Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato
Daga Wakilinmu
__________
A wani hukunci da ake ganin alamar babbar nasara kuma wanda zai kawo daidaito tsakanin al’umma, wanda kuma zai dakatar da tsangwama ga al’ummar Hausawa da Fulani mazauna Jihar Filato, Babbar Kotun Jihar Filato da ke Jos ta yanke hukunci, inda ta umarci Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ta bai wa wata mata Bahaushiya mai suna Fatima Baba Akawu Takardar Shaidar Zama ‘Yar Ƙasa (Certificate of Indigene) cikin kwanaki 30.

Lamarin ya samo asali ne yayin da wata Bahaushiya mai suna Fatima Akawu, wacce aka haifa kuma ta tashi a Jos ta je Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, domin karɓar Shaidar Zama ‘Yar Jos ta Arewa, inda nan take aka hana amma aka ba ta Shaidar Wucingadi.
Gidan Talabijin na Zinariya TV, ya ruwaito cewa, daga nan ne Fatima ta maka Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a kotu.
A hukuncin da Mai Shari’a C. Donglong ya yanke a ranar Talatar da ta gabata, kotun ta bayyana cewa takardar “Residential Certificate” da wasu ƙananan hukumomi ke bayarwa, ba ta da wani matsayi a dokokin Najeriya, tare da cewa ƙin bai wa Fatima Takardar Zama ‘Yar Ƙasa yayin da aka bai wa wani ɗan Berom irin wannan takarda ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa.
Kotun ta kuma bayyana cewa duk ɗan da ya fito daga iyaye masu cikakken matsayin ’yan asalin wani yanki, yana da haƙƙin samun takardar zama ɗan yankin, ba tare da la’akari da ƙabilarsa ba. Haka kuma ta haramta wa Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ci gaba da amfani da “Residential Certificate” a matsayin madadin Takardar Zama Ɗan ƙasa.
Masanin shari’a a Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Bauchi, Farfesa Ahmed Salisu Garba, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma yaƙi da wariya. Ya ce hukuncin ya tabbatar da matsayar cewa bambancin “ɗan asali” da “baƙo” ba shi da tushe a Kundin Tsarin Mulki, idan ana maganar haƙƙin ɗan ƙasa.
Farfesan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato da sauran ƙananan hukumomin ƙasar nan da su yi biyayya ga hukuncin kotun, tare da dakatar da duk wata hanya da ke hana wasu ’yan Najeriya samun cikakken haƙƙinsu bisa la’akari da ƙabila ko asali.
__________












