through Time and Turmoil

September 22, 2024
Ba Za Ku Yi Nadamar Zaɓen Mu Ba

Ba Za Ku Yi Nadamar Zaɓen Mu Ba

June 19, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.